3.

507 72 5
                                    

MARYAMA MARYAM 3.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

RASHIN SANI.

Suna gama wayar ya duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yaga uku da mintuna, tashi yayi yana fita.

Part ɗin Maminsu yayi bayan ya shiga ya tarar Hassan da Hussaini a falon Mami zaune tare dasu.
Zama yayi yana tambayar Maryama.
"Mami ina Maryama ne?"

Hankalinta ta maida kan Ya Nurain.
"Tana ɗakinta kwanakin nan kwata kwata bata fita in ba gurin Kaku zata je ba, ko dan ita ɗaya ce a gidan."

"Bari in dubata."
Ya faɗa yana nufan hanyar ɗakinta.
Ƙwanƙwasa yayi tare da sallama, wayarta dake hannunta ta ajiye bayan karanta saƙon da Ya Faruq ya turo mata da ya fara sauya mata zuciya, bayan ta amsa tana tashi zaune.

Ciki ya ƙaraso ya zauna baƙin gadonta yana kallonta yace.
"What's wrong with you last born?"

Kanta ƙasa tana watsa da zoben hannunta ta girgiza masa kai tace.
"Babu Ya Nurain."

"Akwai mana Ya Faruq ne ko?"

Idanunta ta ɗago tana kallonsa da mamaki sai ta juyar gefe tana turo bakinta tace.
"Ya takura mini Yaya wai fa sona yake, ni dai kaje ka samesa kace bana sonshi kuma bazan aureshi ba ya nemi wata Maryama bani ba."

"Ke mai ya hanaki faɗar haka."

Shuru tayi tai kicin kicin da fuska hakan yasa yaci gaba da magana.
"Na san irin rayuwar da ku kayi da Ya Faruq, sam sam bakwa shiri har ya bar gidan nan amma ko kin san tsana tana komawa ta zama soyayya."

"Sai a kaina hakan zata faru?"
Ta tambayi yayantan tana dubansa.

Ɗan murmushi yayi yace.
"Kwairai kuwa Maryamarmu ki buɗe zuciyarki ki amshi soyayyar ɗan uwanki hannu bibbiyu shi da ya buɗe bakinsa yace miki yana sonki ai wannan rayuwar da ku kayi a baya duk ta wuce sai soyayya da zai maye gurbin, dama wannan faɗar da yake miki da takura duk soyayyace."

Kunyane ya kamata ta juya tana murmushi ta kasa bashi amsa.
Anan yayi ta cusa mata ra'ayin soyayyar Umar Faruq a zuciyarta har taji zata bashi dama kafin ya fita dan jin ƙiran sallar la'asar.

Daya dawo daga masallaci ya sanar Ya Faruq abin da su kayi da ita.
"Ya Faruq na mata magana."

"Thank you brother ka sanar da Abbi suyi magana da Abba a samu iyayenta please i don't want to take time."

"Da wuri haka Yaya."
Ya Nurain ya faɗa yana ƙoƙarin faɗa masa cewa ai mahaifin Maryaman shine wanda yace a fara ma magana kafin nasa mahaifin amma ya tare numfashinsa yace.

"Ka sanar dasu kawai nima zuwa next month zan shigo in na samu free, ka sanar dani mai ake ciki in kunyi magana may be in Abbi yaji labari zai ƙirani."

"To shikenan Allah kaimu sai ka shigo."
Ya Nurain ya faɗa yana kashe wayar.

...

"Why Pretty Lady, mai yasa bakya picking call ɗina ko dai har yanzu ban kai matsayin masoyin ba."

Ita fa yanzu nauyinshi da kunyarsa take ji tun ranar da Ya Nurain yazo mata da maganar taji sauƙi tattare da damuwar da ta shiga, hakan yasa tayi ƙoƙarin nutsar da zuciyarta guri ɗaya ta fara ɗaukar wayarsa yau.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now