Part 72

587 22 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💫💫💋💋🌟🌟

Written By ✍🏻
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

💫🌟FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION🌟💫

❤Gidan zaman lafiya ,Hadin_kai da yardar juna Insha Allah❤

Dedicated to
ZAINAB(Xee) 👏 4 everitin. eally ppreciate

Allah ka k'ara mana son Annabi Muhammad S.A.W.   Allah ka karemu daga mak'iya da mahassada...

          
       🌟7⃣2⃣🌟

Tace".... Allah yasa yace"... Amin can't wait to see mah blood  sister daughter, murmushi tayi tace"..... Muganta mu had'a auranta da fahad saboda inason yarinyar tun tana k'arama rabonmu da'ita.

Daddy yace".... Wane fahad kuma shida yakeda matarsa tace".... Sai ya k'ara don gaskiya bazanso ta auri wani a waje ba."

Uhmm wata Sabuwa inji y'an caca.

Washe gari  su Ihsan suka koma b'angarensu bayan sunyi girki su duka sukaci anan b'angaren Hisham,suna  zuwa b'angarensu  ya nufi d'akinsa donyin wanka .

Binsa tayi atare  suka shiga d'akin ya juyo yace"....uhm kije kiyi wanka namaidaki b'angaren Hisham zamu tafi station.

A shagwaba tace".... Ni bazan iya zuwa ba kaje kayi saika rakani naje nayi nawa,yace"....A'a kode muje muyi tare?kafad'a ta mak'e tace".... A'a ni banaso.

Murmushi yayi yace"...zanga ranar dazaki daina jin kunyata ,tace"... Uhm uhm kaje nide band'aki ya shige baidadeba ya fito."

Yana fitowa ya taradda ita a bakin kofa tana jiransa,dariya yayi yace".... Mutum tsoro kamar farar kura tace"... Uhm naji de muje ka rakani nikam."

Kok'arin sakin towel d'in jikinsa yake niyyaryi saboda yasaka kaya,baya ta juya masa saida yagama sawa ta juyo yace"..... My Queen Muje inraka sarkin tsoro."

Kallonsa tayi ta had'e fuska ,sanye yakeda shadda  fara tas Mara nauyi harzaka iya gano farar singlet d'in dake ciki ga uban sumarsa baki k'irin yasha gyara sai kyelli take ga sajensa ya gyara kamar wani balarabe.

Gira d'aya  ya d'aga mata yace".... Yada kallo hakane kuma kinhad'a fuska?, tace"......yanzu haka zaka fita yace".... Banganeba tace".....mata su dinga kallonka ni banyardaba"

Murmushi yayi ganin y'an kishinne suke kusa yace"..... To yanzu mekikeso ayi tace".... Kawai ka fasa tafiyar yace".... Uhmm akawo mana hari kice karnaje naga waenda suke niyar kasheni.".


Batayi magana ba tawuce ciki binta yayi yace"..... Nina wuce da sauri tajuyo tace".... Banfayi wankaba yace".... Naga kamar you are angry tace"... Am not Amma tare zamu tafi yace".... To naji muje kiyi wankan da murmushi a fuskarta ta shige bathroom don wanka.

Bata dad'e ba tafito tashirya suka koma b'angaren su Hisham,Already su Hisham najiransa don haka yana zuwa suka fita har mota matannasu suka rakasu.


Fuska ta had'e ganin ba halin zuwa ganin hakane yasashi fitowa daga motar yajata gefe,Yace".... Kinga bawacce zan kula kuma kinga su Fatima NA gida kuzauna bazamu dad'eba  mezan kawomiki? Tace".... Chocolate da ice_cream( So fans IHSAN d'inku chocolate lover ce Irina lol)

Yace".....toh baby na saina dawo tace"... Allah ya kare yace".. Amin,nan suka fita su kuma suka koma b'angaren Hisham.

Angel tace".... Mutum sai shagwaba kamar yaro Ihsan tace"... Uhm wai kura zecema kare maye,dariya dukansu suka saka.

D'aki suka shiga suka kwanta dukansu saboda jiya kowa tsoro yahanasa bacci,Bayan awa d'aya  da kwanciyarsu Angel ta farka donyin fitsari d'aga kanta dazatayi taga mutane sunnufi b'angaren su Ihsan da alama harda mace a cikinsu.

Juyowa macen cikinnasu tayi donyima mazan magana,rass gabanta ya fad'i ganin wacece bakowa bace illa wannan budurwar dasu Angel suka duka.

Dakyar ta tashe  su Ihsan tanuna musu,firgici,tashin hankali da tsoro ya shige su.

