63

649 22 0
                                    

❤❤💋💋
*~IHSAN~*
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
💋💋❤❤✨✨🌟🌟

Written By✍🏻
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist🧕.

*~💫🌟FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION🌟💫.~*

*~❤Gidan zaman lafiya,Hadin_kai, da yardar juna Insha Allah❤~*

*~ADDU'AR DA ZAKUYI KAFIN KU FARA ALOLA~*

بِسْمِ اللّهِ

*~Bismillaahi~*

*~In the Name of Allah~*

        Dedicated to
My Bestie. Unique Zara.
So much love.

*~Masoya ina samun sak'onku Allah yabar zumunci nagode sosai.Ana tare.🤝~*

          🌟6⃣3⃣✨

Jin muryar Ihsan ne yasata juyowa tana arba da ita suka tashi ita da Farha suka rungumeta, kawai sai suka fashe da kuka dukkansu ukun.

Meesha tace "....Beatie ina kikaje haka munata nemanki har mun fidda rai", Farha tace "Bestie meyasameki naga kin rame?"

Hawayen fuskarta ta share sannan tace".. Mu zauna labarin mai tsayine,zama sukayi dukansu."

Meesha tace"... Farha ki k'ira su mama kice musu munyi baki,Kafin su mama ta fito Ihsan ta boye abayan Wani Babbar randa."

Su mama na fitowa sukaga  Bak'in nasu  da fara'a a fuskarsu suka karaso,Mama tace " Ah yau kunyi zumunci mun gode sannunku da zuwa."

Mama tace' maza ki kawo musu ruwa da fura,bayan sunsha ne mama tace "... Ya mukaji da hakuri kuma?"

Suka ce Alhamduliilah ya naku hakurin suka amsa da Alhamduliilah, Mama zatayi magana taji ance".. Mama ina wuni."

Da sauri su Mama suka waiga mama  tacema mamarsu Farha tace".... Kinji  menaji kuwa tace"... Kamar muryar Ihsan."

Kafin su k'ara magana sukaji ance  Mama nayi kewarku sosai,Haba su mama kuwa tashi tsaye sukayi sukace"...yau Ihsan tawuce mana   gizo yau harmuryarta munaji."

Ihsna ce ta fito tana dariya Taje ta rungumesu mama tace".. Mama nayi kewarku sosai,cikeda jindadi sukace muma haka y'arnan ina kikaje munata nemanki?"

Tace"... Mama mu zauna tukun zama sukayi mama ta kalli Su Deen tace"... Yaro daman tana hannunku ne ko yaya?"

Anan Hisham ya basu labarin abinda ya faru har zuwa yanzu,Dukansu saida sukayi kuka Mama tace"....Allah yabaki ikon cinye jarabawa y'arnan duka suka amsa da Amin."

Kamar daga sama suka jiyo muryar Inna basu ba harni Deejerh saida naji tsoro,tana zuwa tayi kan Ihsan ta fizgota  saida takusan fad'uwa.

Ta d'aga Hannu zata shararamata mari,Da rawar jiki Deen yayi saurin rike hannun ta.

Juyowa tayi taga wane dan halak dinne ya rik'e mata hannunta,arba tayi da Deen Wanda Blue eyes dinsa ya canza kala zuwa red ganin irin abinda  take shirin aikata masa.

Kwarjini ya mata tayi saurin fizge hannunta ta fara tafi tace"... Shakka babu wato da d'an iskannaki kike yawo ko, to Wallahi yau kuma yanzu zan d'aura miki Aure da Lado muga karshen yawon karuwanci.

Kuka take kamar ranta zai fita,jikinsu  Mama ta fad'a tana kuka kamar antsikerata ta tashi taje gaban Deen takama hannunsa tace"....please mu tafi karta dawo."

Ya d'ago  idanunsa ya kalleta kawai hoton fizgar da mama ta mata yake gani a idanunsa ,ya rintse idanuwansa ya bude yace".... Babu inda zamuje muna jiranta."

IHSANWhere stories live. Discover now