Part 40

592 24 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

( Romantic, love,sorrow.)
❤❤💋💋

Written by.
Khadeejaht Hydar.

💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

❤ Gidan zaman lafiya,Aminci ,Hadin kai ,da yardar juna insha Allah ❤

Dedicated to:❤ Aunty zee Allah ya kareki daga Sharrin makiyi,u means a lot to my world!! ❤

         ✨40✨
Da sauri suka bar gurin cikeda fargaba,Suna zuwa bakin titi suka tsallaka..

Yarinyar ce ta hangi wani lungu kusa da wani gida,tace" muje can mu buya kinga dare yayi,kuma mutanennan kan iya zuwa nemanmu nan.

Da sauri suka shige lungun zuciyoyinsu duk a tsorace,Ihsan tace" baki fadamin sunankiba,dame ya fito dake daga gida harkika hadu da waennna mutanen."

Numfashi ta sauke sannna tace" to ina iya cewa tsautsayine yafito dani daga gida,saboda mu bama fita ,daga makaranta sai gida.

Wata cousin dinace takawomana ziyara ,to tana ganin period dinata,ga mummy na bacci,mai aikinmu tawuce gida,yayanmu bayanan."

To" saina yanke shawarar na karbo mata gun wani mai shago kusa da gidanmu."

Na fito saina tadda anfara shiga sallar isha'i."

Na siya na juya kenan,sai wata mota tasha gabana,ni a tunanina ma irin samarinnanne."

Fitowa sukayi su biyu,kafin nayi yunkurin neman taimako, saikawai naganni cikin mota."

To" kinji meya fito dani,nasan yanxu cousin din nawa da mama suna cikin damuwa,gashi Yaya zeyi tafiya gobe baya gida,ga baba ma yayi tafiya,takarasa maganar tana hawaye ."

WASHE GARI

Deen ne da hisham da fahad a airport."
Sun rako fahad zaije wani course, Wanda dad dinsane ya turashi,saboda shi bazai samu damar zuwaba"

Fahad yace" nizan tafi sai Allah yakara hadamu,duk da bazan dadeba amma wlh naji nafara kewarku."

kuma"Dan Allah ga amanar Nafeesa na baku,kada Ku Bari tayi rashin dan' uwa, duk da nasan zaku kula da'ita.

Amma Sam zuciyata takasa nutsuwa, sainakeji kamar wani abu zaisami wani nakusa dani.

Deen yace" nima wlh tunjiya da daddare nakejin faduwar gaba ,na rasa na miye."

Hisham yace" kuna addu'a Allah yasa alkhairine."

Wayar deen ce tayi kara alamun kira,Yana duba mai kiran kawai saiyaji gabansa ya fadi."

Dagawa yayi, muryar mummy yaji ,alamar tasha kuka ta koshi,tace" ina fahad? Yace" gashinan,ko in basa wayar,tace" A'a kuna Barin airport kuzo ina nemanku,yace" to sannan ya kashe wayar."

Fahad yace" waye yakiraka? Mummy ce yabashi amsa.

Fahad yace" lafiya de ko ,yace" lafiya kalau."

Ze kara magana aka fara kiran sunan passengers, dole ya wuce suna dagama juna hannu."

Suna shiga mota deen ya kira mummy, tana dagawa yace" mummy lafiya naji muryarki haka ?

Tace" ina lafiya kuwa deeni ,tun jiya da daddare  nafeesa ta fita batadawoba haryanxu ."

Subhanallahi deen yace" mama aikenta akayi ?

Ina bacci tafita siyoma cousin insu Abu ,shinefa haryanzu babu ita babu labarinta takarasa maganar tare da fashewa da kuka."

Deen yace" kiyi hakuri mummy insha Allah za'a ganta.?

Nan ya kashe wayar, yayima hisham bayani."

Hisham yace" kaga inajin al'amarinnanne yasa mishi faduwar gaba,kaga harya tafi jikinshi nabashi cewa all is not well."

