Escape

1.8K 193 22
                                    

MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 1️⃣9️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu
https://my.w.tt/WX0KhzpLvcb

Sake leka ramin nayi wasu irin tears suka zubo min, tare da juyawa na kalli cikin gidan, zuciyata ta kasu gida biyu, na sauka nasan idan ban Karerayi ba, tabbas zan mutu. Idan na koma cikin gidan, kuma zasu lalata min rayuwa.
"Kee!" Aka daka min tsawa ta bayana, a razane na juya.
"Karki yarda ki gudu! Dan wallahi zaki gamu da b'acin rai na,"

Had'iye kukan tayi tare da girgiza mishi kai tace.
"Ai na gama muku aikin ku, dama abinda kuka shirya min kenan, Insha Allah ku fata shirin ganin balbalin bala'i, Insha Allah Sir Mahir ba zai tab'a barin ku ba."
"Ke ki tsaya wallahi kika fado mutuwa zaki yi dan."

Ganin yana ƙoƙarin daukar karfe ta kuma razana tare da zaro idanu waje, ta rude ga iska da jirin da yake kwasarta.

Yadda ya dauki karfen ya wullo mata, ba tare da fahimtar inda take ba, tayi maza taja da baya,.sai ji tayi ta tafi luuuuuu..
Wani irin gigitacciyar kara tayi iya karfin ta, "ƙasssssss" taji kashin kafad'arta yayi kara, tare da buguwa da kanta a jikin wani kutitture, tashi tayi cikin ambaton Allah.

Sannan ta kalli inda ta diro, a hankali taja tinga ta tsaya, sannan ta kalle shi yana me ciwon lips d'inshi, yana cewa.
"Sai na kashe ki!"
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Zaka dai kashe wacce zaka kashe Manager, amma na gama kwacewa a hannunku, ka jira abinda zan aikata muku." Jin motsi tayi a gefenta, kamar ance ta juya, wani katon phyton ta gani idanun shi jajjur.

Dariya Manager yayi sannan yace mata.
"Allah ya jikanki. Mun huta!"
A hankali take ja da baya, tare da jin wani irin tsoro ya kamata, sam babu jini a jikinta, tsabar tsoron bala'i, shi kam gyara kwanciyar shi yayi, domin yana barcin shine a jikin kutitturen da ta fado a kai, ta dan taka shine ya farka. Gyara konciyar shi yayi, bai san da ita ma ba, ai tana ganin haka da ta juya da mugun gudu, kawai ta nausa dajin, jin motsinta ya kuma buɗe ido, tare da d'aga kan shi, ya mai da abinshi, ihu Manager ya kwala, sannan ya koma cikin gidan yana faɗin.
"Sai na kashe ka, tunda kabarta ta tsira."

.....
Yana bakin dajin, yaji ihunta. Amma bai san ta inda zai fara shiga ba, kallon inda yaji ihunta yayi, kawai yayi shahaddar kuda, ya faɗa dajin a guje. Yake gudu tare da kiran sunanta A'isha Omar Jimeta!
Gudu sosai yayi tare da rasa ta inda zai kutsa, banda yana d'aga karfe, tare da wasu abubuwan da bai isa gudun nan ba, sannan takalmin kafarshi ma irin me kasar karfen nan ne, shi yasa yake shiga dajin babu wani abu a ranshi.
Yayi gudu sosai, amma bai same ta ba, wani abin da zai baka mamaki duk inda zai tafi sai ya bar alama da zai saka shi ba zai manta gurin ba, amma tabbas ya gama gajiya da wannan niman da yake mata, daman soja ne.
Karewa ko ina kallo yayi, tun karfe biyu na rana yake cikin dajin ga yamma tayi lumshe idanun shi yayi, domin lokacin sallah yana shirin wuce shi, haka ya fito cike da bakin ciki da damuwa, bakin titin ya fito. Ya tsaya tare da buga motar, yana jin wani irin kunci a ranshi.

Karar harbi ya kuma ji, bai san lokacin da ya kuma juyawa dajin da gudu tare da kwal mata kira.
.....
Gudu sosai tayi tare da jingina, da jikin wata bishiya, tana hakki bayan kamar awa taji ana kiran ta, jin muryan tayi kusan biyu, ya sata kara rikicewa.

Jin inda Muryan kusan biyu, ya sata kuma nausawa dajin dajin, kamar zata yi hauka..
A can kuwa a fusace Manager ya kira Aysar Haladu, take aka bazama niman Noorh, dake basira ta kwace musu zuwa gurin macijin nan suka yi zasu kashe shi, harbin shi da suka yi ne Yasaka taji karar, shi kuwa da aka harbe shi gyara kwanciyar shi yayi, tare da bude idanun shi.

Lumshewa yayi sannan ya kuma buɗewa yaga abinda yake hannun ya kalla sannan ya girgiza. Kafin ya mike sosai akan su, lokacin da ya fasa kan shi sai gashi kan shi yayi fadi har kai uku ne, wani irin huci yayi tare da fasa kai..

Cikin tsoro suka juya da mugun gudu, suna niman hanyar niman ceton rayuwar su. Kallon jikin shi yayi inda yake fidda wani baƙin jini, ya tasa ihu a dajin, sai da suka kuma haukacewa, ai kuwa ya fusata ya shiga binsu daya baya daya yana sarar su, sauran kan sun gudu dakyar Manager ya sha duk da katin tumbin shi bai hana shi sukunin gudu ba.

MAH~NOOR🌹Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora