Chased Game

1.7K 190 34
                                    

https://my.w.tt/YXHFir6fUcb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣3️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Sun dauka zata biye musu ne, sai suka ga bata da lokacin su ma, matsalarta daya Mahir ya taimaka ya dauketa daga cikin su, dan ma cikin yayiwa Ummi cikas domin tsakanin ta da Allah take bawa Noorh kulawa, kuma ta fahimci irin rabon nan ne da matukar ba a Barni na zo ta hanyar da ya dace ba, Tabbas zan iya zuwa ta karfin tsiya kusan akwai irin wannan cikin.

Idan bai zo ta hanyar halal ba, toh ko yayi kisa ko kuma yazo ta hanyar banza, dan haka Hajiya take girmama al'amarin cikin jikin Noorh, koda Baban Nazzir yazo da maganar Zoolfah, dakatar dashi Hajiya tayi tace.
"Yanzun muna son mu lallaba shi ne, akan wancan auren da aka yi a cikin jirgin kasa, yaki nutsuwa domin yace ba zai rike mace sama da daya ba, shi mijin mace daya ce."

"Amma Hajiya haka zai cigaba da juya ku, kamar shine sama da kowa? Haba ai ya kamata a tsawarta mishi." Jin sautin takalma ya sashi d'ago kanshi Mahir da Noorh ne hannun su sarke da juna, fuskarta fayau. Dan yanzun take jin laulayin sosai.

            Sai da suka sauko kasa, ta gaida Baban Nazzir, sannan ta koma kusa da Hajiya ta kwanta, tare da jin kewar Mahaifiyarta, dan ji take kamar tana tare da wani na jikinta, shafa kanta tayi tare da saka mata albarka. Jin dumin kwalla yasa ta zubawa Mahir ido, mara kirki ya kame a kujeran yana wasa da puzzle box mission.

      Kallon Baban Nazzir yayi tare da cewa.
"Kawu! Nikam kwana biyu bana ganin Nazzir, ko ya bar kasar nan ne?"
"Yana nan akwai wani gasar da ya shiga ne na chased"
"Ikon Allah yaushe aka fara wasan ban sani ba?"

    "Tun ranar da aka tare mu na sashi shiga gasar."
"Toh kuwa za a buga wani domin ina son farar sarauniyar!"

"Kasan kuwa ba zai dauki bakar sarauniya ba!"
"Zai dauka mata tunda na tsare bayan shi a ina ke buga wasar!"
"A Nicol hotel ne!"
"Har abuja?"
"Ko baka shirya zuwa bane?"
"Tsaf na shirya cikin fahimtar haka!"
"Toh ita wannan wasar ta sake haja ce!"
"Tuni na fahimci haka!"

A wasa a wasa, sukai ta gayawa juna magana, tare da tilasta juna saka abubuwan da suke bukata a game din chased, shi kuwa Mahir yana sane da hakan, domin ta fahimci kawun shi burin su, ya saka Noorh a gasar, shi kuma Mahir Burin shi, a saka Zoolfa a cikin wasar.

    Cikin tsananin zafin rai Baban Nazzir ya tusa Zoolfa, inda yake cewa.
"Na saka kadara Mafi daraja a cikin ahalin gidan mu, kai kuma yarona me ka saka a cikin naka kadara?"
"Kadarar da zan saka biyu ce, akwai abinda nafi so. Akwai kafatan dukiyar Hamoud Boualem,.da  kuma jiragen ruwa tare da masu Safara. Sai numfashin Mahir Hamoud Boualem na saka."

"Maka sane zaka kai labari."inji Baban Nazzir.
"Me zai hana na kai labari an haife ni domin nasara ce!"
."Yarona inda ba kasa?"
"Kawuna nan ake gardaman kokuwa. Mu hadu a garin Abuja."
Daga haka kowa ya mike, dan Mahir zama da Noorh ya koya mishi iya tinzira mutum.

       Domin yaga fusata a kwayar idanun Kawun shi, kuma burin shine ya fusata dan banza, dan haka suka fita. Asibiti ya kaita aka duba lafiyar cikin jikinta, duk da tana nan da halinta bai hana shi kaita gidan shi da yake Ekoyi ba, ya gurgureta son ranshi . Itama yar banza bata hana shi domin tana son haka, musamman cikin ya saka mata son kamshin turaren shi.

     Daga nan yana tab'ata toh zata mika wuya sai ta nutsu ne zata shiga mishi rashin mutunci da borin karya.

   Haka ba karamin dad'i yake mishi ba, kuma ya lallabata da dadin bakin zai kaita Algeria. Dake sokuwa ce, lokaci guda take manta kome.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now