Promotion

1.8K 180 23
                                    

      https://my.w.tt/8Q5hDfaJJbb
   MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣6️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~promotion~

A cikin dakuna biyun man akwai
Manyan bath tub na Alfarma, wanda mutane biyu zasu iya shiga su zauna,
   Second rum akwai.  Retangle corn tub, musamman daga Japan aka zo dashi, aka saka a cikin bathroom din,

Sai third rum, akwa  luxury alcover tub, shi kam wani zuwan Mahir Moscow ya zo dashi, dan ya burge shi.
A ta wajen gidan akwai wani katon costco hot tub, na wanka  aka ajiye shi. Shima mutane biyu zuwa sama da biyu zasu iya shiga cikin shi suyi wanka. Sai kuma Luxury Gym room inda aka zuma inda kayan kayan karfe ne da yake d'agawa, sabida murdewan jiki.

       Sai Games room, inda aka zuba kayan games na manyan maza har da karamin Bar, gidan a iya kawatuwa ya kawatu, zai yi wuya ka shiga gidan ka fito cikin dadin rai, sabida babu inda bai hadu na.

      Duk wannan haduwar gidan bai tab'a burge Mr Mahir ba, sabida yayi alqawarin duk wacce zata shigo gidan, toh ba karamar jaruma ba, shi yana da buri. Amma ya barshi da mahaliccin sa.

       ••
"Maryam! Shin ba zaki yiwa Mahir magana akan auren nan ba, anya kun min adalci? Haka zan koma ga Allah banga jikokina ba?"

      Cikin nutsuwa Ummi ta gyara zama sannan tace mata.
"Jaddih kiyi hakuri! Wallahi Baba kaman me cutar aljanu, wancan watan da suka wuce Ni dashi muka yi magana akwai Nabeeha yar abokiyar aikina tana Kano, mun yi aiki da ita aka meda ta Kano, yaron nan suka haɗu da ita yarinyar me sunan. Anjum, hmm Yarinayr ta dama haukacewa akan shi. Tana komawa gida ta nunawa mahaifiyarta da Murna Uwar ta kirani take gaya min ashe Mahir ya dawo. !na amsa mata da eh anan take labarta min yadda suka yi da yarta, hmm Hajiya na sami Mahir muka yi magana tare da niman Alfarmar kar ya kunyata ni."

Dariya Alishbah tayi tare da cewa.
"Ummi bari na bata labarin abinda ya ce da yarinyar. Lokaci da yaje ya dawo, dan ko awa uku bai yi ba. Jaddih yana zuwa bai yarda ya shigo ba sai da dare.

         Kamar wani wanda ya had'iye wuta haka ya shigo, ya zauna Ummi tace "Baba ya hanya da fatan ka ga yar gidan Hajiya Halimar?"
     
Kallon wani kujera na musamman tayi a falon, ta muna kwashewa da dariya sannan ta cigaba da cewa.
"Jaddih bawan Allah nan ya gyara zaman shi akan kujeran, kamar wanda Ummi tayi mishi fada, ya cigaba da latsa wayar shi. Sai da Ummi ta kuma magana ya bude baki kamar wanda yake ciwon hakuri yace.
"Ummi don Allah meye laifina da zaku hada ni da wata yarinya me siffa kamar tumatir, gaskiya bazan iya rayuwa da ita ba!"

  Haka ya mike tare da barin gidan, nan shiru Ummi tayi  ina ganin kawar Ummi tana kiranta amma taki dauka.

       Idan baki manta ba akwai Jadwa yar Kanwar Ummi, haka yarinyar nan ta haɗu da Ya Mahir, Cope town tayi ta mishi magana, ya Mahir ya shareta sai da suka zo hutu, ta mishi abinci ta kai mishi wancan dakin Ya Mahir ya juye abincin Karen shi Dolna. Wai bata iya girki ba. Ko shi ya shiga kitchen sai ya dafa abinda zai fi nata.
Karshe munafikin karen shi yayi ta barci shine ya dauko wani bindigar shi wai sai ta gaya mishi me tasakawa karen yake barci."

    Aikuwa kakan tayi shiru, tana sauraron jikarta, gyara zaman lullubinta tayi sannan ta kuma rike calbin hannun ta, ta sake murmushi. Sannan tayi gyaran murya tace.
"Ashe yana magana haka?"
"Hajiya yana yi, idan yaso idan bai soba sai ya manna abu a kunnen shi yayi shiru abin shi Allah kadai yasan yawan mutanen da Baba ya sani jin kunyar su, daga yace wancan ta cika kyau, tayi fari da yawa, sai yace ta cika surutu, bakinta babba ne, kai ina bakinta yayi karami wai kawai na tambaye shi Yarinyar tayi maka? Shine sai yayi ta zage su, akwai yarinyar da yace min wai Ummi wancan yarinyar tana da kirji da yawa, haihuwa daya zasu kwanta, wata kuwa ce min yayi idan ya fara tsufa tana da boom zata iya rasa gwiwarta, wata kuwa ce min yayi matsalar yarinyar ta haɗu sai dai guntuwa ce, daya kuma yace min tayi tsayi dayawa, Hajiya babu yarinyar da ba zai kusheta ba, daga tayi tsayi sai ta cika siranci. Na rasa gane mishi kuma idan zai fasa ba zaka ga yayi dariya ba fa a'a cikin kamewa yake maganar"

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now