stupidly

1.8K 174 28
                                    

https://my.w.tt/nRXa3Y11Scb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣2️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Budar bakin ta, cikin kuka tace.
"Wallahi dole yayi min domin ni bana son auren shi!" Cike da mamaki Ummi ta kalleta dai dai tana shiga cikin gidan.

"Kika ce baki son auren da kuka yi? Toh taya haka ya faru?" Kuka ta saka mata, har suka isa cikin gidan, ganin Shibha tayi da gudu, ta rungume ta.
"Aunty Noorh! Me yasa ki kuka? Yaya ne ya dake ki? Ummi dubu yadda?"

"Rufe min baƙi kiyi shiru, ki kaita dakin shi da yake sama," inji Ummi,
Kallonta Samiha tayi cikin fusata tace.
"Wannan ba yarinyar da ta lalata mana kamfanin mu bane?"
"Itace kuma matar shi!" Inji Ummi,
"What???"

"Toh wallahi ba zata zauna mana a gidan mu ba," inji Adeemah,
"Bata da masauki a gidan nan, zoki fita dan abukazan ki."

Inji Hidaya, ta fincikota zasu fita da ita.
"Ina ga kamar nice na zo da ita ko? Tunda Ni ce na shigo da ita babu ruwan ku da ita, kusake ta,kafin raina ya ɓaci da haukarku." Take suka shiga hankalin su, sakamakon yadda suka ji muryanta, sanin cewa idan ta barta a dakin Mahir ba zata sha ta dadi ba, yasa ta kira Shibha tare da cewa takaita dakinta. Domin tasan halin Yaranta. Suna da haɗin kai. Duk abinda ya sami daya toh kamar ya samu daya ne.

Tunda Shibha ta kai ta, dakin kallon duniya tayi sosai, cikin mamaki tare da al'ajabi take bin ko ina da ido, yadda d'an adam yake rayuwa cikin yancin da salama, Kamshin turaren dakin ne ya cika mata, hancin ta rike bakinta da take lubiyar amai,.da gudu ta nufi hanyar fita, suka yi kicibis da Ummi.
"Ga ban daki can, juya ki shiga"
Da sauri ta shige ban ɗakin,, tai yita kokarin juye shi,. amma bai fito ba, karshe zama tayi a ban dakin tare da kishimgida barci, tare da kamshin sabulun wankan da na wanke ban dakin yana ratsa ta, sai kuma baza hanci take, cikin kwanciyar hankali.
Idan ran Ummi yayi dubu sai da ya b'aci sosai, kallon Noorh tayi da take barci a ban dakin.
"Yarinya na! Tashi nasan ai kin san babu kyau kwanciya a cikin ban ɗakin, fito ki kwanta."

          Idanun ta ne suka cika da kwalla, tace.
"Ummi bana son kamshin turaren dakin ne."
   "Toh shi kenan, zo na kai ki daya dakin."
Haka ta mike jikinta babu kwari, amai take ji amma cikinta babu kome, ta wuce da ita daya bedroom ɗinta, ta kwantar da ita a saman gadon, sannan ta kira likita.

       ..... "Shibha gashi ki bata wayarta, don Allah ki tambaye ta meke damun ta, ki tabbatar ta i abinci."
"Insha Allah."
"Amma Yaya yarinyar nan fa tayi maka abubuwa da yawa, me yasa ka taimake ta?"inji Hidaya da Samiha, Adeemah kan ta cika tam kamar zata fashe.
Furza da iskar bakin shi yayi sannan ya juya yana faɗin.
"Kwatsam Allah ya juye min kaunarta, bayan nan bana jin akwai abinda zaku bukata daga gare Ni,.sai dai kar ka yarda naji wani kallon banza ya shiga tsakanin ku da ita. Naji haka toh zan sab'a muku."

      Daga haka ya bar gidan, dan wallahi ya rantse ba za a raba shi da matar shi kuma ace kar ya zo ba.
           --- tunda likita ya gama ainu ne ainun shi, ya amshi fitsarinta yayi mata duk wani test, ya fita, bai kuma dawowa ba sai dare dake ya saka mata drip, lokacin da yazo ya samu, ya kare tana sallah isha, nan ya mikawa Ummi sakamakon,.bata yi mamaki ba. Dan tun daga daukota ta fahimci danyen ciki ne da ita.

             Bata kuma bin ta kanta ba, ta sallami likitan, fada dai na Uwa da d'a Ummi tayi wa Noorh ita da Hajiya, dan sosai suka nuna mata illar abinda suka aikata, tare da mata barazanar sai sun kashe auren, dake yar banza ce bata da hankali, ai kuwa ta sake bakinta ta gayawa Ummi cewa bata son auren dole yayi mata, tare da gaya mata na kwangila ce.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now