Lover

1.8K 167 29
                                    

https://www.wattpad.com/1013100816?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=NXlDHteSUiFoeVV42LoweRgFvkHNx7xBa8D4DmWqpUCwAbPM%2BtzNQwzO2KIOXp%2Bz8otQZ2oWI1ovCSEsEuUaTefzfifZ3q%2Fn0VpLvsrSlIiciStjykoqA6QZyUx1k%2Fkg
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 4️⃣0️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Cikin tsananin tsoro take kallon bakin Mahir, zuciyarta na ta fasa zata kuma magana Faruq ya kuma kafta mishi naushi,

      Aikuwa ya juya tare da zuɓewa a jikinta, kallon juna suka yi.
"Bari na tsaya ya kashe ni kawai."
Aikuwa Sha-sha-sha ya kuma janyo shi zai rufe shi da duka tace.
"Ya isheka haka! Ina ruwanka damu? Kai yayiwa laifi ko ni? Ka kama sai dukar shi kake kamar abu mara daraja, ni... Ni....Ni!"

           Murmushi Mahir yayi sannan ya goge bakin shi ya gyara tsayuwar shi, kallon Noorh yayi kafin ta bude baƙin ta, ya zabgawa Faruq naushi har yana wani bouncing, tare da murmushi.
"Wai meye haka ne? Na hana shi kai ma zaka fara zak..."

    "Ikon Allah! Kai kundun ubanku! Me yarinya tayi muku da zaku saka min ita a gaba, kaji yan banza masu rusa rusan kai.

  Maza ku b'ace min da gani, tunda baku da hankali kunzo zaku daurawa yarinya jidali."
   
   Kallon Dadah Mahir yayi daga kasa har sama, sannan ya soke hannun shi a cikin aljuhun wandon shi, cikin shegen halin shi yace mata.
"An jima zanzo na dauki mata na, ko a sallame ta.."
"Kai dan gidan Uban waye da kake magana da Dadah kai tsaye?" Inji Faruq,
"Ni dan gidan Ubana, kuma akan Idanka zan zo na dauki mata na da cikin da yake jikinta, i don't care da abinda zai faru, amma yau My Wify zata kwana akan Arms dina ne..idan ka isa karfe tara da rabi ka dakatar dani."

       Juyawa yayi ya sumbaci, goshinta, sannan ya kuma takawa gaban Faruq.
"Zaka sha mamaki akan idonka, zata bi mijinta. My sweetheart ki shafa min Baby Love, ki gaya mishi Dad yazo dan haka yayi kicking a hankali,.kuma a ci abinci dukda nasan wacece matar da nake aure, Mr Faruq Hisham Abdullahi keluarga, be careful."

    Tunda ya fita daga Dadah har Faruq kallon Noorh suke, jikin su a mace.
"Dada! Muje gida kullum zasu zo su dubata, idan muka isa gidan zanga yadda zai shigo gidan."

    Kallon shi Noorh tayi ta shige d'akinta, ita da Maman Faruq da Maman Habib, aka shiga hada mata kayanta, duk maganar da ake bata kula su, ba haka suka bar asibitin duk da Raliyah ta sami labarin abinda ya faru, bai hanata gargad'in Faruq ba. A hanyar gida ma, sai da Dadah yayi ta mishi shagube.
"Yau naga ikon Allah, da fin karfi kabar miji da mata suyi rayuwa kayi wankan tsarki zaka hana ruwa gudu!

   Toh zauna ka hana su, su wataya. Bayan kai ka gaza shawo kan taka matar shine su bari ka rana su da tasu soyayyar. Idan nace maka me rankwalelen kai, ka fata huci gashi nan rankwalelen kan bai maka rana ba,ka dubi Noorh da kyau mijinta take so,ka zauna kana Shashanci shiga ranar ruwa a damina, toh wallahi kafita idona kafin na sab'a maka,"

     Haka ta wanke shi tass, sannan suka isa gidan, tunda suka shiga cikin gidan Noorh ta sake bakinta tana duniyar da aka shirya mata, dakin da zata zauna. Jikinta ne yayi mata sanyi domin ganin kome take like a dreams.

    Yau d'akinta ne aka ware mata kamar wata princess, ga masu aikinta a tare da ita. Sai dai kuma duk wannan abin da ta samu har yanzun ji take bata cika mutum ba, domin Mahir shine cikon rayuwarta, a yau da ta ganshi kome ya tsaya mata. Dan haka ta shige dakin ta rufe kofar taki tayi magana da kowa, masu kula da ita ma koran su tayi.

        Har Magarib Mahir bai shigo ba, sai ma kara jin haushin rashin zuwansa, A kasa kuwa Faruq ya kasa ya tsare sai ga ta inda Mahir zai shigo musu gida.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 19, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now