Kidnapped

1.8K 225 21
                                    

https://my.w.tt/BYUEG7lptcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 1️⃣8️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

Hmm 🤨🙄

Murmushi nayi mishi tare, zama na daura d'aya akan daya, ina kallon shi, tare da murmushi. Huci yake amma zuwan wani mutum naga fuskar shi ta sake, tare da mika mishi hannu, kawai ji nayi jikina yayi sanyi, a duk lokacin da na d'ago kai na kalle su, zanga suna hirar su alamar ma basu damu da ni ba.

    Kai musu abin sha Waiter yayi, sannan ya koma ya kawo min nima kamar ba zan sha ba, na amsa sannan na d'an kurb'a, na zauna ina kallon yadda ake abubuwa kafin na ji yau ina sha'awar buɗe sakon wayata, a hankali na fara duba email. Jin ana hayaniya ya sani hakura da shi na mike tsaye tare da kokarin barin gurin, ban daki na nufa sannan nayi uzurina kafin na fito zan bar gurin.

     .. juyawa nayi tare da kallon shi, yana tare da mutane, haka kawai nake jin kamar kar na bar gurin sai naga ya bar gurin, amma tsabar na yarda da kaina na juya nayi tafiya ta, sai da na fita naga garin ya fara duhu, dan haka na d'an kara sauri kasancewar dare ya fara yi, gashi babu abin hawa, a hankali nake kallon rufaffun shagunan dake gefe da gefe, kamar na fasa ihu domin gurin da nake babu kowa sai wucewar ababen hawa, nayi tafiya me nisa kafin na isa wani unguwa babu mutane a layin sai dai motar bus, da wasu kartin maza suna tsaye tare da shaye shaye, jin cikina nayi, ya hautsine.

              Ina isowa inda suke, suka ce.
"Barka dai Yar jarida!" Ji nayi cikina ya kulle. Kirjina yana bugawa tare da tsallen da zuciya ta take, had'iye yayi nayi sannan ina ji daya su yana cewa.
"Sir! Gata nan zamu kai ta!"
"Zo ki shiga!"
Juyawa nayi zan fasa ihu, sai ji nayi kamar sun samun wani abu a fuska na, Atishawa nai sannan na zube a gurin.

             ---
Yana gama abinda zai yi ya juya tare da barin gurin, bayan yayi sallama da mutanen, tun daga nesa ya hango jakarta da takalminta, dauke kai yayi har suka isa gurin, har sun wucce kawai yaji zuciyarshi ta kasa samun sukuni, dawowa yasa Wali yayi sannan ya fita daga motar, ya iso gurin kayanta. Abinda ya fara kiran yan sanda.

          Cikin abin bai fi awa daya ba, b'atar Noorh ya zaga ko ina, lokaci ƙalilan, aka shiga nimanta.

   Duk tambayar da ya dace anyi, sai dai a take wasu suka bada shaidan shi yasa aka dauke ta, dan abinda take Mishi, wasu kuma suka ce bai bar gurin ba sai bayan tafiyar ta da dogon lokaci ya fito.

    Cikin awa daya kalmar Mahir ta daure shi, yayinda Yan jarida suka Mishi caaa, take akayi amfani da hakan domin a yake shi sai an kai shi kasa.

       ***
Barci take hankalinta kwance, kawai taji saukar ruwan sanyi, wani bahagon ajiyar zuciya ta ta sauke, a tsaye suke a gabanta fuskokin su a rufe, a hankali ta mike da jikakken kayan jikinta, doguwar riga ce fara kai, sai wando iya gwiwar ta, a cikin rigar. Sai Pink bra da ta saka, wanda ya dace da shigar ta, ruwa da aka kwara mata ya fitar da baiwar da Allah yayi mata, domin bra ɗinta irin me net din nan ne har kana hango nipples ɗinta,  da suke mike curr.

        Had'iye yawu suka yi tare da kallon yadda take diga,.gamon gashin kanta ya warware, niman hanyar fita take, tana kallon bayanta. Gammmm taji saukar wani abu kamar karfe a kanta, zubewa tayi tana kallon Manager ya bude abun fuskar shi tare da Aysar Haladu, suka fashe da dariya, na ukun ne bai bude fuskar shi ba, shigowar na gudun su lokacin ta suma ya d'aga rufin fuskar shi Nazzir.

       Kiran wayar shi Mahir yayi sannan ya saka wayar a kunnen shi.
"Lion Man! Lafiya?"
"Yarinayr nan an sace ta! Kuma Ni nayi mata barazana..don Allah kayi wani abu! Ko kuma nayi wani abu, dan wallahi na kama wanda ya sace yarinyar nan wallahi Allah sai na kashe shi.!"

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now