hypocrisy

1.8K 161 24
                                    

https://my.w.tt/gzD1s747pcb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣7️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#hypocrisy

Bai fasa alkawarin shi da da ya dauka ba , dan ta na 'n kawai zai rama abinda tayi Mishi.

Yana zaune a Office din shi, yana sauraron hirar da ake da ita, wanda yake cike da zallar yarantaka, uwa uba rashin hankalin da take sakewa ana wasa da rayuwarta, kalle shegen bakin rashin kunyar yayi yaga yadda take magana tana juya shi, dauke kai yayi zai kashe tv yaji ta bada amsar da ya sashi mik'ewa. Domin kuwa an tambaye ta.
"Shin haka zaki Cigaba da kallon Mr Mahir yana hana ki aikin ki zuwa aikinki?"

Cikin shashantarwa tace.
"Ba zai hana Ni aiki na ba, amma kuma na san shima na zame Mishi kalubale ta kowacce fuska, domin dani Nasan dani yake kwana dani yake tashi zai tab'a dogon lokaci yana nazarin meye ya kawo haƙa! Amma kuma ba zai tab'a sanin amsar ba.

Sabida yadda yake cutar da Alummommi masu yawan gaske, ya sani,. Sabida shi mutane da yawa sun mutu, tare da rasa matasa babu iyaka, dan haka na shirya domin na kai shi kasa, Insha Allah next shirina akan shi ba zai mishi kyau ba"

Kura mata ido yayi cikin nutsuwa sannan yace.
"Duk abinda zan mata bai kai wanda tayi min ba, amma bari naga ta ina zata bullo min."

Tabbas rayuwar ta shiga rayuwar shi, yadda baya tsammanin. Ta shige mishi hanci fiyye da tunanin shi, a duniya Noorh ce kawai ta iya tsayawa ta gaya mishi cutarta, kuma bai dauki mata ki ba. Mikewa yayi zai fita suka haɗu da Tasleem wacce take tsaye tana leken shi.

Dauke kai yayi kamar bai ganta ba, har ya isa bakin kofar ya tsaya cak juyawa yayi tare da kallon ta. Takowa yayi gabanta, sanan yace mata.
"Ke yar uwarta ce ko?"
Jikinta na rawa tace.
"Eh sir!"
"Hmm! Zan baki cantract, me kike so?" Unexpected ta d'ago kanta da mugun sauri, tace mishi.
"Babu sir, iya haka ma Alfarma kayi min." Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ok! Ki san yadda zata ki da ita, kawai ki b'ata mata suna"
"Sir!" Ta faɗa a razane,
"Ba zaki iya bane?"
Ya tambaye ta cikin tsawa.
"But!"
Dakatar da ita yayi tare da cewa.
"Bar shi kawai!"
"Sir zanyi wallahi!"
"Karki soma, ki bar shi zan dauki mataki da hannuna."
Tafiya yayi cikin nutsuwa, abin shi zai dauki matakin da kan shi, dan haka yayi gaggawar dakatar da Tasleem, sannan yayi tafiyar shi.
--- karfe biyar na yamma, ta fito zata koma gida, Aysar Haladu ta gani, yayi fakin din motar shi a gabanta, sauke glass din motar yayi tare da sunkuyar da kanshi yace mata.
"Jaruma!"
Murmushi tayi sannan ta kalle shi, tace.
"Barka dai, yallabai"
"Shigo Mu shiga daga ciki."
"A'a sir zan koma gida da wuri ne!"
"Toh zo na ajiye ki."
Babu yadda ta iya amma da ba zata shiga ba, haka ta shiga motar cikin sanyin jiki, ta zauna ya shiga janta da hira, suna tafiya kallonta yayi yaga tana kallon agogon hannun ta.

"Karki damu zamu isa gidan akan lokaci but me zai hana mu dan tsaya na miki take away." Karamin murmushi tayi sannan tace Mishi.
"Nagode sir!"
"Ko kina tsoro na ne?"ya tambaye ta, tare da kashe mata ido,
Murmushi tayi sannan tace mishi.
"Da ina tsoron ka da ba zan shiga motarka ba, kawai ina Son na isa gidan akan lokaci ne." Ta bashi amsa, murmushi yayi tare da parking a wani gurin sayar da kayan ciye ciye, kallonta yayi sannan yace mata.
"Zo muje mu zab'i abinda kike so!"
"Sir nagode zaka iya kawo min kome nagode!"
"Taso muje," ya gaya mata, a hankali tafito kamar ance ta d'aga idanunta ya sauka a motar Mahir, gabanta ne ya fad'i. Dan duk sai taji babu dad'i, bata son magana yau din nan, a hankali take d'aga kafarta, cikin nutsuwa har suka shiga cikin gurin kayan abincin, suna zab'a kawai aka kira Aysar Haladu, ya ce mata tana zuwa.
Ya fita, can sai aka gama zab'ar musu abinda zasu saya, ya tafi. Juyawa tayi ta ciki taga babu motar shi, gabanta ne ya fad'i, buɗe bag dinta tayi tare da ciro kudin zata biya kawai taji ana mata dariya a gurin, bata damu ba, ta dauka just funny suke, tana amsa ta juya, Mahir na zaune abin shi.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now