Numfashi deen ya sauke ,daya tuno abinda fahad yace" ( ku kularmin da kanwata)."

A haka suka isa gidan ,kowa da abinda yake sakawa a ransa."

Suna isa suka nufi parlou din mummy,tana zaune jugum babu magana ,ga Hanan azaune itama shiru."

Sallamar su hisham ne ya fargar dasu,mummy ta tashi tace" sannunku da zuwa ,Ku zauna.

Suna zama wayar mummy ta hau ruri,dataga abbansu fahad ne me kira ,hankalinta ya sake tashi ,da sauri ta daga wayar suka gaisa,yace" ya naji muryarki haka,tace" babu komai."

OK daman na bugu infadamiki ina cikin gari tunjiya ,wani aikine ya tsaidani ,amma insha Allah inakan hanya yau ."

Tece" to sai kazo ,ta katse wayar tana hawaye."

Deen yace" barimukai maganar police station, mama tace " to sannan suka fita."

Su ihsan kuwa gari daya waye,saisuka kama tafiya ,har sukazo bakin titi zasu tsallaka.

Sun shiga,tsakiyar titin da niyyar tsallakawa ,amma kaddara tasa wata mota tana zuwa tayi awon gaba da ihsan😭😭😭."

Zubewa tayi agun kamar matacciya,ita kuma Nafeesa ganin ihsan cikin jini kamar bata numfshine yasata sumewa

Jama'a ne suka cika gurin,ana Neman yaza'ayi dasu."

Wanine ya debo ruwa ya zubawa nafeesa,lura da cewa suma tayi."

Tana farfadowa tayi kan ihsan tana ihu,tana Neman taimako.

Wata mota ce tazo wucewa,har motar ta wuce saita dawo baya dan ganin  mutane antaru,wasu na salati,wasu na neman motar daza'a kaita asibiti."

Fitowa yayi daga motar ya nufi gun jama'ar ,Yana isowa suka fara budemai hanya saboda sunsanshi."

Nafeesa ce ta dago danyin magana,kawai sai idonta ya sauka akansa,da gudu tayi wurinsa ta rungumesa tana kuka,sannan tace"  daddy ka taimaka karta mutu,tana zubda jini, itama ta taimakeni."

Rasa bakin magana yayi,meyakawo nafeesa nan? Miye alakarta da wannan yarinyar ta kwance?"

Saurin kauda tunanin yayi aransa,yayi saurin daukarta yasata acikin mota Yakama hanyar wani Babban hospital,saboda yadda take bleeding ( zubda jini)

Suna zuwa akayi emergency da'ita,saboda mai karatu inkaga ihsan bazakayi tsammanin itabace,saboda duk ta sauya.hmm Allah yabaki lfya Ihsan, fans kumata addu'a fa lol.

Bayan anshigar da'ita ne,su kuma suna zaune a inda ake zama ,daddy ya kalleta yace" meke faruwane,anan ta bashi labarin komai,sai kawai yaji Ihsan ta kwanta masa arai,hmmm nace ba dole ba."

Wayarsa ya Ciro a aljihu,ya danna kiran mummy.

Tana ganin kiransa da bazata daukaba ,amma" se tayi ta maza ta dauka ."

Tana dagawa yace,Naga nafeesa ,kuzo muna asibiti,yafada mata sunan hospital din ya katse kiran."

Tanajin ya ambaci asibiti hankalinta ya tashi,atare suka fito tare da hanan."

A harabar gidan sukayi karo dasu Deen,zeyi magana tace" dadynku ya kirani wai yaga Nafisa amma yanxu haka suna asibiti."

Innalillahi suke maimaitawa,daga bisani suka shiga mota zuwa asibiti.

Toh Nina na Shiga motata don inje nagaida :: FAGEN MARUBUTA WRITERS .

TAKU A KULLUM

IHSANWhere stories live. Discover now