Suna tsaye suna kallon window harsuka  fito suka komab'angaren  fahad,ganin insuka tsaya zasu zo duba b'angaren Hishma yasasu fita zuwa parlour.


Suna tsaye suna Neman mafita  sukaji alamun buga kofa ai a 360 suka shige kitchen, suka rufe jikinsu sai b'ari yakeyi.

Ihsan ce taduba kozataga irin k'ofar dake kitchen d'inta da sauri ta bude suka shige ta kulle.


Suna zuwa kofar d'akin Hisham sukaga akwai security,Fatima ce ta bud'e da kyar don har sunfara hawowa sama.

Suna  shiga akan idon budurwar tace"....gasy can Ku bisu Ku kamomin wannan mai kamada Y'ar sadaka yalla da wannan mai zubin aljanun.

Su kuwa suna shiga suka saka security suka rufe, hamdala Fatima tasaka ganin wayarta nan tak'ira layin Hisham baya shiga layin Fahad ma haka hankakinsu duk ya tashi gashi sai buga k'ofar akeyi.

Layin Deen tak'ira  yashiga yana d'agawa ta mik'awa Angel da sauri ta karba tafad'a masa cikin tashin hankali ya sanar ma su Hisham A firgice suka nufo gida suna tunanin waye waennan suke takawomusu hari haka.

Sun kusa b'alla k'ofar ne su Deen suka shigo falon tare da y'an sanda,Sama direct suka nufa a lokacin duk sun ajiye bindigoginsa suna neman bud'e kofa.

Kawai sai sukaji ance!! Hands upp, Da sauri wani daga cikinsu yayi niyar d'aga bindiga daya daga cikin y'an sandan yace".... If u try anything stupid am going to shoot ur head jin haka yasashi  fasa d'aukar bindigar.

Fatima ce ta bud'e kofar d'akin tafito a guje hakama Angel,Ihana tazo wucewa budurwar nan ta rik'e mata hijab tana kok'arin bude robar hannunta,ganin hakane yasa Deen ya iso gun da sauri kuma azuciye.

Dai_dai nan tayi nasarar bud'e robar tana kok'arin zuba Mata a fuska da zafin nama Deen ya tureta ya fisge Ihsan daga rik'on datamata.

Turetan dayayi ne yasa abin dake cikin robar a zubarmata tun daga fuska har wiyanta,wani wawan ihu tayi Wanda yasaka Kowa zuwa gunta da wuri saboda nanda nan harta fara canza kama.

Deen a zafafe yasa k'afarsa ya tureta yace".... How dare you kina    nufin matata kikayi niyyar zubawa acid a fuska.

Kowa saida yayi shock jin zancen Ihsna kuwa jikin Fatima tafad'a tana kuka,nan suka Hau rarrashinta y'an sandan  suka tasa k'eyarsu aka nufi station ita kuma aka nufi asibiti da ita.

Toh bayan wahalar da y'an ta'addan farko sukasha sukace inna ce ta aiko su su kuma babu maganar shaida tunda tare sukazo da uwar gayyar.

Inna na zaune   taji sallama amsawa tayi tace".... Waye?,shigowa sukayi su uku sukace anbamu damar kaamaki daga hukumar y'an sanda so Madam you are under arrest."

Cikeda masifa tace"....yo ni nasan wani yaren dakike ganin zata b'ata musu lokaci ne yasasu saka mata handcuff tana ihu haka suka sata a mota.

Su Deen kuwa duk yabi ya rikice don Ihsan sai kuka take,dakyar yasamu tayi shiru, Hisham yace".... Kawai muje mu sanar a gida abin dake faruwa haka suka tashi a mota d'aya dukansu suka kama hanyar gidansu Fahad.

Suna isa mama na zaune a parlour da sallama suka shiga ta amsa musu da fara'a tace".... Sannunku yau kune  a gidannamu.

Ganin yanayinsune yasata tambayar lafiya? Nan Fahad yafad'a mata  komai , fad'a tafarayi  tace"....yaza'ayi Ku zauna ai tun farko yakamata Ku sanar.

Kallonta takai gun Ihsan dake kusa da Deen,saurin mik'ewa tayi don ganin kamannin a fuskar Ihsan bakinta na rawa ta furta Khadeeja!!!!!

Tnx u all fans hrt u much
Ur du'a is needed plss going 4 a mission.
Tnx 👏👏👏👏👏👏
[1/18, 9:48 PM] Khadeejaht hydar Novelist

IHSANWhere stories live. Discover now