35.

464 69 2
                                    

MARYAMA MARYAM 35.


Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Da safen kafin su Maryama su wuce ta shiga gurin Kaku yi mata sallama bayan sun gaisa Maryama ta tashi zata tafi kaku itama ta miƙe tace.
"To a dai kula kar aje gidan miji ayi ta cin tuwo a kumbura kinga dai abokiyar zamanki yanda take duk da ta fiki shekaru amma bata da wani ƙibi jikinta dai-daine, ke kuma yanzu ki ke ɗanyarki kije ki ci tuwo ki kumbura duk abubuwan ki su ɓuya mijinki ya daina ganinsu."

Ko kulata Maryama ba tayi ba ta wuce abinta Kaku ta bi bayanta tana ƙara faɗin.
"Kuma karki raga mata in ta taɓa ki in kin kasa ramawa ki ƙira ni ki faɗa mini in rana miki kan uwarta."

Sai lokacin Maryama ta juya tayi murmushi ta wuce gurin Ammi ta mata sallama Ammi tana ta bata hakuri da nasiha kafin ta fito ta samu Hussain ya kaita gidan Nafisa.

Data isa Nafisah ta jata zuwa ɗaki tana ta mata faɗa akan ta dage ta kula da kanta dan ba ita ɗaya bace gurin miji kuma wannan rashin kunyar ta rage mishi ta cire kunya gefe ta kula da mijinta sannan yawan shan fruits yafi komai gyara mace akan liƙe liƙe da manne manne.

Dariya Maryama tayi son ranta Nafisa ta bita da kallo tace.
"Wato ma abin dariya kika mai dani."

Maryama na dariya dakyar ta tsagaita tace.
"Mamaki nake ashe Safina haka take."

"Ban sani ba ki zauna wannan Maryam ɗin ta kwace miki miji, wanda dama tun asali ke yake so ba ita ba dama ni na sani Ya Faruq mugun so yake miki wanda shi kansa bai sani ba."

Murmushi kawai Maryama tayi tama Nafisa sallama Hussaini ya maidata gida wajen ƙarfe sha biyu.

Abinci taci ta cika cikinta ƙarfe ɗaya ta gabatar da sallah kafin Ya Faruq ya shigo suka gaisa da Mami yace Maryama su tafi.

Ɗakinta ta shiga ta jawo akwatinta ta fito ya taimaka mata suka fita tare yana riƙe da hannunta.

A bakin motar suka tarar da Maryam tsaye itama da akwatinta tana ganinsu haka fara'ar fuskarta ya ɗauke suka ƙaraso ya saka akwatin Maryama boot ganin haka ya hana Maryam saka tana ta buɗe gidan baya ta shiga dan tasan shi zai shiga Maryama ta zauna a gaba ita da Hussaini da zai kaisu airport.

Ya Faruq ganin Maryam ta bar akwatinta yaja ya saka mata dan duk a zauna lafiya ya zaga ya buɗewa Maryama gefe ɗayan ta shiga ya rufe ya zagaya ya shiga gaba Hussain da ya iso ya shiga yana tada motar suka bar harabar gidan.

Maryama da Maryam ba wanda yama wani magana ko wanne ya ɗauke kansa Ya Faruq duk yana lura dasu bai ce komai ba.

Da suka isa airport ɗin Hussain shi ya cirowa ko wacce akwatinta kafin su wuce yaja motar yana barin gurin.

Cikin jirgin ko wacce da seat ɗinta ba suma ga juna ba har suka sauƙa kafin su isa gida.

Ɗaki suka shige Maryama ta fara gyara ɗakinta data bari tsawon sati shida ana cikin na bakwai.

Sharewa tayi tas tai goge goge ta wanke bathroom ta saka turaren wuta ta kunna Ac ɗakin yayi sanyi sosai, kafin ta shiga wanka ta fito ta nemi kaya cikin kayanta riga ƴar kanti ta saka taki shafa lotion saboda zafin da take ji ta feshe jikinta da turare ta sauƙa ƙasa dan jin wani yunwa na cinta.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now