Part 85

610 15 0
                                    

❤❤💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic,Love,Sorrow)
💋💋❤❤🌟🌟💫💫

Written By✍
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist.

✍✍✍✍✍✍✍✍
GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION.
✍✍✍✍✍✍✍✍
❄We are bearers of sooo golden a pen
We write assidiously percieven no pain
Sooo magical
Our creative golden pen
Be hold our words
A product of our pen
Savour our words, for it will cause you no pain❄

Dedicated to.
IHSAN FANS.
INA YINKU IRIN SOSAI D'INNAN BAZAN MANTA ALKAHIRINKU DA DUA'INKU BA TNX FANS MUAHHH.

HAUWA'U SAEED GODIYA NAKE ALLAH YABAR K'AUNA NIMA INA GAIDAKE.REALLY APPRECIATE UR EFFORT DEAR.

8⃣5⃣
Bayan bikin gida ya koma tsaf kamar ba'ayi wani taro ba,Su Ihsan sunsha gift daga jama'a hardasu Mama Daddynsu Hisham ya bata sabuwar mota fil,Daddynsu Fahad kuma kayan d'aki ya saiyamata sabon yayi,Daddynsu Deen kuma Makka ya musu alk'awari tare da kasa biyu Wanda su zasu  zab'a in y'an uku sukayi wayo.

Ihsan rasa inda zatasa ranta tayi don d'ad'i tama rasa dawane bak'i  zata musu godiya,Hawayen farinciki da godiya take su Dad sukace tadaina yi musu godiya ai itama y'ar suce kuma anzama d'aya.

Da daddare tana zaune bak'in gado Bayan angama musu wanka,Sanye take da rigar bacci har k'asa green in colour tana kok'arin basu nono yayi sallama ya shigo.

Zip d'in rigar ta maida tare da gaishesa,Murmushi yayi don yagane kunyar basu nono take a gabansa.

Ahmad wanda suke k'ira da (Muneeb)sai Maryam dasuke k'ira da (Muneeba)sai Aisha dasuke cemata (Mubeena).

Muneeb ne ya saka kuka alamar yanason yasha mamma,Kallonshi tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa,Zip d'in gabar rigarta yayi tare da d'aura mata yaron akan cinyarta.

Feeding d'insa tafara saida tagama feeding d'insu sannan tabasu madara ta kwantar dasu,Tana niyyar tashine Deen ya kwantar da kanshi akan cinyarta sannan yayi muryar yara yace".... Nima zansha nono."

Dariya yabata amma saita dak'e tace".... Ni katashi kar wani ya shigo, yace"... Nd so ba matata bace ke."

Bayadda ta'iya haka tabarshi ya fara  lalubarta harya ta kwantar da'ita,kok'arin rabata bud'e zip d'inta yake tayi saurin tashi tasaka kuka don ta tuno da zancen su Mama dasukace  tana yarda dashi zai mata wani ciki ga  y'ay'a har uku kuma ga tuno da zafin haihuwa da tayi."

Kallonta yayi a hankali yana k'ok'arin tab'ata don ya rarrashinta,saurin ja da baya tayi tace".... Karka tab'ani kallonta yake a zuciyarsa yace"... To meyasa kullum insuka keb'e daga ita sai shi sai yana ganin tsoronshi a idanunta."

A hankali ya tashi yabar d'akin ita kuma ta kwanta ,yana fita yaje gunsu Fahad, Fahad yace".... Abban su Muneeba ya akayine?".

Yace".... Uhmm wlhh bansan meyasa ba tunda IHSAN ta haihu batason na tab'ata sai wani tsorona  take,Hishma yace".... Common guy chill Wlh tsoron ka takeji karka sake mata wani cikin u know she  is still young akwai tsoro ai."

Sai a lokacin yagane yace"... Eh gaskiya amma may be our mothers are behind it zasu iya jamata kunne,Fahad yace... Wlh kuwa k'aramin aikinsune kam kawai kanemi hanyar rage zafi da'ita kawai she is your wife u knw how to handle her."

Waya takeyi dasu Meesha tana fad'a musu Abin Alkhairi data samu bayan sun tafi,Meesha tace".... Kawai ki bawa mijinnaki inyace ki ajiye to,IHSAN tace"...yauwa meesha yaushene auranku wai?,tace".... Watan mai zuwa,Allah ya kaimu kigaida su Mama kimusu ya gajiya."

Su Meesha sun had'u Da Samarin sune a auran Deen hargashi yanzu ansaka musu rana,sai lokaci ake jira.

Sallama akayi Mama ce ta shigo tare da Babban faranti a hannunta,ta kalli IHSAN tace"... Tashi kisha ayi wanka ki kwanta la' asar tayi tashi tayi tasha sannna ta ajiye kofin,sbd yanzu su Mama a gidan suke wuni su Angel ma sun dawo gida saboda haihuwa ta kusa.
To Alhamduliilah yau Ihsan zatayi arba'in yara masha Allah sai girma suke saboda Sam basu da rigima ga madarar ta karb'esu,ita kuwa tana samun kulawa agunsu mama ciki da waje sai wani kyau ta k'ara da shek'i.

Abinci akayi aka rabawa jama'a kamar suna,IHSAN da y'ay'an ta sunyi kyau matuka Harda uban gayyar,kowa a gidan masha Allah.

Washe gari Deen yana zaune tare dasu Fahad Mama tak'irasa tace"... Tanason ganinsa yanzu su Fahad nacewa yau zai zama ango yana Murmushi, yana zuwa mama tace"... To yanzu so muke ka d'auki Ihsna ka kaita k'auye tamusu koda kwana biyu ne."

To yace dukda ransa ba hakan yasoba,yana shiga d'akin yaganta tagama had'a kayanta ta shirya shi take jira,harararta yayi tare da d'aukar jakarta yakai bayan boot anan yasanar dasu Fahad yana had'a rai.

Dawowa yayi ya d'auki Muneeb da Muneeba ita kuma  ta d'auki Mubeena suka fito abin sha'awa,d'aukarsu hoto su Fahad suka yi batare da sanin suba.

A gaba ta zauna tare da y'ay'an ta ta kwantar dasu,su Fahad kuma suna baya a haka har suka kai kauyen.

Suna isa sukayi kicibus da Meesha tana shirin fita,Ai da gudu tak'araso gunsu Tana murna da unexpected visit d'insu.

Ciki taje ta sanar aka musu izinin shigowa Deen na rik'e da namijin,Meesha na rik'eda Mubeena,Ita kuma Ihsan na rik'e da Muneeba.

Share.
Comment.

Tnx fans 4 d love.

Royal Blood typing
[2/11, 9:48 PM] Khadeejaht hydar Novelist:

IHSANWhere stories live. Discover now