Part 39

548 17 0
                                    

❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, love,and sorrow)
❤❤💋💋

Written by
Khadeejaht Hydar.

💫FAGEN WRITERS ASSOCIATION💫

❤Gidan zaman lafiya,Aminci,Hadin_kai da yardar juna insha Allah.❤

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

Dedicated to (My Arab mother). Hrt u umeee ❤❤

39

Tashin hankali Wanda ba'asamasa rana.

Haka su mama da baba dasu meesha suka kama hanyar tasha, Sunje amma basu samu wata alama dazata sa su ganeba.

Haka suka koma gida, zuciyoyinsu cike da damuwa.

A b'angaren ihsan kuwa tana sauka ta nemi guri don ta duba address, tasan ina ya kamata ta nufa.

Zanin ta ta kwance don ta duba, amma wayam babu alamar wata takarda.

Hankalin ta yakai k'ololuwar tashi, don batasan inda zata nufa ba.

Tace "Yau ni ihsan na shiga uku, bansan inda zan nufa ba."

Gashi har anyi sallar isha'i, don haka sai ta kama tafiya ba tare da sanin inda zata nufaba.

Tayi tafiya a k'alla na awa biyu, ba tare da sanin abin yi ba.

Can dai ta nemi guri ta zauna, tana kallon mutane k'alilan d'in dake wucewa, saboda dare yayi kowa na haramar komawa matsugunnin sa, hawaye ne ke sakko mata na ganin irin jarabawar da take ciki.

Tashi tayi tacigaba da tafiya, a zuciyar ta tace "Ya ubangiji ka kawomin d'auki da gaggawa."

Wani shago ta hanga, da alamar me shagon ya kulle.

Bench d'in da ta gani ta hau ta zauna,tana tunanin abinyi .

Kamar daga sama ta jiyo ihun mutum, in kunnen ta bai mata karya ba kamar muryar mace ta jiyo,gaban ta ne ya tsinke ya fad'i,tayi saurin sauka  daga saman bench d'in tana dube dube.

Kamar ance kalli can ta hangi wasu maza  biyu,suna k'ok'arin cire ma wata hijab d'in ta, ga kuma wuk'ak'e da adduna a hannun su.

Batasan lokacin da ta saki wani firgitattcen ihu ba,da sauri suka juyo don ganin waye .

Ido hud'u suka yi da d'aya daga cikin su,d'ayan yace "Kamo ta kar ka bari ta tsere."

Tana  jin abinda yace ga kuma d'ayan ya nufo ta gadan gadan yasa ta kwasa da gudu tayi hanyar jejin data gani a kusa da titin.

Binta yayi shima da gudu .

D'ayan kuma cigaba da yunk'urin hallaka yarinyar yake,hannunta ta mik'a ta d'auko wata wuk'a data gani ,shi kuma yana k'ok'arin had'a wata allura,Sara masa wuk'ar tayi a kansa .

Ihu ya saki,kafin yayi yunk'uri har ta tashi ta fita a guje tayi hanyar wani jeji data gani.

Tashi yayi cikin jini ya biyo ta,ganin da tayi ya biyo ta ne yasa ta k'ara saurin gudun ta.

Ihsan kuwa sai da taga tayi masa nisa, sannan ta nemi wani lungu ta shige ba tare da tunanin wani abuba.

Kamar daga sama ta jiyo kukan mutum,da sauri ta juya tana son ta saki ihu, saurin rufe mata baki tayi, tana hawaye tace. "Kar kiyi ihu in suka ji zasu kashe ni dake gaba d'aya."

A tsorace tace, "Suwaye?, ke me ya kawo ki nan?."

"Satoni suka yi sai Allah ya aiko min da taimako, wata ta gansu tayi ihu shine d'ayan yabi yarinyar, ni kuma daga nan na samu na kub'uta."

Kallon ta take cike da fargaba tace, "Ni ce wacce d'ayan ya biyo a sanadiyyar ihun da nayi."

Yarinyar tace "Amma me ya kawo ki wannan gun a daidai wannan lokacin?."

Hawaye ne ya zubo mata nan ta fara bata labarin ta har ta gama.

Tace, "To amma me yasa kika zo cikin gari wa kike nema?."

Kafin ta bata amsa suka jiyo muryar mazajen na cewa wallahi sun gudu amma sai mun kama su, gunki ya sha jini.

Sude suna lab'e a tsorace, sun kasa motsi sai da mutanen suka kwashe a k'alla minti talatin kafin subar gurin.

Suna tafiya ihsan tace mata, "Muyi gaggawar barin nan inba haka ba zasu biyo mu."

Queen ceh !!!
https://free.facebook.com/groups/228916361333651?view=group&ref=opera_speed_dial_freefb&_rdr#groupMen

IHSANWhere stories live. Discover now