6.

457 62 2
                                    

MARYAMA MARYAM 6



Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Tun ranar Maryama bata ƙara gigin haɗa hanya da Ya Faruq ba, da zaran taji muryarsa bata fita in kuma yana part ɗinsu bata shiga.

Haka har aka cinye sati guda lokacin da appointment nasa ya fito an turasa Abuja, cikin kwana uku ya gama shiri suka ɗau hanya.

Suna tafiya Ya Nurain zai kaishi airport hankalinsa akan titi yace.
"Nurain ka sawa Maryama ido sosai Please."

"InshaAllah ya maganar school nata."

"We will talk later."
Yace yana maida hankalinsa ga tukin da yake yi.

Bayan sun isa airport ya bawa Ya Nurain key ɗin motar shi kuma ya wuce.

Tun da ya tafi taji gidan ya mata daɗi duk da ta matsawa Abbinta akan school ya ce sai Ya Faruq yayi magana amma hakan bai sa ta fasa masa magana ba.

Wuni take tana shiga wajen Kaku da part ɗinsu sai wajen su Nafisa da bata cika zuwa sosai ba.
Saleem yazo taki fita ya ƙirata wayarta kashe ya shiga damuwa sosai amma hakan bai saka ta fita wajensa ba dan ta lura da abinda yake so sannan kuma ga duka da tasha hannun Ya Faruq.

Tafiyarsa da sati uku aka fara thumbprint na WEAC, da ya samu labarin ya ƙira Nurain.

"Ya Faruq ya kake ya wajen aiki?"
Ya Nurain ya faɗa bayan sun gaisa.

"Lafiya kalau Nuru ya mutanen gida."

"Duk lafiyarsu ƙalau."

"Kasan mai yasa na ƙiraka wani aiki za kamin Please, akan school na Maryama ka ɗauketa kuje tayi thumbprint an fara sannan in har ban samu zuwa ba har suka fara paper za kana kaita kana dawo da ita ka amshi timetable din saboda sanin lokacin yin papern."

Murmushi Ya Nurain yayi cike da farin ciki yace.
"InshaAllah zanyi haka kasan har ta hakura ta daina maganar."

"Yanzu ma ban bata damar aikata wani abun bane ka sanar da ita ta kiyaye in kuma ba haka bane zan hanata gaba ɗaya."

"Shikenan inshaAllah fatan kar a kuma maimaita."

Ameen ya faɗa a cikin ransa su kayi sallama.

Washegari ranar talata ya faɗa mata tayi farin ciki sosai sai murna take harda tsallenta a ɗaki kafin ta shirya cikin shirin uniform ta fito suka tafi.
Tayi lafiya dan komai a gabansa a kayi kafin su dawo gida.

Sunyi haka da sati biyu timetable ya fito yaje har makarantar ya karɓa mata yayi photocopy ya riƙe ɗaya ya bata ɗaya ya ɗauka a hoto ya turawa Ya Faruq.

Haka rayuwar taci gaba da tafiya har su kayi Jamb ta samu score mai kyau, suka fara WEAC saura NECO.

Ranar papern karshe suka zana Biology, Ya Nurain yazo ɗaukarta.

A gajiye liss ta shigo falon ba kowa a nan saman kujera ta cire hijab ɗinta ta zuba komai dasu questions paper da pen din hannunta ta kwanta saman kujera, baccine ya ɗauketa a gurin.

Tun da ya dawo ya shiga yaga Mami bata nan ya shiga part ɗinsu anan ya samu harda Ammi ita da Aunty Saleema sun fita gaisuwa asibiti.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now