Part 1/25

4.3K 82 2
                                    

Bismillahir rahmanir raheem dasunan Allah me rahama me jin kaiii godiya ta tabbata ga Allah Wanda yabani ikon rubuta wannan littafii ya Allah kamin jagora acikin abinda nake niya..
Sadaukarwa ga ummee maimuna hydar arab

IHSAN (❤❤❤)).
1
Ruwan sama akeyi mai karfin gaske Wanda yake barazanar tafiya da duk wanii abin da baya killaceh .Rakube take a soron gidan tana rawar sanyii ga kayanta duk sun jike kuma bawanii kayan arziki bane ajikinta ..Hawaye ne kebin kuncinta .. Yarinyaceh kyekkyawa itaba fara ba ita ba bakaba wato tsaka tsakiya doguwa siririya tanada manyan idanu Wanda cikinsu keda launin brown,ga Zara zaran eye lashes inta ,tanada madaidaicin bakii mai dauke da pink lips ,kana iya hango gaahinta ta cikin kerarran hijab inta Wanda yakai har waist inta ...Amma kallo daya zaka mata kasan tana cikin halin talauciii da rashin gata.
Khadeeja kenan Wacce ake kira da (Ihsan) 'ya ce ga Malam Ahmad hydar Allah yayiwa mahaifiyarta rasuwa me suna ( Maryam ) Rasuw tun tana karama yar shekara shida mahaifinta yayi jimamin rasa mata ta garii da yayii bayan shekara daya da rasuwar matarsa dangi suka matsa masa da yayi aure,haka yahakura yayi badan ransa yasoba, saboda bayason wani Abu da zaitaba yar marainiyar dake gareshiiii ....
Toh fan kubiyoniii domin karanta wannan littafi mai abin tausayii,da soyayya....
Queen ceh
IHSAN(❤❤❤❤)
2
A haka take azaune agun har aka gama ruwan bakin asuba ga wata iska mai tsananin sanyiii .
Jikinta duk kyarma yake tana zaune tana gyangyadii har bacci ya kwasheta .

Acikin baccin taji wani marii Wanda yagigitata ,Afirgice ta tashii tana hawaye, inna Hama ceh matar babanta tsaye a kanta tana hucii ta kalleta a wulakance tace kin zauna kina baccin asarah wakika barwa zuwa rafii da yin wanke wanke. Cikin rawar jiki tace inna kiyi hakurii wlh bacci ne yadaukenii bansamu nayi bacciba jiya.

Kallonta tayi tace ai keda bacci mai dadi saidai kiga anayii ,maza ki wuce zafin na miki duka ,cikin sanyin jiki taceh inna banyi sallah bahh ,toh masu addini cewar inna wacce ta ke mata kallon tsana .

Haka tawuce cikin gidan tafara hada kayan wanke wanken tanayi tana sharar kwallah haka tayi tagama lokacin garii yafara haske ta dauki tulu zuwa diban ruwa ga sanyi ga kayanta ajike .

Haka taje tadawo saida tacika randunan gidan gaba daya kafin lokacin yunwa duk taci karfinta sbd rabonta da abinci tun jiya da ranaa.

Tana gamawa ta canxa kayanta xuwa na islamiyya taje gun inna ta tsuguna cikin tsoro da fargaba tace inna zantafii makaranta tace yo mezanmiki tace inna wlh yunwa nakejii,saida ta kalleta shekeke tace ai ubannaki da zaiyi tafiyarsa be ajiyemiki abincibah,idontane yakawo kwallah tace inna kitaimakamin ,tuwon da ya rage na jiya ta tunkudo mata tace gashii kicih yarinya sai taurin Kaiii maikama da aljana kawaiii saura atashii karki dawo kimin tallah da toh ta amsa tatashi tatafii tana tunanin yaushe sauki zaizoma rayuwarta

Wani dattijo na hango zauneh acikin wani babban falo Yana zaune da jarida a hannunsa Yana karantawa kana kallonsa zakaga kamala da dattijontaka atare dashi ga dukiya ta zauna ..

Taku na jiyo a hanyar step Wanda yasa najiyo naga wake saukowa wata matace sanye da atamfah ruwan kore Matar bazatawuce kimanin shekara 50 zuwa 55 bah faraceh Amma ba canba Dan wannan dattijon dake zaune daga ganin alama shine mai gidan yafita haske sosaii .Tanada tsayi ga dogon hancii ga gashin komaidai masha Allah ..

Karasow tayi tace INA kwana alhaji tace lfya kalau harkin sauko taceh ehh yace masha Allah toh ina autannaki .

Kafin tayi magana sukaji motsi dukansu juyowo sukayii suna murmushi ganin dansu daya tilo a duniya nimahh me rubutun saida na jinjina kyau da baiwa irinta Zaharaddeen ..( Deeni)

Matashine Dan kimanin shekara 29 kyekkyawane ajin karshe dogo ne me dogon hanci ga madaidaicin bakinsa maidauke da pink lips ga farar fatarsa fes kamar na mahaifinsa sai sheki takeh ga gashin kansa yasha gyara abin baamagana kanagajinsa kaga asalin kanurii .

IHSANWhere stories live. Discover now