21.

413 49 2
                                    

MARYAMA MARYAM 21.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Momy wallahi na tsaneta hankalin Ya Faruq na ƙoƙarin komawa kanta duk da yana nuna min nice zaɓinsa da abar sonshi."
Hawayen idonta Maryam ta share bayan ta gama ma Momynta bayani komai ta ƙara da faɗar haka.

"Dai na kuka akan mace Maryam nawa Maryama take da har zaki zubar mata hawaye, ke har kin manta shi uban Faruq ɗin ta ya na aureshi balle ɗanshi Faruq."

Faɗin Momy ta jawo jakarta ta ciro goruna biyu da rubutu a ciki wanda sai ka lura zaka gani, da kuma ƙullin magani ta bata.
"Ki tabbatar sun sha dukkansu da zaran sun sha tsanar junansu da rashin son kusantar juna zai samesu in har wannan abun ya faru shikenan zai gaji da ganinta har ya saketa, ba zai taɓa karyewa a jikinta ba sai ranar data haihu kinga kuwa babu rana da zaran ya saketa balle maganar samun ciki, wannan kuma kiyi wankan tsarki dashi kar ki bari tsarkin ki ya karye har sai ya haɗa shimfiɗa dake daga lokacin zai zama maganarki yake ji."

Karɓa Maryam tayi a tsorace dan ire iren abun nan tsoro suke bata amma ance cikar buri yafi komai.
Ɓoyewa tayi in da tasan ba mai gani ta dawo gurin Momynta.

"Momyna nagode inshaAllah zan yi ƙoƙarin yin hakan, maganar zuwa Maiduguri kuma fa."

"Kar ki damu in har abun nan yayi aiki zuwanki ba matsala in kuma aka samu akasin haka to sai kinzo."

"To shikenan ba za'a samu matsala ba."

Sun jima suna hira kafin suka sauƙa ƙasa Maryam ta ɗaura abincin rana suka ci ta ajiyewa Faruq nashi.

Kwanan Momy biyu ta koma bayan ta haɗa ƴartan da huɗuba marasa amfani.
Kullum safiya maryama tana fita ta gaisheta tana amsawa kamar ba komai a ranta.

Ya Faruq da Maryam sun raka Momy airport Maryama ta sauƙa ƙasa dan ɗaura abinci, shurun da taji gidan ya tabbatar mata ba kowa.
Kitchen ɗinta ta shiga ta tafasa indomie ta juye a plate ta fito har zata wuce sama ta tuna ba ruwa a fridge ɗinta ta buɗe fridge ɗin falon ta kwashi goron ruwa uku da ta gani ya rage ta wuce sama tana cewa in sun ga babu ai zasu sayo wani.

Zama tayi taci abincinta ta ƙoshi tasha ruwa ta saka sauran a fridge.

Basu dawo gidan da wuri ba sai da suka biya shan ice cream suka sha ya sayawa Maryama kafin su dawo suka wuce sama ɗakin Maryama ya shiga ya ganta kwance tana bacci ya buɗe fridge ɗinta ya saka mata ya koma ɗakin Maryam.

Tana samun damar ya wuce ɗakin Maryama ta shiga bathroom ta haɗa ruwan wanka ta fito dan rage kayan jikinta ya shigo ɗakin tana ganinsa tayi ƙoƙarin komawa bathroom ɗin ya riƙota.

"Ina kuma zaki?"
Yace yana zuge mata zip ɗin rigarta.

Tana ƙoƙarin kwace jikinta tace.
"Wanka zan yi ka bari dan Allah."

"Ai ke da wanka sai kuma anjima."

Bai bata damar sake magana ba ya rufe bakinsa da nata ya fara mantar da ita.

Bayan komai ya lafa ya ɗauketa su kayi bathroom ruwan wanka da ta haɗa ya bari ya wuce ya tara musu wani tana kallo ba daman magana kamar tayi kuka amma in ta tuna da d'ayan sai hankalinta ya kwanta.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now