34.

459 69 7
                                    

MARYAMA MARYAM 34.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

A hanyar shiga part ɗin Mami Ya Faruq ya haɗu da Kaku hannunta riƙe da jug data hangoshi ta ɓata rai har suka haɗu a baƙin kofar shiga falon yace.
"Tsohuwa mai ran ƙarfe ya daren."

"Kai kam ka shigesu ace mutum kuɗin shi ya ƙare a iska kullum kana tsakanin hanya baka ciwon baya ."

"To ya zanyi matata tana nan."

"Ku kuka sani magulmata da kai da ita din kana so kaƙi nunawa sai yanzu kuma da tace bata so itama nasan gulmace ta hanata nunawa amma tana son."

"Allah ko Kakus ki mata magana nasan za taji maganarki."

Baki Kaku ta riƙe tace.
"Wah ni Hamsatu ai duk jikokina bayan Safina ba wanda ya rainani sai Maryama."

Dariya Ya Faruq yayi suka shiga cikin falon, da rayuwarshi ya fara haɗa ido ya mata murmushi da ya sata jin zuciyarta bugawa ta sunkuyar kanta kasa taci gaba da cin abincin ta.

Kaku Jug ɗin hannunta ta ajiye gurin Maryama tace.
"Ga furarki da kika sani dama miki ko Ahmadi baya bani wahalar da kike bani."

"Nagode."
Maryama tace ta buɗe taga da ƙanƙara a fashe a ciki yayi sanyi ƙalau ga ya damu kawai ta kafa baki bata jira zubawa a cup ba.

Ya Faruq gurinta ya ƙarasa ya zauna jin haka yasa ta ajiye jug din tana dubanshi ya karɓi jug din ya gani ya kalleta yace.
"Zai miki illa yayi sanyi sosai."

"Nafi son haka."
Tace ta mai da hannunta cikin abincin ya kalla yaga faten wakene ya kalli Maryama yana karantarta tsaf.

Ganin ya ciki kallonta ya sata tashi ta ɗauke plate din ta kai kitchen ta wanke hannunta ta wuce ɗakinta da jug ɗin a hannunta.

"Wai dama Umaru haka take maka wannan mugun ci kamar gara kace da mun kusa kawo maka taimakon gaggawa."
Faɗin Kaku da taga Ya Faruq ya bi Maryama da kallo.

Girgiza kai yayi ya miƙe ya bi bayan Maryama ya bar Kaku da baki sake dakyar ta samu ta rufe tace.
"Yau naga fitsara a gaban nawa zaka bi mace ɗaki Umaru, to ka mata uwar me? Itama ƙaramar yarinya har tasan ta shiga ɗaki miji ya bita, mukam zamaninmu har ka shekara gudun miji kake, bari iyayenku su dawo yau ba gobe ba ka ɗauke matarka ku bar mana gida fitsararru."

Surutun ta tayi tai da Ya Faruq bai ma san tana yi ba da ta gaji ta bar falon.

Ya Faruq na shiga ɗakin ya ja stool ya zauna ya saka Maryama gaba yana binta da kallo kusan mintuna tace.

"Lafiya?"

"Lafiyarce ta kawo haka."

Kai ta ɗauke tana shirin kai Jug din baƙinta ya rike.
"Yayi sanyi sosai zai miki illa ki bari ya huce."

Rai ta ɓata tace.
"In ya huce ba zan iya shaba."

"Yaushe zamu koma gidanmu?"
Tambayar daya mata kenan ta dubeshi idonshi cikin nata ta ɗauke idanunta taƙi bashi amsa hakan yasa yaci gaba da maganar shi.
"Dan Allah Maryama duk abinda na miki a baya kiyi hakuri mu koma gidanmu muci gaba da rayuwarmu, Umar Faruq ba zai iya zaman Abuja ko gidanshi ba in ba tare da rayuwarshi ba wanda Maryama ce na rokeki kiyi hakuri."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now