Part 65

605 20 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤🌟🌟💫💫✨✨

Written By
Khadeejaht Hydar ✍🏻
Young Novelist🧕🧕

💫✨FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION✨💫

❤🌟Gidan zaman lafiya,Hadin_kai,da yardar juna Insha Allah🌟❤🌟❤🌟❤🌟❤

Nagode da bibiyata dakuke,kuma magana akan ina typing dayawa shine ,zande kokarta amma yanzu anyi resume kuma ina koyarwa saide kuna manage Tnx All 4 ur support Ana mugun tare🤝❤🔥❤🔥❤🔥❤

Dedicated to My Fanzz
         🌟6⃣5⃣🌟

Ahanya suka rabu kowa ya wuce gida don sanar ma iyayensu mata,Deen na isa ya tadda dukansu a parlour.

Zama yayi kusa da Mama fuska a shagwabe yace".... Habibty nagaji  wayyo kafata,tace"... Aikinme kayi?yace".....babu zama ne yasa kafata ke ciwo.

Yace"... Habibty  kinsan k'iran me Daddy ya min,tace"... A'a saika fada nan ya fad'a mata idansa nakan Ihsan wacce sai alokacin ta d'ago don kallonsa.

Tashi tayi ta wuce d'aki ta fad'a akan gado tafara kuka,uhm ni Tame gari nace to Ihsan kukan me kikeyi kuma.?"

Mama ce tayi murmushi don ganin Ihsan ta tashi,tace".... Allah ya tabbatar da alkhairi,Angel tace".....yea Yaya zairigasu Yaya Hisham aure zamu sha biki wayyo da'di."

Harararta yayi yace"..... Au Fahad bekirakiba?tace"... A'a zatayi magana wayar dake hannunta tafara ringing d'aga kiran tayi."

Fahad yace"... Alhamduliilah Baby Anyanke ranar auranmu yau ansaka wata d'aya,kirjinta ta dafa tare da cewa wat tace".. Amma yaya Fahad bahaka mukayi dakaiba aii ni bazanyi auren ba."

Deen dariya yayi yace"..... Lil sis Ai aikin gama ya Riga ya gama sai hakuri kema kinsan maganarsu Daddy,Da gudu tawuce d'akinsu tana kuka."


Turus tayi ganin Ihsan na kuka kamar ranta zai fita,share hawayen ta tayi tak'arasa kan gadon ta dafata tace".. Sis what happened ko bakyason auran ne?.

Girgiza mata kai tayi zatayi magana kenan Deen ya shigo don lallashin Angel,Shima turus yayi ganin Angel na rarrashin Ihsan.

Tana ganinsa tace".... Bro what happened to sis?beyi mata magana ba sai kallon Ihsan yakeyi  da har yanzu take kuka,Angel ce tafita don atunaninta problem d'in tsakaninsune.

Zama yayi bakin gadon yakira sunanta cikeda nutsuwa,juyowa tayi da oily brown eyes d'inta da yafara ja saboda kuka yace"..... What's wrong with you?"

Cikin sheshshekar kuka tace".... Bakomai yace"....no please kifadamun kinsan danuwarki tawace ko kinason namiki kuka?,Girgiza masa kai tayi yace"..... Then tell me why are u crying?"

Tunowa da Baba da Mama na nayi ana shirin aurar Dani amma babu dangina ko d'aya aciki, Sai yau na tabbatar uwa wata gib'i ce arayuwa rasa uwa na daidai da rasa rayuwa mai inganci da rashin  gata ta karasa tana fashewa da kuka,tausayintane ya kamashi ya janyota jikinsa yana buga bayanta because she need a shoulder to cry on.

Cikin sanyin muryarsa yace".. Plss kidaina kuka insha Allah muna tare dake,Kuma Insha Allah zamu nemi y'an uwanki kinji, kaita gyada masa tana share hawayenta yace"yauwa amaryata ko kefa murmushi kawai tayi.

