part 43/44

564 21 0
                                    

💋💋
IHSAN
❤❤💋💋

(Romantic, love,sorrow)
❤❤💋💋

Written By:
Khadeejaht Hydar.

💫  FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

❤Gidan zaman lafiya,Aminci,hadin kai,da yardar juna insha Allah ❤

Dedicated to ✨My Buddy( Bro Muserh) Allah yakara daukaka✨

              ✨43/44✨
Suna isa sukaje dakin mummy suka dauka passport dinta,sannna suka hada kayan bukata don kaiwa asibiti.

Sun fito harabar gidan kenan kiran fahad ya shigo wayar hisham,Dauka yayi suka gaisa yace" na sauka tun dazu shine nace bara nakira nafadamuku."

Hisham yace" to madalla Ga deeni;ya mikamasa wayar,deeni ne yakarba wayar suka gaisa sannnan fahad yake tambayarsa sunje gidansu ne yanason yin waya da nafeesa ;amma layinta baya zuwa ko lafiya.?

Deen yace" lafiya kalau ai munje gidan dazu tana bacci, Anana hankalinsa ya kwanta yace" to kunje gun ihsan ne.?

Yace" A'a sai gobe insha Allah zamuje."

To Allah yakaimu inji Fahad ,sannna ya yanke kiran suka fita daga gidan sukayi asibiti.

Suna isa suka tadda mama da baba a zaune ,basu kayan sukayi sannan deen yace" baba ya za'ayi maganar passport din ita Mara lafiyar."

Baba ya nisa sannan yace" haka za'a mata,Ku hanzarta kuyi komai yau gobe saisu wuce."

Toh suka amsa sannna suka shiga dakin datake,kwance take idonta rufe amma ba bacci takeba.

Sautin muryar shi taji kamar a mafarki,Amma yadda idonta ya kumbura yasa takasa dagowa ta kalleshi bare tayi magana.

Hawayene yafara sakkowa a idanunta,Wanda duk motsin datake akan idon deen ne.

Kallonta yake har fahad yagama daukarta passport din ,sunzo gurun fitane, sai alokacin deen ya lura da hawayen datake.

Mamaki yake aransa aina yasan ta,kuma meyasata kuka?

Ita kuwa tanajin fitarsu,ta sauke ajiyar zuciya,Dan tasan tabbbas Inda deen dintane daya mata magana,to amma meyasa take hawaye? Ko Dan ta tuno dashine sanadiyar mai murya irintashi.

Hmm ihsan baki kalli face dinki a madubi bane,dakema zakice bakebace.

Suna fita deen yace " Fahad kamar nasan fuskar yarinyarnana ,Amma Sam na rasa inda nasan ta.

Fahad yace" daman haka Allah yake ikonsa,yayi mutane  masu kama da juna.

Deen yace" hakane please gobe zaka rakani gun Ihsan ."

To Allah yakaimu,Amin ya amsa ,sannan suka nufi airport.

Sai yamma suka dawo asibiti,suka bawa su mama komai na Visa din sannnan suka koma gida.

Washe gari da safe,da misalin karfe goma su mama harsun gama shirin tafiya,Nafeesa sai kuka take tana rikeda hannun ihsan.

Da kyar hisham ya dagota yana bata baki,yace" ki mata addu'ar samun lafiya kidaina mata kuka kinji.

Gyada kai tayi tace" to, ihsan ce  ta riko hannun nafeesa tana murmushi bakinta na mosti Idonta a rufe.

Da sauri nafeesa ta tsugunna ta daidaita kunnenta zuwa bakin ihsan, Ahankali ihsan tace" in Allah ya hadaki da Nafeesa ,da Yaya deen kice" musu su yafemin,kuma kifada musu ina hannu mai kyau zandawo garesu inda rai da rabo."

Hawaye take hakama IHSAN ,ta rike hannunta tace" kidaina kira mutuwa ,insha Allah zaki tashi ki taka da kafafunki.

Deen ne ya rabata da ihsan,sanan mama ta dauketa takaita cikin mota.

Su duka suka shiga motar don yi ma su mama rakiya,suna isa babu bata lokaci aka fara kiran passengers.

Su deen ne suka taya mama kaita cikin jirgin,sannan suka musu sallama suka koma.

Suna tsaye agun har jirginsu ya daga,sannna su kuma suka shige cikin mota suka koma gida suna musu fatan alkhairi..

Toh Nima ina muki fatan alkahiri fanss

Kuyi hakuri. Wlhh banajin dadi, har

IHSANWhere stories live. Discover now