26.

419 64 8
                                    

MARYAMA MARYAM 26.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Dr Ilyas ya buɗe baki zai yi magana Nurse ya shigo tare da folder ya miƙa Dr Ilyas yana fita.

Miƙa Ya Faruq foldern yayi yace.
"Gashi ka duba bayanin ciki za kaga komai."

Bai iya karɓa ba yace.
"Bazan iya karantawa ba Dr ka min bayani kawai."

Rufe foldern yayi ya kalli Ya Faruq yace.
"Ba wani matsala bane inshaAllah da yardarsa komai zai zo da sauƙi, munyi scanning mun mata test sakamako ya nuna mana cewa matarka ba zata iya ɗaukar ciki ya daɗe jikinta."

"What? How?"
Shine tambayoyin da Ya Faruq ya jera Dr Ilyas.

"Ka kwantar da hankali ka Dr kamar yadda nace maka komai zai zo da sauƙi, abun da yake jawo hakan kaima ka sani yawan abortion ko shan drugs na hana ɗaukar ciki ko over dosage na shan drugs na abortion wasu kuma haka tasu mahaifar yake, amma in har ya kasance mace tayi ɗaya daga ciki zai yi wuya ciki ya zauna a jikinta sai in har taci Sa'a tana shan magunguna zata iya ɗaukar ciki har yayi kwari in ta kusa haifa sai a mata CS."

Girgiza kansa Ya Faruq yayi yace.
"Maryam ba zata aikata haka ba domin a budurwa na sameta bayan haka ma ba zata iya abortion ba yaushe ma ta samu cikin? Wannan shine cikinta na farko, sai dai Ƙaddararta ya zamto haka."

"Kar ka damu Dr zamu bata magunguna inshaAllah zata samu sauƙi gashi ka duba foldern za ka fahimci komai sama dani."

Tashi Ya Faruq yayi ya fita a office ɗin nashi bai iya karɓa ba ya shiga ya samu Maryama zaune ya zauna kusa da ita tana binshi da ido tana ganin hannunshi suka zagayeta ya rumgumeta tare da ɗaura kansa saman kirjinta can ciki yace.
"Maryama I lose my baby again."

Dum taji zuciyarta ya buga tausayinshi taji na shigarta a hankali, duk da tana jin zafin fatar jikinshi a jikinta amma ta kasa hanashi hakan yadda take ganin yana cikin halin damuwa.

Sun daɗe haka ya ɗago kansa ya kalleta itama shi take kallo yace.
"I'm coming."

Daga haka ya fice a office din ya nufi ɗakin da Maryam ke kwance ya sameta da drip na jini an saka mata gefen d'ayan na ruwa, ƙarasa wajen gadon yayi ya ja kujera ya zauna ya zuba mata ido wani tausayinta na ratsashi.

Ƙarar wayarsa shi ya sashi ɗauke idonshi a kanta ya ciro yaga Aunty Sameera bayan ya ɗauka tace ta ƙira Maryam bata ɗauka yace sun fita zuwa anjima zai dawo za taji komai.

Ganin la'asar tayi ya sashi fita ya samu Maryama yace suje gida.

Da suka isa gida bayan sun shiga falon zata wuce sama ya dakatar ta ya karasa wajenta yace.
"Please little sister ki tafasa mata ruwan zafi kafin mu wuce."

To tace ta wuce ɗakinta tayi sallah ta canza kaya ta sauƙa ta dafa ruwan zafi ta saka a tea flask ta ajiye saman table ya fito ɗauke da kayan Maryam da abun da take buƙata suka wuce asibitin.

Anan suka samu Maryam ta farka har lokacin idanunta rufe sai hawaye dake fita.
Wajenta ya ƙarasa ya riƙo hannunta ta buɗe idanunta ta dubeshi tace.
"Ya Faruq babyna."

"Allah zai bamu wani."
Yace ya rufe bakinta da yatsarshi ta juyar kanta tana fitar da hawaye, tana son cikinta taji zafin fitarshi.
Haka dama ake jin zafin fitar ciki? Haka in kaso abu kake jin zafin rasashi?.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now