Confessing

2K 195 24
                                    

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 2️⃣9️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Cikin shashekan kuka, ta gyada mishi kai tare da amince da abinda ya yanke akan makomar su.

Komawa saman kujeran falon yayi tare da daura daya akan daya, yana mata kallon renin hankali, tare da diban albarka, kafin ya mike bai kuma ce mata kome ba, ya wuce dakin shi, wani kasaitaccen murmushi ya sake, sannan ya lallubi wayar shi, ya kira abokan shi ya labarta musu yadda suka yi, wanka yayi tare da shirya wa cikin manyan kaya, dan ya gama shirya kome nashi dama ita yake tsumayen jin ra'ayin ta, haka ya gama tare da dawowa falo ya same ta a inda ya barta a tsaye, yana zuwa ya kalle ta, ya ga har lokacin share kwalla take.
"Idan bai miki ba, mu hakura naga kina abu kamar wanda ya tirsassaki, ga hanya sai na kai ki Airport ki kara gaba, na gaji da kayan taurin kai." Hawayen da take dannewa ne, ya zubo mata tace mishi.
"Ina tuna iyaye na ne, da suna raye a mutunce zaka aure Ni, a Yanzun da basu da rai sai na kamar bani da darajar kome, don Allah idan ka gama abinda zaka min karka tozarta ni, na san nayi laifi don Allah karka wulakanta ni, ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka, don Allah karka."

"Jeki shirya ina jiran ki!" Ya ce mata, tana juyawa yabi bayanta da ido, yadda yaga baki daya tayi laushi kamar ba ita, baya da ra'ayin wulakantatta har abada ba zai wulakantata ba, kawai yana amfani da haka ne domin ya kare soyayyar da yake mata, amma ba dan ya tozarta ta ba.

Yana sonta amma baya nufin zai bata ragamar rayuwar shi ta rike, shi yasa ya dauki shawarar Usman koda anyi auren na zai je mata kai tsaye ba, dole ya shirya hikima yadda zai na samun ta. Kuma.

Haka ta fito sanye da doguwar riga tare da babban hijab, suka fita. Idanunta yayi kyau a cikin hijab dinta, wani irin kyau tayi gashi fuskarta ya fito sosai, haka suka bar Unguwar shi da kanshi ya kai ta gurin saloon aka gyara mata gashi sannan ya saka aka mata duk wani abinda akewa amare, kama daga gyaran jiki zuwa lalle a farce da hannun ta, kai tsaye gidán limamin dake unguwar su Usman Kamfut, suka je aka rangada auren akan sadaki dubu saba'in da biyar tare da sisin gwal, tana cikin gidan liman din ya aka kirata, tare da mata wanka da turare, sannan aka zuba mata sadakinta, a lokacin wani irin kuka ne ya kwace mata, me mugun cin rai. Tana tuna mahaifinta da burin su, akan ta. Duk da bata iya tuna wasu abubuwan. Haka ya taso ta suka dawo gidan su. Tun a bakin kofar gidan, taga shima jikin shi yayi sanyi, dan haka suna shiga cikin gidan, ta wuce d'akinta.

Yana gama abinda zai yi sai gashi ya fito, ya buga mata kofar dakin ta, budewa tayi tare da sunkuyar da kanta, domin darajar aure yasa yayi mata wani irin girma da cika idanu.
"Zo na kai ki wani dakin.!"
"Amma kace cantract marriage ne, me zanyi a wani dakin After wannan."
"A bisa kudirar auren mu babu musu, kuma babu takura juna, sannan nayi miki alkawarin gyara duk wani kuskuren da nayi miki, sannan kuma a cikin wata daya zuwa biyu, ko hannunki ba zan kama ba."

Kura mishi ido tayi, sannan tace mishi.
"Na yarda da kai, amma kuma idan na gama aikina zaka sallame ni?"
"Me lafiya ma kuwa, Ni da kaina zan saka ki a jirgin sama zuwa garin iyayen ki.".

Gyada mishi kai tayi ya kai ta, lady bedroom. Kallon dakin tayi cikin wani irin mamaki da al'ajabi, sannan ya dauko wata akwati ya mika mata, tare da wasu shirgi yace mata.
"Daga gidan Marayun jos," amsa tayi tare da bude kayan cikin shi tana warewa, fita yayi tare da tsayawa a bakin kofar dakin yace mata.
"Idan kin gama karki manta da abinda zamu yi buda baki dashi, sannan gobe zamu tafi har Yola, karki Mantawa da Now you Are mrs Hamoud Boualem, dan haka a san shirin da za ayi zuwa gobe, dan bana son rashin nasara."

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now