Personal information

1.8K 173 11
                                    

https://my.w.tt/3Nb7WDqOPbb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣7️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

Kuyi hakuri! Abubuwan ne suka min yawa, amma Insha Allah zaku Cigaba da ganin shi koda ba kullum ba! Insha Allah zan kokarta 🙏🏼😘😍
~#PI~
"Deem baki tunanin ya biyo ki, kin san ba hakuri ne dashi ba, karshe yazo ya haɗa dani, dan na fahimci ya tsane ni." Inji Zoolfa,

      "Ina ruwana, shi ya sani, ayi rayuwa babu wanda zai maka gwaninta, na tsani rashin mutunci. Wallahi na tausayawa matar da zata zauna dashi dan nasan a duniya babu wacce take mishi gwanin ta, sai Ummi da Jaddih, sai ko Alishbah. Dasu Hadiya da Suhaila. Amma ni kullum sai yace ban iya ba.

Ke kwalliya idan nayi sai ya harare ni, wai na cika hauka. Ubangiji ya sa ya hadu da wacce ta fini hauka ta mishi rashin mutunci yadda sai ya san cewa kowa hakuri yake da rashin adalcin shi."
         "Aikuwa nayi imani da Allah, yan matan da yayi breaking heart dinsu sai sunyi farin ciki, mutum sam bai san ana mishi adalci ba, wai da Jaddih ta mishi magana yazo ya nemi aurena cewa yayi wai bani da kunya.
        Kiji fa, sai kace a kaina aka fara rashin kunya kuma ban tab'a mishi kome ba."

     "Ba dai Uban yan tsari ba, muna nan dake sai ya dama bilayin shi sannan ya hadu da wata kucaka..yayi fell in love da ita."
   Haka suka gama kare mishi tanadi, sannan suka shiga hiran samaruka su.
     •••
Cikin nutsuwa yake saukowa daga jirgin, iska na kad'a rigar jikin shi, sanye yake da riga da wando na Puma, rigar me hula ce.
    Kayan jikinshi baki daya Black ne, hatta takalmin shi puma ce, daga can nisa ya hango autar su, tana d'aga Mishi hannu. a cikin wani irin taku me tattare da jarumta, yake tafiya yana isa gurinta, ya bude mata hannun. Da gudu ta isa tare da fadawa jikin shi tana faɗin.
"Barka da hanya Ya Mahir!"
Peck ya mata a goshi sannan yace mata.
"Queen Shbah, ya school!"
"Lafiya lau!"
Ya fada tare da gyada mishi kai, a hankali suka isa motar su, bayan driven ya tawo da kayan shi.  Sai zuba mishi surutu take, yana lumshe idanunshi, tare da shafa kanta.
  Har suka isa gida, tunda ya fito masu aikin gidan suka ganshi, kowa ya nutsu, sun san cewa kana mishi karamin kuskure kora ne.
    Da sallama ya shiga falon gidan.
"Barka da zuwa, miskili kafi mahaukaciya ban haushi."
Murmushi yayi sannan ya isa gurin Jaddih ya zauna tare da daura kanshi a kafad'arta.
"Ina kewarki." Ya faɗa ƙasar makoshi, yadda ita daya ce ta jiyo muryan shi,
    "Magulmaci karya kake, ka fadi gaskiya dai, ya dace kayi aure dai wallahi daga kai har wancan d'an uwan naka, ku nimo mata. Ga yan mata a gari idan ma nan basu muku ba,.ku tafi can algeria akwai yaran mata a cikin dangin mu gaba da baya,.zaku sa.."
      "Hmm!"
"Hmm, din gidan ku. Kai gaya min Aljana ce ta aure ka."
Lumshe idanun shi yayi tare da taryo abubuwan da suka gabata a rayuwar shi, a hankali ya saka hannu a cikin aljuhun wandon shi ya ciro wata sarkan azurfa. Irinta kafa.
    Sake shafa sarkan yayi yana kuma sake motsawa, ba zai iya cewa akwai dalilin mallakar wanan sarkan ba, amma kuma yana da Tabbacin mallaki ne. Na wata, a kala sarkan tafi sama da shekaru goma sha biyu a hannun shi.

           "Allah Alhaji ka fita idanu na, matukar baka yi wani abu ba, nan da karshen shekara zan muku auren dole." Mikewa yayi tare da haurawa sama, ya barta a gurin, bayan shi tabi da harara, tare da musu addu'a Allah ya kawo musu mata na gari.
      Tunda daga bakin kofar dakin shi, yake hango alamun datti. Idanun shi suka nuna mishi, har ya bude dakin cikin takaici yake kallon kura a saman Center table din shi, cike da mugun kyam-kyame ya juya zai bar d'akin. Yaga Ummi tana tawowa.
      "Baba ka dawo lafiya." Yake yayi sannan yace mata.
"Alhamdulillahi Ummi. Na same ku lafiya ya aiki."
Kallon shi tayi na wasu lokuta kafin ta share, duk da tasan shi ba ma'abocin tsawaita magana bane, but.
"Ina zaka kuma, ka shiga ka huta mana."
Cikin gajiya da damuwa, yace.
"Waye aka bawa gyaran dakin?"
Lek'awa tayi ta dai iya hango Center table da dan kura amma shima daga nesa zaka fahimci haka.
           "Haba Babana, kuran nan ba mannewa zai yi a jikinka ba,ka shiga kayi."
"Hmm! Bari naje Apartment dina kawai."
Ya gwammace da ya shiga, cikin wannan ƙurar gwara ya koma gidan shi wanda kullum na duniya, sai an gyara gidan har bedrooms din gidan. Wani yaron shi haroon.
        Yaron bayarabe ne, kusan Mahir shi ya kub'utar dashi daga shaye shaye, ya kawo shi gidan, yana bq. Duk wani nauyin shi Mahir ya dauka. Shi kuma sai ya zabi ya kula da gidan Mahir din.
             A gaggauce ya bar inda Ummi take, tana jin saukar shi, bata dakatar da shi ba, domin ko tayi haka ba zai saka ya kulata ba.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now