Silent

1.9K 176 26
                                    

MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣5️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

Idanun ta ne ya kuma komawa kan bindin shi, tana kallon shi kamar taga dodo, ta leka sai kuma ta rufe fuskar ta, tana kuma lek'awa zata rufe fuskar ta.
Wandon ya dauka ya saka tare da xora jallabiyar shi ya bar mata d'akin, dan ya fahimci haukata shi take son yi.

Ga yadda yake ganinta naked babu abinda zai hana shi bai farmata ba, kitchen ya nufa, har zai fara bada oda abinda za a girka mishi dan yasan Haroon zai iya zuwa da wuri, sai ya koma dan yasan ba karamin aikinta bane fitowa tsirara. Allah sarki tana can ta gaji har ta fara barci, rufeta yayi tare da gyara mata kwanciya. Sannan ya wuce daya dakin ya kwanta.
Washi gari da safe, ya rigata tashi, har ya gama zai fita sai ya tuna babu kaya a jikinta, dan haka ya dawo ya saka mata kaya, tana barci sannan ya tashe ta tayi wanka da karyawa kafin ta sata tayi sallah. Tana idarwa ta fara barci. Sannan ya fita ya barta.
Karfe sha biyu zata sha na rana, tun sha biyu saura ya dawo, ya bata sannan ya koma gurin aikin shi, haka ya bashi damar kulawa da ita, kuma sosai yake hakuri da kiriniyarta, domin wallahi bata jin magana.

Ga barna kamar bera, sau uku tana fasa mishi Center table, na farko wai ta hau zata zauna, tana cikin zama kawai taga ya canza channel din tv dake tana kallon Dora in Magic Land ne, kawai ta fasa ihu tare da tashi tsaye ta daka tsalle badan yana gurin ba da sai ta raunane, ya dauke ta, aikuwa ta shiga ya kushinsa tare da kai mishi duka, abin ya masifar b'ata mishi rai, dan haka yana sauke ta, ya dalla mata mari. Sai da ta dauke wuta a tsorace ta kalle shi.
"Uncle duka na! Ammyn Abbina."
Yadda tayi maganar shi kan shi sai da idanun shi ya cika da kwalla, wato abinda ya Fahimta duk da manta kome iyayenta suna makale a ranta rungumo ta yayi ta fashe da kuka.

Rungume ta yayi, ta k'amk'ame shi tana goge fuskarta a jikin shi, daukarta yayi ya kai ta d'akin dan haka kawai yaji kamar zai yi baki, yana sakata a daki ya bata maganin barcin ta, ko minti biyar bayi da ita ba, yaji muryan Nazzir.

Rufe kofar d'akin yayi, sannan ya fito kallon juna suka yi sannan ya koma ya shiga tattara Broking glass din falon, ya kai waje. Sannan ya dawo yana jin shirmen Nazzir, da ya gaji ya kwanta tare da daura daya akan daya, yace "mishi idan ka gama shirmen ka ina zaka iya rufe min kofar gidan."

Haka na biyu, ma ta fasa wai zata yi wasan sauka da hawa, shima faɗowa tayi daga Center table din, na uku ne tayi a gaban Haroon, bai san tana gidan ba, lokacin da yaji karar fashewar abu a falon,.sama ne ya zo da dubawa yaga wata cutie face.

.kamar ya zura da gudu, amma ya tsaya, tare da kallonta itama kallon tsoro ta mishi sannan ta gudu dakin ta, shiru yayi tare da cewa a ranshi yaushe tazo.
Dan haka da Mahir ya dawo bai san abinda ya faru ba, sai da tace mishi.
"Uncle! Wani yazo?"
Shiru yayi tare da kallonta kamar yana son tuna wani abu, kafin ya shiga dakin shi na aiki ya ga, ai Haroon ne bai kuma bin ta kanta ba, domin shiri yayi akanta a cikin gidan.

---
Yau asabar, wanda yayi dai dai da cikar su wata daya da dawowa ta tashi da ciwon mara, haka tayi ta birgima gashi harun ya tafi kwara, tun daga d'akinta take fama har ta fito falo, shi kuma yana can Gym room, haka ta yar yada mishi jiki tun daga falon farko na sama har falon kasa, kuma taki zama guri guda.

Sai kuka take tana niman Uncle, yana cikin daki yana faman d'aga karfe, jin sautin muryan ta yasa shi, fitowa, yana zuwa ya ganta zaune ji yayi zuciyar shi kamar zata fado kasa, domin daga ita sai pant da wata shimi, kamar ya fashe da kuka, yadda ta b'ata ko ina, da jini. Haka ya rikota suka nufi ban dakin falon kasa, ya cika da ruwa ya turata ciki, sannan ya koma kitchen ya nufi loundry ya dauko bokitin mopping ya ciko da ruwa, zunzurutun tashin zuciya, haka ya zuba hypo, Klin, izal da dettol, sannan ya zo ya fara goge falon yana yi yana yatsina fuska, yana jin da yau Noorh da hankalin ta zai tasha faɗa, dan ya tsani kazamta.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now