Part 67

605 18 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic,Love,Sorrow)
❤❤💋💋💫💫✨✨

Written By
Khadeejaht Hydar ✍🏻
Young Novelist🧕

💫🌟FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION🌟💫

❤Gidan zaman lafiya,Hadin_kai da yardar juna Insha Allah🤝.

Dedicate to
Sayner Nasir  wannan page d'in nakine inayinki sosai

        🌟6⃣7⃣🌟

Ilimantarwa:
Kuma kada mutum yace" sai Allah ya shiryeni zandaina sab'o ,saboda yin hakan Yana daga alamomin y'an wuta,da tab'ewa da kuma b'atar Baseera.
Allahumma Ajirna Minannar.🤲🤲🤲

  Suna isa cikin hall d'in aka musu jagora zuwa inda aka tanadarma amare da Angwaye,Bayan kowa ya zauna ne MC ya bud'e taro da Addu'a sannan akafara gudanar da Shagali yadda yakamata.

Nan aka bukaci kawar kowace amarya tazo ta bada speech akan kawarta,Wow Meesha ce ta fito sanye da kaya irinnasu Ikram wato na gidansu Deen,Tana sanye da gown pink daga takalminta,D'an kunnenta,da flat shoe d'inta duk blue ne Masha Allah tayi kyau ba magana.

Fitowa tayi ta tsaya agaban jama'a tafara da addu'a sannan tafara bayani kamar haka, Khadeeja M hydar is a great friend,My childhood Frnd she is NYC nd caring Beautifull nd innocent.

Nd also I knw Bro Deen will be proud to have her as wife nd mother to his children nd Insha Allah she will be a good In-law, she can cook very well I wish all of u will come to her precious  home to eat her meal Thank u.

Rap rap aka hau mata tafi,ikram ma tafito tayima Angel ,saiga Antii Deejat Abubakar tazo tayi represent d'in na Fatima lol.

Bayan kowa ya zauna sainaga wani  yana tashi anata gud'a,Da kyar na samu na'isa gun saboda yadda mutane suka taru kome suke kallo Allahu A'alam.

Da'isata gun kawai sainaga dandazon Mutane sunkai trailer guda  Ashe su Antee Deejat ne Fans d'in  Khadeejaht Hydar ,Can na hangi Fauziyya Muhammad tasha anko tamaida hankalinta gun kallon Deen uhmm nace kwalelanki,daga baya nahangi sayner Nasir tana kwasar shoki uhmm Ashe de su sayner an iya rawa.

Sunana naji ank'ira ina juyawa naga y'an group d'in Zama na Amana suma sunxo sai kyalle suke to duk mungode harda su gayyar karere su oo duk muna godiya 😜😜😜😜

Bayan kowa ya nutsu aka bukaci Kowane ango yafito yayi rawa da amaryarsa,Hisham ne yafara fitowa da Fatima jama'a aka hau tafi nan aka sa musu waka  Sun d'an taka ba laifi,Sai Fahad da Angel ganin wacce tafitone aka saka ihu don ansan gwanar rawace  ,ana sa musu kid'a suka fara rawa jama'a nata ihu don gaskiyar rawar tasu tayi.

Deen da Ihsan ne karshe  don haka da'aka k'irasu taki tashi,da kyar ya tadata suka fito nan aka samusu kid'a Rike hannunta yayi yana rawa a hankali in a romantic way  garin rawa tayi kamar ta fad'i yayi saurin riketa kawai sai jama'a suka saka tafi a tunaninsu style ne haka suka koma mazauninsu masu vidio nayi masu camera nayi.

Abinci akayi na kece raini  serve ur self kowa yaci yasha ya karbi gifts ba adadi,an raba pic d'in amare da angwaye.sai da karfe 7 aka tashi bayansu  Deejat anyi selfi da amare da angwaye.

To Alhamduliilah Washe gari Yakama alhamis kuma aranar za'ayi walima, Amare suka  saka abaya baka mai silver stone ajiki yaji ado da hijab karami fari sunyi kyau matuk'a ,Angwaye kuma suka saka alkebba da farar hula wow fans inkuka ga su Deen kamar larabawa.

