i'm in luv

2K 232 47
                                    

https://my.w.tt/6c5DIJjMLcb
MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 2️⃣7️⃣
     MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

*Great joy to see your enemies turn into your lovers, Great sorrow to see your loved ones turn into your enemies*

Girgiza kai yayi cikin sanyin jiki, yana kallon Dr, bai barshi ya kai karshen Maganar shi ba, yace.
"Ina da ra'ayin SOYAYYA! Bana son hada shi da wancan abun ina son na bata damar ta fahimce ni, yadda zata nime ni da kafarta bawai na nuna fin karfina akanta ba.

     Shi kuma wancan d'an iskan kyale shi lokaci nake jira akan shi. Idan yazo zan bashi damar haka.'
"Amma for your health!"
"Karka damu, a da nace maka zan tawo da ita ban san wacece ita bane, sai da na binciko labarinta, na fahimci wacece ita.

    Zaman jinyarta kawai ya sani kara nutsuwa da ita, bawai dan wani abu ba,  ba zance am in love ba, amma am feeling sumtins akanta yadda take rigimammiya, bata da tsoro.

     Duk abinda zata yi kai tsaye take yi, wich means anyi raised ɗinta haka ne, so nake ta koma kasa da ni, yadda kowa na nime aurenta zata dauke ni a matsayin mijinta, idan nace zan yi abinda kake bukata, dama ta rena ni ba wani jin dadin zaman zanyi da ita ba. Shi yasa na ki kawai ka barni da ita, Insha Allah zan duba Alamarin."

      Wannan ra'ayin rikau na Mahir da ban haushi yake, dan haka Dr ya kama kafar ya nad'e da bandaji, sannan ya gyara mishi, yana jin shi yana nishi, suka kuma fashe da dariya, kafin Mahir yayi wani kara irin na jin jiki.
Tana waje sai zarya yake kamar wacce ta aikata mugun abu, fitowa Dr yayi ya same ta a dame.
"Hmm! Ayi a hankali dashi domin kafar ta kwaɓe, kuma ina dai kin san ba zaki kula dashi ba, na kira familyn shi"

"No-no. Zan iya kula dashi, don Allah karka bari su sani." Ta faɗa muryanta na rawa, kad'a kai yayi ya ficce daga cikin gidan, a hankali ta shiga d'akin, yana ganin ta ya dauke kan shi kamar bai ganta ba, cikin sand'a ta shigo dakin tana kallon yadda aka daure kafar,  zare medical glass din shi yayi tare da kuma dauke kai.

"Ina son ruwa zan sha magani!"
Da sauri ta juya gurin dan karamin frij da yake dakin yace.
"Bana son me sanyi."
Fita tayi, ya sake murmushi yace.
"Zaki dawo ki koma."
Tana shigowa,.ya dube ta daga sama har kasa yace mata.
"Ina kofin da zan sha ruwan?"
Juyawa tayi ta fita, can ta kuma dawowa..ya dauke kai kamar bai san da ita ba.
Haka ta bashi ruwan ya sha, kafin ya jefa VC ya kuma korawa da ruwa.
    Tana tsaye kamar status, bata ko matsa ba, sai da yace mata.
"Yanzun haka zan zauna da kafa daya? Gashi Dr yace idan kafar bata warke ba za a iya yanke min shi!"
Cikin wani irin faduwar gaba ta kalle shi. Bakinta yana rawa,
Gyada mata kai yayi idnun shi kwal-kwal, akanta kamar zai yi kuka.
"Am sorry!"
"Please give me a Little hug!"
Ya mika mata hannun, buge hannun tayi cikin masifa da damuwa tana fadin.
"Ko tausayin  kanka baka ji, kana niman magana."
   Fita tayi, tana nazarin me zata bashi yasha domin ance duk lokacin da mutum ya kone yana bukatar abu me sanyi dan haka ta dauko fresh milk, ta zuba a kofi ta kawo mishi, ya sha.

     Har zata tafi yace mata.
"Idan zanyi fitsari ko pupu waye zai raka Ni?"
Dafe goshinta tayi tare da cewa.
"Kai kan da kunya kabi kudu yabi yamma. Ba zan zauna daki daya da balagagge ba."
Ta juya tayi ta fitarta,  tunda ta koma d'akinta ta kasa sukuni, bata minti talatin zata zo duba shi, dan renin hankali yana kwance kamar me barci idanun shi biyu.

                 Ganin har karfe biyu saura tazo duba shi, har dai dai inda yake kwance..tazo duba fuskar shi, kawai ya fincikota. Tare da matse ta a jikin shi.
"Don Allah sake ni!"
"Shiii! Just sleep!"
Ya faɗa mata a hankali,  haushi ya bata ta kai mishi cizo, shi kuma ya sake mata wani irin nishi a kunnenta sai da tsigar jikin ta ya mike tayi shiru, tare da jin wani irin kasala ya saukar mata once, murmushi jin dadi yayi tare da gyara mata kwanciya, kasa barci tayi..yana jin bugun zuciyar ta..har zuwa lokacin da barci yayi gaba dashi. A hankali ta juya yana kallon shi. Idan ta tuna lokacin da yake bata wahala sai taji ranta ya b'aci, a hankali ta zame daga gadon. Tayi ficcewar ta.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now