Contract Marriage

2K 205 33
                                    

https://my.w.tt/GmD0CxtiNcb

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 2️⃣8️⃣
     MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Kallon shi tayi jikinta yana rawa, ta juyo gaban shi.
"Zan duk abinda kace don Allah karka kore ni!"
Wani kallon banza yayi mata, tare da dauke kan shi, ganin yadda take kuka sai Yaji haushin abinda yake mata, but halin Noorh da a zamanin  fir'una tazo tabbas. Itama sai Annabi Musa yasha fama.

                 Dauke kai yayi cikin mugun miskilanci ya cigaba da zarya a falon hannun shi goye a bayan shi, kamar bai san da ita ba, sannan ya d'ago kan shi yana faɗin.
"Zan baki zab'i daga nan zuwa gobe kawai"
Cikin rawan jiki ta karkace kanta tana me cewa.
"Duk abinda kasani zanyi."

Cikin wani irin jan aji, yake kallon smart watch din shi, tare da cewa.
"Na manta sharadin jeki idan na tuna zan gaya miki, amma ki kwana da shirin zaki bar gidan nan gobe."

     Kallon shi tayi bakin ta a sake tana share kwalla, cikin damuwa da tsoron karta mishi magana ya bayyana mata, cewa ya fasa yasata jan bakinta tai shiru, shi kuma haka bai mishi dad'i ba, yaso yaga ta ji haushi, amma sai bai ga haka akan face ɗinta ba, sai ma damuwa da tashin hankali.
           Haka ya bari yazo wucewa, ya kai hannun shi ya daki bom-bom ɗinta, cikin masifa ta juya, ta shiga zazzaga mishi tijara, dariya ne yaso kwace mishi ya kura mata ido, kafin yace mata.
"Ni kike gayawa magana? Daga an d'an make ki sai ki buɗe baki zaki min rashin mutunci, ke ni Ban da zuciyar musulunci, me zanyi da sauran gardawa,.da suka gama lalatawa.
          Toh zoki fita min a gida, yau zaki bar gidan nan ba gobe ba."
"Amma, dai kasan abinda kake haramun ne, idan ranka ya b'aci kayi hakuri ba zan kuma ba. Amma don Allah ko bani ba, ka taya matan da basa tare da ahalin su, yana min ciwo idan ka tab'a jikina sai naga dan iyayena basa raye ne."

      Duk sai yaji babu dad'i, domin yadda ya fahimce ta, duk abinda za ayi da ita, matukar ba za a tab'a kimarta ba, toh babu abinda zai dame ta, amma matukar aka tab'a kimarta duk sai ta rikice tayi ta fada.
Sab'anin wasu yan matan da kana tab'a su magana ya kare, sai dai ma su nuna maka sun fika zakewa.

               Mikewa yayi, ya bar gidan ma baki daya, haka ta wuni cikin damuwa da tararadin abinda tace mishi, kar ya kuma tambaye ta abinda ba zata iya bashi ba, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun,ta fadi haka yafi sau goma.

      •••
Tsare Mishi hanya Nazzir yayi, cikin isa da iko, bai ce kome ba, yaja motar da baya, da gudu sannan yazo a guje ya daki motar Nazzir sai da ya bugi wata bishiya da aka dasata domin kwalliyar fasalin gidan. Sannan ya wuce abinshi yana gargad'in shi da hannu ya shiga hankalin shi.
        Dan haka bayan Ya wuce, ya nufi gidan Ummi ya samu suna hada kaya.
"Ya Mah ba zaka umrah. toh ka shirya Aunty n..."
"Shii! Bana son magana, idan wani yaji fa?" Wuce ta yayi ya haura dakin shi ya kwanta, yana jin sam bai mata adalci ba, sam babu adalci a wannan al'amarin yaso kan shi da yawa, taya za ayi ya sako batu me girma haka?

   Anya Dr da Brst basu kai shi sun baro ba kuwa? Toh me zai ce mata? Shi baya son abinda zai kai ga cutarwa ne,.idan al'amarin ya fito, toh tabbas zai iya janyo mishi rikici a kamfanonin shi.
      
    Amma idan ya tuna da, yadda haka fitowar ta zai zama me musu bakandamiya sai yaji nutsuwa a ranshi, sabida yana da shiri na musamman akan Bayyanar da Noorh, shi yasa yake niman hadin kanta, toh ya fahimci. A yadda ya gama tsorata ta, zata iya bashi hadin kai a ruwan sanyi. Dan haka yana gidan har dare sannan zai fita zuwa masalaci, ya hadu da Baban Nazzir, nan ya gaishe shi sannan ya wuce, bayan sun fito sallah isha ne, suke tattaunawa.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now