Welcome to Hamoud Boualem Company...

2.3K 261 32
                                    

https://my.w.tt/nWJXAaLzxbb

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 0️⃣2️⃣
    MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

Welcome to HB Campany.

     Ina ganin rayuwa a tare dasu, amma nasan ƙaddara tace, kuma na shirya amsar shi hannu bibbiyu, ina gama saka unifoam. Ta fito bata da kunya, cire towel ɗin tayi tana wani irin taku, ga yan boons kamar na tashen balaga.

      "Sisters! Ni bazan saka babban hijab ba, zanyi amfani da  fashion hijab, kuma na san zan fita a haɗe domin Mommy ta sayo min rigar kara boons da kuma hips zan fito masha Allah."

       Tana fadar hakan tana kallona daga sama har kasa, sabida fitowar da surana yayi, gimtse fuska tayi ta wuce, aka shiga makeup, "karki manta yau shine first day dina da zan fara attended din inda aka tura ni, dole na hade gudun kar na hadu da my Superb"
Ta kashe min ido daya, sannan ya shiga niman kayan ta. Ta saka ina kallonta. Har ta dama tare da dauko cikonta ta saka.

..... A hankali take shiryawa wanda nayi imani da Allah da nice sai anyi kamar za a d'aga gidan, dan haka na zuba mata ido, tana gamawa ta tsaya a gaba na, kallon kirjin da hips din nayi naga sun cika tam, dariya nayi sannan nace mata.
"Ok mss world zamu iya fita."

Tsaki taja sannan ta dauki fashion hijab ɗinta ta saka, muka fito falo.
"Good Morning Mommy daddy"
     "Morning dear! Kin tashi lafiya ya yau kinyi mafarkin Mr Perfect kuwa?" Inji Mommy, Daddy ya fad'adda murmushin jin dadi, sannan yace mata.
"But kin mishi magana"
Cikin jin dadi tare da. Kallon su tace.
"Wowwww "
      Ta fadi haka tana jan kujera, sai da na zauna na gaishe su, basu kulani ba, sabida dreams din Yar su, suke son jin labarin shi, a hankali na fara zubawa kowa na shi, sannnan na zuba nawa na fara ci.
"Noorh wato ba zaki daina kyashi bako? Me yasa kike da mugun hassada ne? Ki tayata jajjanta yanayin ta ma, kin kasa noorh farin jinin Tasleem kike bakin ciki dashi."

    Kallon su nayi, dama sun saba min haka, idan suka fara ina tashi na bar musu gurin cikin abincin ne. Yau kam ban zan iya barin gurin ba, kuma ba zan musu magana ba, sai da na cinye abincina, na mike zan bar gurin Daddy ya daka min tsawa.

"Koma ki zauna, wato dan bakin ciki da hassada, shine ba zaki iya taya Tasleem murna ba, wai me yasa kike son kanki da yawa ne!"
   Sunkuyar da kaina nayi, hawaye na zuba min, ina kuka jin kewar iyayena, a sanyayye na ce musu..
"Kuyi hakuri!"
     Daga haka na bar falon nayi tafiyata, ina cewa.
"Insha Allah zan tara kudi na tafi wurin dangin Ammina na huta, da bakin halin da ake jifana dashi "

              Ban tsaya jiranta ba, dan ita ta iya mota, ni kuma sunce ai ba lallai na iya ba, tunda mijin da zan aura bai wuce a sama min me matsayin malamin secondry school ba. Shi yasa nima ban damu kaina ba, yan kudin da ake bamu kyauta, idan Daddy yayi baki.

keke napep na hau ya kai ni, inda inda zan duba post dina, abin da na gani bai yi mamakin na Tasleem ba, amma ni kuma taya za a kaini Hamoud Boualem Company, me zanyi a can ni da nake yar jarida,

       Shiga nayi na musu bayani suka ce ai tun jiya aka shigar dani, cikin jerin sunayen mutane da zamu je can dan haka babu wani abinda zasu min. Gaskiya am feel bad, haka na juya zuwa in gida. Dan naji ana cewa Inda aka turani akwai nisa.

       A hankali na shiga gidan babu kowa, Mommy tana dakin ta, nima na haura na wuce dakin mu, ina zuwa na cire kayan na kwanta, dan haka babu wanda ya san na dawo, kuma indan so samu ne yau na fara zuwa gurin da aka turani.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now