Part 45

563 20 0
                                    

💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

( Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💋💋✨✨

Written By
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist ✍🏻

💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

❤Gidan zaman lafiya,Aminci,Hadin_kai,da yardar juna insha Allah ❤

Dedicated to : My WhatsApp Group.

✨45✨

Suna barin airport kauyen su ihsan suka nufa ,Baba da Nafeesa kuma suka wuce gida.

Suna isa a kofar gidansu ihsan suka sauka, Sun dauki tsawon minti talatin basu samu Wanda zasu aika ba.

Kamar ance hisham ya juya,sai ya hangi Farha na kokarin juyawa.

Ganin zata wuce ne yasashi kiran sunanta,juyowa tayi ahankali batare da ta iso gunsu ba.

Saida hisham yace"karaso mana,tukun ta karaso ta tsaya suka gaisa."

Hisham yace" ina zakije haka kike ta sauri? Tace" wallahi mama ce ta aikeni shine nake sauri nakaimata."

Yace" okay to ,Dan Allah kimana alfarma daya kikiramana Kawarki saiki wuce."

Juyowa tayi gun Deen wanda tun bayan gaisuwar su bai sake magana ba,tace" Uhm Yaya bata fadamaka zatayi tafiya ba?

Kallonta yake,kafin yace"tafiya kuma zuwa INA?"

Tace"wani kauye taje jiya amma yau zata dawo,taje gun kanin inna ne."


Tana fada ta juya zata wuce Deen yakirata,juyowa tayi tana kokarin mayar da hawayen dake shirin zubo mata.

Amma batayi nasaraba, don hawayen sun samu nasarar zuba.

Deen ne ya kalleta na tsawon minti biyu ,kafin yace"Dan Allah kifadamin gaskiyar al'amari jikina na bani ba lafiya ba."

Tace" yau kwana biyu ✌
Kenan ba'a ga Ihsan ba,munyi nema har mungaji babu labarinta .

Anan ta fadamai komai, jiyayi kamar an doka masa guduma a kirjinsa.

Kasa magana yayi,sai hisham ne yayi karfin hakin tambayarta yace" to bata fadi inda zataje ba?

Tace" eh to kafin Baba ya rasu ya bata adress din yan'uwanta,kuma a takardar data bari ta nuna cewa zataje neman yan'uwanta ne.

Sai a lokacin Deen yayi magana, yace" ko zamu iya samun copy in takardar."

Tace" to muje gidansu meesha,mu tambaya ko zamu samu,

Haka suka tafi jikin su asanyaye,suna isa suka tadda meesha da mama a zaune a tsakar gida.

Da sallama suka shiga,Meesha ce ta dago jin muryar Deen, gabantane yabada rass,tana tunanin yadda zai dauki zancen.

Amma ganin yanayinsu yasata gane cewa sun San komai,tabarma mama ta shinfida musu.

Ananne Hisham yayima mama bayanin komai,jinjina kai tayi cikeda tausayinsu sannan tace" Abin tsoronma shine,yanzu ko ta samu yan'uwannata ko kuma yaya ne.

Ta cigaba da cewa ko awane hali take? Gashi anrasa takkadar da Address din ke ciki,mum nema sama ko kasa ba'a samuba.

Gaban su hisham ne yabada rass,jin ba'asan inda takaddar takeba.

Mama tace" yaro Allah yabaka juriya ,Allah yasa ka ganta ,Allah ya aiko ka cikin rayuwar tane don ka zama Noor a rayuwarta.

Hawaye ne tab a idon mama,saboda tana tsananin tausayama ihsan ko dan maraicinta.

Sallama suka musu,haka suka wuce gida cikeda damuwa.

Su IHSAN kuwa suna isa motar asibitin suka zo daukarsu,direct special ward aka kaita .

Randa suka isa,ranna fara bata treatment saboda yanayin jikinnata ga idanuwanta da suka kumbure saboda buguwar da tayi.

To Alhamdulillahi washe gari ansamu idonta ya washe ,tana iya ganin mutane.

Da safe tana zaune abakin gado,mama ta shigo tace" sannu y'ata ya jikinki tace" da sauki mama,to madallah Allah yakara sauki.

Likitan ne ya shigo ya dubata ,yace" ma mama abata tea mai kauri,don anjuma anason shiga da'ita dakin tiyata.

Mama ce ta taimakamata tayi brush,sannan ta hada mata shayi tabata tasha.

Tana gamawa likitan ya turo a dauketa a keken guragu,haka aka dauketa akayi dakin tiyata da ita mama na mata fatan alkhairi..

Abangaren su Deen kuwa suna isa gida,bangaren iyayennasa ya tafi,yana zuwa ya fada jikin dadynsa yace" Daddy naga samu naga rashi.

Atare suka dago suna kallonsa,mama tace" kamana bayani yadda zamu gane mana.

Anan ya basu labarin komai,kowa agun seda ya tausayama Ihsan da Deen.

Angel ce ta share hawayen daya zubo mata tace" bro nafasa tafiya dasu ikram gobe,zan zauna munemo ta.

Ikram ma tace" nima nafasa tafiyar,zamu tayaka neman sis Ihsan.

Thank you lovely sisters, Amma dakagansa kasan yana cikin tashin hankali.

Washe gari da safe ummi da Fatima suka koma yamal,aka bar ikram.

Abu kamar wasa su Deen sun bincika amma babu labari, A can kauyema kullum cikin cigiya suke.

Wata safiyar lahadi Deen ne yafito cikin blue jeans da farar T_Shirt yayi kyau mutuka,amma duk ya rame sai hasken daya kara.

A dining area ya tadda kowa na gidan ana jiransa,zama yayi ya gaida iyayensa,kannensa kuma suka gaidashi.

Daddy ne yakalleshi yace" haba son kayi tawakkali mana kayi hakuri inda rai da rabo,mama tace" insha Allah za'a ganta kaji.

To dahaka yaji zuciyarsa tamasa sanyi,ya saki ransa ya danci Abinci.

Amma sede me yana tashi kawai sai gani sukayi yafadi kasa sumamme,ihu Angel tasaka tana jijjigashi amma inaa kamar macecce haka yake.

Ruwan sanyi aka debo aka watsa masa amma shiru kakeji,hankalin iyayennasu ya tashi da sauri baba ya daukeshi yasa shi a mota sai asibiti.

Young Novelist ce Ae

IHSANWhere stories live. Discover now