Yace"... Inason naje wani gu amma yanzu zan dawo,jin haka yasa itama ta shirya tana jiran ya gama ta bishi batare da saninsaba,yana fita itama tabi bayansa.

Mota ya shiga saida ta bari ya bar gidan sannan ta fito tayima Angel wacce ke b'oye abayan flowers alama data fito,tana fitowa suka kama hanya suna zuwa bakin titi suka tari mai napep,sukace dan Allah malam waccan motar mukeso ka bi konawane zamu biyaka.

Jin ance haka ba musu yafara bin motar su Deen uhm nide mace Anty Ihsan inazaku?,Adaidai wani Babban  Hotel Deen,Hisham, Fahad suka sauka,su Angel  kuma suka sauka a d'an nesa dasu.

Angel ce  ta fito ta sanya nikab tawuce ta gabansu Deen ta shiga ciki,tana zuwa ta nemi guri ta zauna,kamar ance kalli can kawai ta hangeta aikuwa da sauri taje  ta sameta  tafara hawaye tace"..... Plss taimakonki nake nema Yaya na yana waje baida lafiya."

Tsaki taja tace"....to what is my business wit u nd ur fucking bro,kamar zatayi kuka tace"....kwatantamin ke akayi,wai ince Inji Deen ta juya zata tafi tayi saurin riketa tace".... Muje ina yake?  Tace"......yana waje."

Ta kofar baya tabi da'ita, suna zuwa waje ta sauke ajiyar zuciya don ganin su Deen sun shiga ciki.

Kallonta tayi tace"... Ina yake?tace"... Yana kwance acikin napep incan tamata nuni da napep d'in da Ihsan ke ciki."

Da saurinta ta nufi napep d'in saurin juyowa tayi ganin babu Deen aciki,kafin tayi tambaya Angel ta sharara mata mari,nikika Mara yau zan nunamiki d'aga hannu tayi da niyyar marinta Ihsan ta rike hannunta ta sharara  mata mari guda  ✌lafiyayyu wanda ya haddasa mata ganin tauraru sun gifta.

Angel tace".... Daga yau se yau inkika k'ara kula yayana  ko kika nuna kinsanshi sai min miki mummunan duka,mezeyi dake banza ballagaza nonsense guntun mazan waje.

Kiyi gaggawar cireshi aranki  donshi nan da wata daya zeyi aure,Kallonsu take ace yara k'anana sun mareta ta kasa ramawa,a zafafe tace".... Nasan wacce ze aura bata kainiba kuma yanzu zannunamuku yadda ake rashin mutunci."

Zatayi magana Ihsan ta cire nikab d'in dake fuskarta ,Angel tace".... Ki kalli Matar daze aura kema kinsan tafiki komai.

Kallon Ihsan tayi aranta tace".. Tabbas yarinyar akwai kyau Amma ta tsuke fuska ta cakumo Ihsan tana kokarin kaita kasa."

Ganin hakanne yasa Ihsan rike kafarta ta kaita kasa ta haye kanta tafara duka,Angel ma tasa hannu sukayi ta dukanta.

Ganin zasu lahanta tane yasaka mai napep d'in shiga gurun da sauri don Neman taimako,abakin gate yaci karo dasu Deen Wanda sungaji da nemanta suka fito.

Da sauri yace" ...Dan Allah kuzo kutaimaka fad'a akeyi acan gun,da sauri suka bi bayansa ,kamar ancema Ihsan takalli can Fahad ta hango ai da sauri tace"... Sis kyaleta gasu bro zuwa  mu  wuce."

Da gudu suka  bar gurin suka barta tana kuka baki da hanci duk jini,Su Deen ne suka iso ganinta yasa su mamaki.

Plss manage

Share
Like
Comments

[1/9, 8:38 PM] Khadeejaht hydar

IHSANWhere stories live. Discover now