Hamoud Boualem Family

2K 215 39
                                    

https://my.w.tt/fpBMaONrHbb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣5️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~#HB Family~

Wani dan iskan rawa jikina yake tare da zaro idanu waje, cikin karaji tace.
Fitar min a gidan Ubana, bana son kuma ganinki, bana so? Bana kaunar ganinki, fita ko na saka a kashe min ke!"
   Ta shiga turani da karfin tsiya, hawaye ke tsiyaya a idanuna, a hankali momy ta tako tare da zuwa gaban mu, ta kifa min mari.  Kafin ta kuma d'ago kaina.
       "Ke! Kike niman hanyar da zaki wargaza farin cikin Baby Queen?"
Bakina na rawa nace mata.
"A'a momy wallahi ba  yadda take tsammani bane, wallahi babu kome a tsakanin mu, kawai tana zargi ne don Allah kiyi hakuri wallahi ba zan kuma shige mishi ba."
          Kallona a hankali tana danne zuciyarta ga abinda yake tinxirata, gani take me zai hana ta lalata fuskar da mutane suke rawan kai akan shi. Idan ta tuna kuma yadda dangin Mahaifiyar Noor suke mahaukatar masu kuɗi ne, sai taji jikinta yayi sanyi. Dan tasan tana tab'a lafiyar Noor kamar ta kashe yarta da ranta ne.
     .Sake ajiyar zuciya tayi sannan tace mata.
"Karki kuma sakewa naga kin fita zuwa HB. Company idan kuma na fahimci haka toh zan lalata miki."
"Insha Allah ba zan kuma ba kiyi hakuri don Allah."
   "Wuce ki bani guri."
Da sauri na bar falon tare da hayewa sama, ina wucewa suka bini da kallo.
"Momy!"
"Bana son ci da zuci, idan muka mata wani abu kece zaki fara faduwa, idan muka barta kece zaki moreta. Dan haka ki zuba mata ido, zan barta ta koma amma kafin nan kin shigewa Mr Nazzir.

Yadda babu wanda ba zai san kuna soyayya ba, karki sake ki bada damar da wata zata gane cewa kina jin haushin Noorh, dan haka ki shige mishi. Insha Allah akwai wata mata mari, tana hada magani na musamman, sabida irin su Mr Nazzir.

        ---
A hankali na zube a bakin gadon,  na fashe da kuka. Tare da dafe goshina..ina kuka ina karawa, sai da nayi ya ishe ni sannan na mike na cire kayana na shiga ban daki nayi wanka tare da alola na fito.

           Na saka dogon riga, tare da hijab nayi sallah. Sannan na kwanta a kan abin sallah. Ina sauke wasu kwalla masu shegen zafi. A hankali har barci ya dauke ni.
      ---
Lagos.
A duniya Allah ya halicci mutane da halayyar su daban daban, wasu zaka samu suna masifar son sanyi wasu kuma suna son zafi, haka wasu kuma suna matukar son ruwa. A cikin wannan dabi'ar Mr Hamoud Boualem ya gina Iyalin shi. Mutum ne mai matukar kaunar ruwa. 

        Shi yasa da ya tashi gina gidan shi ya gina a bakin tekun Lagos, a banana island. Inda ya saka ka je har kasar Kuwait aka zano mishi hoton wani dankarerren gida, me mugun kyau, inda ya sanyawa gidan sunan.
Narrabeen beach housa. Yayinda mutane kewa gidan lakabi da honey house, kasancewar gidan guda hudu ne a cikin unguwar.

   Gida na daya gidan Shi da iyalin shine, kafin rasuwar shi. Four bed room ne, sai kitchen guda biyu da falo uku.

    Hajiya Maryam itace matar shi, daga ita bai kara aure ba, ita daya ce tal. Hajiya Maryam tana da yara biyar namiji ɗaya sai mata uku.
Mahir shine babba, me shekara talatin da uku, sai Hadiya. Wacce take da shekara shirin da takwas. Tana aure a lekki. Sai Suhaila wacce take da shekaru ashirin da hudu, tana karatunta na karshe a Calgary.
    Sai Adeemah wacce shekarunta Ashirin da daya, tana karatun a jami'ar Abti Yola, sai yar Uwarta su Alishbah. Itace take secondry school, ss2.
        Mansion din cike yake da ma'aikata, wanda suke karkashin kulawar mahaifiyar Mahir, kasancewarta babbar  Judge na garin lagos.
Mace mai addini da Sanin ya kamata, sannan bafulatana ce gaba da bayanta, dan ko Hausar ta har yanzun bata ware ba. Gidan.
       Sai Mansion na gaba, gidan Barraq Abu Aswad, Mahaifin Mr Nazzir Abu Aswad. Kanin ne ga Hamoud Boualem, wanda suka kasance Uwa daya.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now