Walimar ta samu halattar manyan malamai maza da mata,Inda wata malama tazo tayi jawabi akan zaman aure jikin kowa yayi sanyi agun saboda wa'azin yayi matuk'ar shiga zucuyoyin mutane.

Haka dai akayi walima cikin birgewa da nishad'i kowa ya samu kyauta kala_kala,haka taro ya watse imani hak'ara shigan mata .

Washe gari yakasance d'aurin aure Mazan gida kowa na shirin zuwa d'aurin aure, unguwar tacika mak'il da motocin manyan mutane,ciki kuwa harda Governor yobe,da sarakunan karkara Dana birni.

Masallacin babbane  amma mutane ancika sosai,Angwaye na hango sai washe hakora suke sunsha farar shadda gazna mai tsada,ga hula da takalma duk farare Masha Allah.

Karfe goma   dai_dai aka d'aura auren Hisham da Fatima,Deen da Khadeejaht, Fahad Da Nafeesa akan sadaki dubu hamsin.

Abokan arziki sai tayasu murna ake,wata matace ta shigo cikin gida tana gud'a cewa take Allah yayi yau and'aura aure Allah yasanya Albarka.

Kuka Ihsna ta fashe dashi don tuno da iyayenta datayi yau ranar aurenta ranar farincikinta amma babu iyayenta ko danginta,kuka takeyi na fitar hankali anyi lallashin Sam tak'i.

Ganin yadda take kukana yasa Angel shigewa band'aki ta kira Deen ta sanar masa,hankali atshe yabi kofar baya ya shigo d'akin nasu,suna ganinsa suka koma daya d'akin saurin zuwa gunta yayi ya dafata yace"....Sweet hrt meyafaru kobakya faeincikin wannna ranar ne ya tambayeta a raunane.

Ganin yanayinsane yasata fad'awa jikinsa tace"..su Baba na tuno ace yau ranar aurena babu wani nawa agun kuma....bata karasaba kuka yaci karfinta  rungumeta yayi yana bubbuga bayanta yana fad'a mata kalamai masu dad'i.

Lafewa tayi ajikinsa  tana sauke ajiyar zuciya ya d'agota yace"... Kimin alkawarin bazaki sake zubda hawayenki ma su baba ba kina musu add'ua nasan is not easy amma ki daure kinji.

Gyada kai tayi tana share hawayenta,kugunta ya rike pulling her so close to him,kokarin rike hannunsa take yace"... Noo let me please you are my wife now."

Tace"... Uhm nasani aii  amma please kabari  kaga su Angel na cikin daki,yace"... And so what sunsan akwai privacy tsakanin mata da miji."

Fuska ta shagwabe  tace"... Kabari kaina na ciwo kaji,Murmushi yayi yace".. Uhmm shikenan zamu had'u anjuma ai yajuya ya koma.

Kaya suka canza zuwa atamfa fari mai kyau kowa an rufemata fuska da gyalenta aka musu jagora zuwa parlour Abba,Bayan addu'a Baba ya musu nasiha mai ratsa jiki bakajin komai sai tashin kukansu Angel.

Haka suka koma bangarensu Mama ananma haka aka musu nasiha sosai,daga nan aka fara shirin kai amare .

Dakyar aka fiddosu daga d'aki aka sasu a mota d'aya aka  nufi gidansu dasu,Fatima aka fara kaiwa b'angarenta sai Ihsan  sannan Angel.

Bayan y'an kawo amarya sun wuce ne abokan angwaye suka raka Angwayen  bangarensu,bayan  nasiha irinta abokai suka musu sallama su kuma suka rakosu suka kulle gidan kowa ya nufi b'angarensa.

Sorry Fans can't type more am tired.

Share
Vote
Like
[1/11, 8:07 PM] Khadeejaht hydar Novelist

IHSANWhere stories live. Discover now