hateatfirstsight

1.7K 171 26
                                    

https://my.w.tt/LFTaVMaeacb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 1️⃣3️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

🙄🤔 _Wai ya naga kuna harara ta ne Aunty Mami, Jikar kulu Ni meye nawa ne, Yar gatan mijinta, Mommy Sayeed! Zahrah Adda Ramla, Maman Abdul, Faization. jaderah, Halima, matan quarts grp, Ruwa biyu comments section, Maman Batul, Maman Nana, Sister Nusaiba. My Wattpad fans, kuna manne a button din heart dina, ina yin ku sosai, Wayyo 😲 My Telegram fans ga naku kuma 😜❤️ Allah yabar kauna! Idan baku takawa Noorh birki ba, zata rasa kafaffuna, domin Major ha shirya tsaf dan suburbudar duk me rena mishi hankali!_
BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#hateatfirstsight

Cire rigar saman yayi tare da nad'e hannun a kirji, tare da cire daya hannun ya kalli Nazzir, wannan y sake wani irin murmushi.

Takowa yayi gabanta, sannan ya zuba hannun shi a cikin aljuhun wandon shi, tare da juyawa cikin isa da girman kai, yana kallon ta, tare da sake murmushin mugunta. Fakonta yake ya cire nikkab din, itama da ke ta ankara da nufin shi, kaf kaf take da nikkab ɗinta, tana kuma kallon motsin shi.

Cikin wani irin zafin nama, ya kai wa nikkab din cakfa tare da riko hijab din ta, ya sab'a riko nikkab din, ture shi tayi zata fita, ya fisgota tare da wurgata tsakiyar Office din, ya zuba mata ido, tare da balle botirin hannun shi, ya kalli Nazzir tare da daka mishi tsawa.
"Dauko min A4 din!"
Ya kuma takowa gabanta, tare da zuba mata ido, dukawa yayi tare da jan dogon hancin shi.
"Zaki kwafe!"
Cikin tsiwa da rashin tsoro tace mishi.
"Idan naki fa? Zaka saka a b'atar dani kamar yadda kuke sawa ana yiwa mutane."

Cikin fusata, ya kai hannun shi wuyar shi tare da jan iskar bakin ciki, tare da bude idanun shi, ya sauke akanta.
Hannun shi ya kai keyartar da, daidai shigowar Nazzir, ya ajiye A4, ya janyo ta ya wurgata gaban takardun sannnan ya koma table din shi ya dauko takardun ya zuba a fuskarta, sannan ya juya bayan shi tare da yin wani motsa hannun shi, yace.
"Zaka iya bamu guri!"
Ya faɗa haka, fita Nazzir yayi tare da cewa.
"Please Lion!"
"Ka karo wani A4 din!"
Haka ya kuma karawa fahimtar da yayi matukar ya roke shi, kamar yaja mata rashin mutunci ne ya sashi fita, tana zaune a gurin bata d'ago domin tayi magana ba,asalima ma itama wani karsashin rashin mutunci take ji, dan ta rantse a ranta ko gawarta za'a fitar ba zatayi rubutu ba. Ai ita ba baiwar shi bace.

Juyawa yayi ya cigaba da aikin shi bai kuma d'ago kai ya dube ta ba, asalima Mantawa yayi da ita a cikin office din, wani silent Office din ya bada, baka jin kome sai karar Ac. Babu wani alamar motsin rai a cikin gurin.

---
"Me yasa Aeesha Omar take da taurin kai, gashi can mahaukacin can ya sakata aikin da ba zata iya ba.". Tsaki yaja,

Haka yayi ta yawo a Office din shi, shi kuwa ya damu da ita ne, kamar zai zubda kwalla, domin yasan halin mutumin tunda bai kore ta ba, tabbas haka zai sanya ta.
... Awa daya ta wuce, biyu yazo ya kuma wuccewa, d'ago kai yayi daidai lokacin da agogon Office din ya buga, ganin yadda ta manta da abinda ya saka ta, tana zaune ta daura daya akan daya, irin ga gidan Ubanta. Ranshi ne ya b'aci. Bai tab'a gamo da mutum irinta ba, tasowa yayi gabanta, tare da kurawa hannunta ido, fisge wayar yayi tare da buga shi da ƙasa. Ya nuna mata aikin da ya sakata, d'ago kai tayi tare da kallon wayarta a kasar ofishin sa.

Da sauri ta nufi gurin laptop din shi, saka mata doguwar ƙafarsa yayi tare da take kafarta. Ya durkusa a gaban ta.
"Zaki yi ko sai na baki mamaki! Allah ya bani damar gyarawa irinki sittings."
Ya fadi haka tare da zare tie din shi, ya wurga saman table din shi, da wani mugun sauri ta kalle shi tare da rufe fuskar ta da hannunta biyu. Yana ɓalle rigar shi ya fara.
"Zanyi!"

MAH~NOOR🌹حيث تعيش القصص. اكتشف الآن