Part 36

565 23 0
                                    

❤❤💋💋IHSAN❤❤💋💋
36
By Khadeejaht hydar .

Shiii ,yasa hannu akan labbanta ,sannan yaceh  ki musu addu'a shine abinda suke bukata ,taceh toh,.

And karki kara cewa bakida kowa kinada Allah sannan ga mummy da daddy gasu meesha ga Angel ga kuma nii.

Murmushi tayi taceh nagode Allah ngd maku ,taceh Amma bakafadamin me yasaka rama ba kuma ka kara haske,yaceh banda lfya ne ,tace meyasameka ,shiru yayi yana kallonta ya zuba mata browny eyes dinsa masu kamar me bacci,yaki mgna a hankali ta janye idanunta sbd Sam bazata'iya jure kallon cikin idanunsaba,.

Juyawa tayi zata koma ciki  harta fara tafiya ya kira sunanta a sanyaye ,juyowa tayi Amma bata karasoba, zuwa yayi har gabanta ya tsaya yaceh Khadeejer look into mah eyes ,dagowa tayi ta jefa idonta anashi haka suke kallon juna kowa da abinda yake rayawa a zuciyarsa,

Yaceh plss Khadeeja ,dagowa tayi jin yadda yakira sunanta ,yaci gaba plss don't leave me,mah happiness is u ,am nothing without u,promise to love me in good or bad tyms,am ready to face any task because of u ,my life will be totally ruined without u in my kingdom..

Kallonshi take kamar wani sabuwar halitta a hankali taceh I promise to stay wit u for d rest of mah lyf until death do us apart .

Ajiyar zuciya ya sauke damuwa akan fuskarsa yaceh ::; yaceh mushiga daga ciki nayima su mama gaisuwa .

Tana gaba yana bayanta suka shiga ,lokacin kuma daddy da mum suna niyar fita ..

A tabarma ya zauna Yana me gaida su mamansu farha sannan ya musu ya hakurin raahin baba,sukace alhmdulilah..

Meesha ce ke bawa farha sign yadda deen ke kallon ihsan..

Angel ce ta furta ahankali  yadda su ka dai zasuji ,taceh gulma ajali ,murmushi sukayi dukansu banda su mama  dabasusan me akeyiba ..

Deen ne yatashi yace musu saida safe sannna Angel ma tamusu sallama suka fita ,..

Farha tace  am ihsan bazaki rakasu ba ,cikeda da kunya ta tashi ,tabi bayansu,,..

A bakin mota ta hangi shi da Angel ,Angel ta ganinta tashige mota,ita kuma takasa karasowa shiya karaso gunta ,tsayawa yayi yana kallonta ,dataga baida alamun mgna tacemai kaga su mama sunajiranka,,yaceh ba damuwa bari inje nace musu su tafi ,tayi saurin kallonshi tana girgiza kai,tace mai Aa gskiya ka tafi,kaga bakada ishashashen lfya,yaceh to zantafi ,kifadamin Abu mai dadi taceh inka dawo gobe zan fadamaka ,ya bata fuska yaceh shikenan tunda daman ba so na kikeba sai anjuma tayi saurin cewa toh zanfada Amma ka rufe idanunka rufewa yayi sannan taceh ..UHIBBUKA HUBBAN SHADEEDAN( INA SONKA SO MAI TSANANI) ANTA FAKAT FIL HAYATEE( KAI KADAINE ARAYUWATA ) Tana gama fada ta gudu zuwa cikin gida tabar shi nan tsaye ,horn in dayaji ne yasashi bude ido ,yaga wayam bb kowa murmushi yayi ya shiga mota ,suka wuce ..

Tana shiga ta zauna taceh mama inason nayi wata mgna,Amma saisu baba sun shigo,suka CE to Allah yakaimu ..

Bayan magriba su baba suka shigo gidan ,bayan kowa ya zaunane ,ihsan tace baba daman kafin baba ya rasu  ya bani adress din yayan mama ,nan tagayamusu yadda baba yafada mata.

Dukda sunacikin jimamin mutuwa hakan bai hanasu jin dadi cikin ransuba ,yau ga ihsan da wasu yan'uwa .

Baba yaceh insha Allah,zamu bincika Allah yasa muji alkhairi sukace amiin.

Nan su farha suka koma gidansu akabar ihsan agidansu meesha .

