22.

418 61 4
                                    

MARYAMA MARYAM 22.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Ihun Maryam shi ya saka Maryama fita a ɗakinta da sauri ta duba in da taji ihun can karshen step ta hangota tana juyin azaba.
Kamar karta sauƙa amma halin da take ciki ya sakata jan kafarta ta ƙarasa wajenta ta ɗan tsaya nesa da ita.

"Ke lafiyarki."
Shine abinda Maryama ta faɗa daga inda take.

Maryam bata ma ji mai Maryama ke faɗa ba taci gaba da juyi tana ƙiran sunan Allah.

Ganin haka yasa Maryama juyawa ta koma ɗakinta, kasa zaune tayi ta jawo wayarta ta ƙira Ya Faruq da ya kusa isa gidan yana hanya barinsa office.

Yana ɗauka bata jira yayi magana ba tace.
"Yaya kayi sauri kazo ga can matarka na ihu zata mutu."

"Maryam ɗin? Mai ya sameta? Gani nan zuwa."
Yace da sauri yana kashe wayar ya ƙara speed na motarshi.

Tana jin ƙaran buɗe falon ta fito da saurinta taga ya nufi Maryam dake kwance cikin jini yana ɗagota ba ma numfashin kirki jikinta.

"Let's go hospital Maryama ɗauko mayafinki."

Da sauri ta koma ta zari mayafinta ta kulle kofarta ta sameshi cikin mota ya kwantar da Maryam a baya, front sit ta shiga ta zauna sabon maigadin daya ɗauka ya buɗe masa get yana jan motar a 140.

Bai tsaya ko ina ba sai asibitinsu aka karɓeta, kasa dubata yayi ya fita waje ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zirga zirga yake.

Ganin yadda duk ya tada hankalinsa yasa Maryama danne abinda ke tasowa a zuciyarta ta nufi wajenshi.
"Yaya ka zauna mana addu'a zaka mata."

Kallonta yayi wanda maganan kirki ta haɗasu har ya manta, manyan idanuwanta ta zuba masa ya sashi takawa ya zauna inda take itama ta zauna gefenshi.
Bata ankara ba taji kanshi saman cinyarta ya ɗaura tare da riƙo hannunta.
"Maryama mai ya samu Maryam lafiya ƙalau na barta, ina son Maryam bana son wani abu ya sameta."

Shuru ta mishi jin kanshi da ya ɗaura mata take tamkar ƙaya haka hannuwansa da take ji tamkar wuta yana ƙonata.

"Mai ya samu Maryam?"
Shine tambayar da ya maimaita mata.

"Nima ban sani ba ina ɗakina naji ihunta."

Zai yi magana Dr ya fito hakan yasa yayi shuru ya tashi ya nufi wajen Dr.

"What happen to her Dr."
Ya Faruq ya tambayi Dr.

"Sorry Dr Faruq ta samu miscarriage ne ."

"Cikine da ita dama?"
Shine tambayar da Ya Faruq yana Dr da sauri cike da mamaki.

Kai Dr ya ɗaga masa yace.
"She's 7weeks pregnant but munyi ƙoƙarin muyi saving ɗin Baby abun ya gagara ya fita Allah baka wani."

Shuru Ya Faruq yayi har Dr ya wuce Maryama ta ƙaraso wajen tace.
"Lafiya?"

Kallonta yayi murya can ƙasa yace.
"Na rasa child ɗina Maryama, Maryam tayi miscarriage."

Dum taji maganarshi ya shigeta har zuciyarta ya buga ta kasa furta komai sai kallonsa take.

Ganin haka ya sashi shiga ɗakin da Maryam take ya samu ta farfaɗo sai kuka take, bakin gadon ya ƙarasa ya riƙo hannuwanta.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now