part 64

569 19 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💋💋✨✨🌟🌟

Written By
Khadeejaht Hydar.✍🏻
Young Novelist🧕🧕

💫🌟FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION🌟💫

❤🌟Gidan zaman lafiya,Hadin _kai da da yardar juna Insha Allah🌟❤🌟❤🌟❤🌟❤

Dedicated to
My Precious Deary Muhammad (Namari Jnr)❤🔥❤🔥❤🔥


Naga sakonku y'an Group D'in Zama Na Amana Nagode Allah yabarmu tare🤝🤝🤝


🌟6⃣4⃣🌟

Bayan yasamu bacci su mama suka koma bangarensu,Ananne Hisham ya nemi ganin Ihsan.

Bayan tazo yace" Khadeeja Inaso na miki wata tambaya kifad'amin gaskiya shin Deen ya taba Nufarki da wani mummunan hali?"

Tace"....A'a yace" to abinda ya faru d'azu atsakaninku ba laifinsa bane,cikeda mamaki take kallonsa aranta tace"....to laifin waye?"

Kamar yasan me take fada yace".....D'azu Bayan munje gun party.....Nan de ya fad'a mata yadda akayi,Ta yadda kuma ta kudircewa ranta saita koyama Yarinyar hankasallamaTace"....Shikenan komai ya wuce,yace"....dafatan anjuma zakije ki duba shi. "

Tace"....Insha Allah, ya mata sallama ya wuce.

Komawa tayi tana tunanin yadda zataci uban yarinyar,uhm Ihsan take it easy mana.

To Alhamduliilah daya farka komai ya sakesa sai a lokacin ya tuna da abinda ya faru,rik'e kansa yayi cikeda takaici ko ya Ihsan zata d'auki abin?"

Mama ce tace".... Angel kuzo ku dubo Yayanku ko ya tashi, to suka amsa sannan suka nufi part d'insa."

Da sallama suka shiga parlour bayanan,don haka suka kama hanyar bedroom d'insa.

Suna shiga yana fitowa daga wanka towel d'aure a kugunsa,fita sukayi don bashi damar shiryawa.

Sauri_sauri ya shirya sannan ya fito,samunsu yayi zaune akan kujera.

Ya jiki suka masa ya amsa amma idonsa nakanta don ganin yanayinta,Angel ce tace".... Sis jirani anan bara inje nakira mama."

Tana fita dama kamar yana jiran ta fitane ya taso ya zauna kusa d'ita,zeyi magana tace"... No need to explain naji komai Allah yakiyaye gaba."

Dad'i yaji ganin komai yazo mai da sauki ba yadda ya d'auka ba,Yasan bame masa wannan sai Hisham that's why he is proud of them.

Murmushin jindad'i yayi yace".....tnx for ur understanding me,Insha Allah zan d'auki mataki akanta."

Tace".....Uhmm Ka kyaleta kawai kallonta yayi yace"...kamarya? Tace".....A'a cewa nayi ka kyaleta taje itada halinta."

Yace"...To shikenan tunda kince A kyaleta,zatayi magana su Mama suka yi sallama suka shigo. "

Mama tace" ...ya jikin yace"... Da sauki to madalla ga abinci kaci kasha magani,Yauwa Babanku yace".. Gobe kasameshi a guest House."

To Allah yakaimu,Amin suka amsa sannan suka masa sallama suka fita.

Lumshe idanunsa yayi yana tuna moment d'insa da Cutie d'insa,yace"...wannan yarinyar taso ta jefani cikin halaka kwafa yayi yaci abinci yasha magani ya kwanta."

Next Day(Washe Gari)
❤❤❤❤❤❤❤❤
Zaune suke suna breakfast bayan sun gama Abba yace"... Dafatan de kaji dakona,yace"..... Eh Insha Allah ina gamawa zantafi."

Abba yace"... Kuma bance ka biya ko'ina ba,yace"... Toh Abba.

Abba ne ya fara fita shima yana gamawa ya fita,a kofar fita sukaci karo da Ihsan gaidashi tayi tawuce murmushi yayi ya wuce.

Yana isa ya tadda su Fahad kowa da daddynsa,gaidasu yayi ya zauna yana jinjina abinda yasa aka tarasu.

Kowa cikinsu ya nutsu musamman Fahad, inkukaga Fahad sai Ku rantse ba shine wannan mai dariyar ba. Kunsan iyaye maza ba wasa.lol

Bayan Bude taro da Addu'a Babansu Fahad wanda shine babba yace"... To Alhamduliilah rana bata k'arya saide uwar d'iya taji kunya."

Alkawarinmu ya cika don haka kowa ya fad'i wacce ya tsayar,Inba hakaba kunsan sauran.

Shiru sukayi bawanda yayi magana uhm Ashe de su yaya Fahad anada kunya lol 😜,Daddy yace"....Ku muke jira fa.

Hisham ne yafad'i tasa ( Fatiman yamal) sai Fahad( Anty Angel 😜) sai oga Deen(Baby Ihsan)❤.

Hamdalah sukayi gaba d'aya sannan aka yanke aure wata 1 tunda duk 1 suke,Baba yace"... Saiku fara shirye_shirye."

Dadynsu Deen yace"... Ni kyauta ta agareku itace gida,na dad'e da gina muku shi babu Wanda yasani don haka duk randa kuka samu dama kuje Ku gani.

Godiya sukayi sannan Babansu Fahad yace"...na dauki nauyin gado da kayan d'aki, Masha Allah nanma sukayi godiya. "

Dadyn Hisham yace"... Nikuma na muku alkawarin zuwa hajj da kasashe 2 waenda kukeso,godiya suka dinga yi daga karshe suka bama iyayennasu waje.'

A hanya Deen yace"... Allah yasaka ma iyayenmu da alkhairi ,yabasu gidan aljanna Ameen suka amsa duka.

Share.
Comment.
Like.
4 comments.07016167938

IHSANWhere stories live. Discover now