Haka rayuwa taci gaba  da tafiya yau kwana 7 darasuwar  baba , kuma har lokacin ihsan bata koma gidansuba..

Da safe ne akayi abin sadaka na kwana 7 da rasuwar baba .

Da azahar tana kwance tana tuna babanta , hawayene suka gangaro mata ,tana sharewa,meesha tayi sallama ,batajiba saida ta dafata tukun ta juyo ,zama tayi kusa da ita  taceh haba ihsan kiyi hakurii kibarwa Allah komai ..taceh  insha Allah zandaina ...

Yauwa su yaya deen sunzo fa shine nazo nafadamiki...

Da sauri taceh dagaske taceh ehmana,tashi ki shirya kije ,to taceh sannan tasaka kayanta sannan tadauki hijab blue har kasa ta fita .

Tana fitowa  ta hangi su su uku,hisham,fahad,da gwarzon nata .
Suna sanye cikin kaya iri daya farare deen ne atsakiyansu .

Tundaga nesa ya kafeta da idanu,harta karaso ta gaidasu tana sinne kai, hisham da fahad ne suka amsa,shikuma bai amsa ba illa  kafeta da ido dayayi,dagowa tayi don tasake gaidashi, idonsu ya sarke cikin na juna,tayi saurin kauda kanta gefe,tana gaidashi amsawa yayi Yana murmushi..

Su hisham kuwa ganin deen ba bari zeyi su gaisaba yasa  sukayi gyaren murya ,juyowa tayi gunsu hisham tana mai murdama deen baki..

Gaisuwa sukayi mata da mata nasiha,sannan suka shiga cikin motar,.

Juyowa tayi gunsa tayi alamar kuka taceh shine run rannan baka dawoba koh takarashe mgnar da turo bakinta ..

Kallon fuskarta yayi ,yaceh yemmata inason shagwabar nan taki ,Amma kafin muci gaba dazu wa kika murgudawa baki ,taceh nikuma nikam banyi komaiba .

Yaceh yarinya zakiyi bayani ne innafasamiki bakin muga nacin abinci,don naji ance ke acici ceh ,ta kwabe fuksa taceh nikam ba acici bace saidai kaii..

Daman ance duk marasa jiki sunfi cin abinci,dariya yafara yaceh to kenan kinfini ci tunda bakikaini kiba ba ,taceh Aa fah ,taceh meyasa bakazo da kanwarka ba yaceh ,yanzu ma batasan nazoba databini ,innazo daita bazata bari naji dadin fira ba,,..

Taceh uhm pls kazo da ita gobe yaceh tohm ,suna tsaye sai kawai sukaga mutum akansu.

Lado ne   a tsaye Yana huci akan su yanunata yaceh ,kinsan ankusa mana aure shine zakizo ki tsaya da  wani gardi .

Kallonshi tayi  taceh kai Malam dakata min yaza'ayi kazo kana mana hauka anan.
Ba deen ba harda su hisham saida sukayi mamakinta ,lado yaceh wanene shi taceh Mijin da zan aurane wannan don haka kayi gaggawar cireni aranka donni bazan auri Dan iska irinkaba .

Ido Deen ya zaro😳😳. Kafin ya ankara saiyaji karar mari ,lado ne ya tsinkama ihsan mari kafin deen yayi wani yunkuri har ta tsinkama lado maruka 2 a fusace taceh kada ka kara gigin tabamin fuska ..

Ya harxuko zeyi kanta da fada deen ya tateshi yaceh karkaga namaka shiru inkayi wani Abu yanzu zankiramaka yan sanda .

Jin an'ambaci  Dan sanda yasa ya wuce simi simi yaceh wlhh  nanda kwana 5 za'a daura mana aure ..kunsan jama'ar kauye da tsoron police lol.

Deen me yabata hakurii itama tabashi sannan yaceh wanene.nan tafadamai ,komai ,ahaka suka taba hira ya mata sallama tare da bata kudi ,fir taki karba saida ya nuna bacin ransa tukun ta karba,tana masa godiya,yamata sallama ya wuce ta koma gida..

Abangaren inna kuwa lado yaje yafada mata abunda yafaru sai ta cemai karya damu ai saura kwana 5 saga ta tsiya lol anya kuwa inna .
Muje zuwa.

IHSANWhere stories live. Discover now