Part 46/47

560 20 0
                                    

💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, Love,Sorrow)
❤❤💋💋✨✨

Written By
Khadeejaht Hydar.
Young Novelist ✍🏻

💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

❤Gidan zaman lafiya,Aminci,Hadin_kai,da yardar juna insha Allah .❤

Dedicated to : FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION❤ Hrt u All.

           ✨46✨

Suna isa akayi emergency dashi,Doctor's Biyar akansa amma saida suka kwashe tsawon awanni hudu suna Abu daya.

Amma shiru kakeji, cikeda karaya suka fito bayan sun saka masa oxygen a hanci,Babban likitan ne ya nemi ganin su.

Dukansu ne suka shiga suka nemi guri suka zauna,Likitan ya dubi Daddy yace" to Alhaji munyi iya kokarin mu naganin ya tashi amma abin yaci tura."

Don haka ina me baka shawarar fita dashi waje, kana iya zabar kasar da zaka kaishi nanda kwanan✌.

Jiki a sanyaye suka fito suka  nufi dakin dayake kwance,Kowa acikinsu saida ya zubda hawaye saboda yadda suka sameshi kamar babu rai a tare dashi.

Fita sukayi don zuwa gida ,saboda baba yace" gobe za'a fita dashi."

Sunzo shiga mota  sukaga daddyn fahad da daddy'n Hisham .

Gaisawa sukayi sannan daddy'n Hisham yece" Ashe Deen ne babu lafiya? Munje gidanne don mu sanardaku abinda yafaru shine mukatarar da labari wai kuna asibiti."

Baba yace" Haka ne ,Meyafaru kuma ,Dady'n Fahad ne yafada musu duk abinda ya faru."

Angel tace" to Baba yanzu kenan yarinyar tana Mexico tare  da mummy. "

Daddy yace" eh tana can, yau da safe ma munyi waya ,tace" Har ankaita dakin tiyata."

Mama tace" to Alhaji inba damuwa kawai shima akaisa Mexico din ,kaga sai muyi jinyarsu a tare."

Angel tace"  Habibty zan tafi dake,ikram ma tace" nima haka."

Mummy tace" A'a zaman asibiti fa zamuyi,kawai Ku hada kayanku  sati me zuwa Daddy ya kaiku Yamal inyaso in komai ya lafa saikuzo ganin su."

Bahaka suka so ba amma haka suka amince, Baban hisham  ne yakira  Hisham ya fada masa yadda akayi saboda lokacin baya gari.

Daga nan airport sukaje ,sukayi booking flight na safe,bayan angama komai ne suka dawo gida kowa ransa ajagule.

Washe gari da safe motar asibiti takai Deen har airport, inda su mama da hisham duk suna nan,Nan suka musu sallama tare da fatan samun sauki da dace gurun ubangiji.

Hisham ne yadaukesa yakaisa cikin jirgin ,saboda yace" dashi za'aje, to daman anason namiji saboda dagawa da kwantarwa Wanda mama bazata iyaba ita kadai.

Haka suka tsaya har saida jirginnasu ya daga ,sannan suka koma gida Angel na kuka saboda yadda taga yayannata  kamar bashida rai.

Suna isa motar asibitin na jiransu,don haka ba wani bata lokaci akayi asibiti dasu.

Suna isa akayi emergency dashi, zaunawa sukayi a waiting parlour da Addu'ar Allah yasa a dace.

Har magrib likitocin basu fito ba ,haka  sukaje sukayi salla suna masa addu'ar Samun rangwame daga Ubangiji.

Suna komawa cikin asibiti likitocin na fitowa,Babban likitan ne yayima hisham Alamar yazo.

Suna shiga likitan yace" Agaskiya condition dinsa yayi muni," don haka zamu turaku wani branch dinmu Wanda sunfi nan kwarewa,zamu saka mota ta kaiku."

Godiya ya masa sannan ya fito yayima mama bayani,Zuciyar tace ta karaya hawaye suka sakko mata .

Share hawayen tayi,ta daga hannu sama tana yimasa Addu'a.

Hisham  Wanda yana lura da'ita ,amma yaki su hada ido saboda shima zuciyarsa ta karaya sosai yaji kirjinsa ya masa nauyi.

Be ankara ba kawai yaji hawaye na sakko masa ,Share wa yayi jin maganar likitan na sanar masa zuwan motar.

Daukansa yayi  tare  da taimakon likitan suka sashi a mota,likitan ya musu fatan alkhairi sannan ya karbi numbar Hisham  su kuma suka kama hanyar asibiti.

Suna isa aka karbesa,don Doctor Ayub yariga ya sanar musu da zuwansu.

Daga kai nayi ina kallon haduwar asibitin ,komai na asibitin mai tsada ne .

Daga kaine nayi naga sunan asibitin arubuce,Kamar haka.
SPECIALISTS HOSPITAL.

Nace" wow Asibinan yaci sunansa ,Kai Khadeejaht Hydar fans nasan kuma inkungani zaku ga haduwarsa.Fauziyya Muhammad  ma ta yaba da hospity din lol.

Bayan minti ashirin dashiga dashi dakin tiyata ,aka mikowa Hisham wata takarda yasaka hannu  za'a masa aiki a zuciya.

Jiki ba kwari  yasa hannu ,Likitan ya wuce .

To Alhamduliilah Anmata aiki cikin nasara,komai dai_dai.

Su mama na zaune akazo aka wuce da Ihsan ta gabansu,Mama tace" Allah ya baki lafiya baiwar Allah .

Hisham ne ya dago don yaga wacce mama kewa magana,kafin ya kalli inda suke har sun wuce da ita dakin hutawa.



      ✨47✨

Mama ce ta fito don siyoma Ihsan kayan fruit,Amma sede me tana fitowa saitaga kamar hisham.

Karasowa tayi dan ganema idonta gaskiya,tana isowa tayi tozali da Habibty.

Cikeda mamaki tace" Umman Deen!  Dagowa sukayi atare ,cikeda mamaki Umma tace" Hajiya Daman anan kuka sauka?"

Mama tace"Yanzu muka zo nan,Nande tabata labarin komai."

Zama tayi tana jinjina kai ,tace" to Deen kuma abinda ke faruwa dashi kenan to Allah ya bashi lafiya."

Amin suka amsa, Hajiya tace" ina  majinyaciyar taki?mama tace" yanzu aka fito da ita daga dakin tiyata," sanadiyar wani karfe daya shige kafarta, ba'a kula ba sai anan."

Mama tace" to Allah yabata Lafiya,Deen ma yanxu aka shiga dashi dakin tiyata."

Mama tace" bara na siyo kayan fruit,Hisham yace" kawo nasiyi miki."

Ta nuna masa dakin dasuke sannan  ya wuce, su kuma suka shiga dakin.

Maman Fahad tace" Allah Sarki ai wannan itace nagani dazu,ta gabanmu aka wuce da'ita."

Mama tace" uhm baiwar Allah ,daga taimako itama ta hadu data ta kaddarar."

Mummy tace" haka Ubangiji ya tsara mata ,Allah de ya basu lafiya gaba daya Amin."

Hisham ne ya shigo dakin da sallama dai_dai nan ta farka, Amsawa sukayi shi kuma ya karaso ciki ya mikawa mummy ledar.

Kallonsa take cikeda mamaki,meya kawo shi nan? A saninta itada mama ne suka zo, juyawa tayi don kallon mama,gabantane ya fadi ganin mum din Deen.

Kanta duk ya daure,Hisham ma kallonta yake yanason tuna inda ya Santa.

Gabansane ya fadi saboda wannan tayi masa kama da IHSAN,to amma ita meyakawota nan,miye Hadin ta da mummyn Deen?.

Karde itace wacce sukayi accident da Nafeesa harshi da Deen suka sata a jirgi.

Zuciyarta ce tabata shawarar kawai takirashi,Dan taga alamun daga shi har mama  babu Wanda ya ganeta.

Tunaninsane ya tsaya,jin an ambaci YAYA HISHAM !!!

Tanx 4 ur Du'a

Alhamduliilah Am feeling More Better.

For comments::07016167938

My fb group: Khadeejaht Hydar Hausa Novels.

My fb user: Khadeejaht Hydar Deejah

IHSANWhere stories live. Discover now