destinations

3.6K 278 19
                                    

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 0️⃣1️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
https://www.wattpad.com/981993411?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published

#Destination
From lagos to Yola...
Gudu suke a cikin jirgin kasa, wanda yake tafiya cikin sauri, fuskarta lullube da wani yadi me hade da fari da baki, sai motsa gashin Idanu ta take cikin jin dadi, sannan ta mai da glass ɗinta, duk da bata wuce shekara goma sha biyu ba, amma haka ba zai hanaka fahimtar tsantsar kyan da Allah yayi mata, tab'ata kanwarta tayi tare da cewa.
"Adda, zan sha madara."
Kallon iyayen su tayi sannan tayi magana cikin shagwaɓa tare da faɗin.
"Mom! Ni fa idan muka isa kawai gidan su Nunu  zan sauka ba gidan kaka ba. Ina zuwa rinka damuna da A'isha kaza Aisha kaza."
          Kallonta matar daya gefen tayi cikin murmushi tace mata, "Ya sunanki?"
"A'ishah!"
Ta faɗa a sanyayye, kamar yadda muryanta yaƙe,
Murmushi matar tayi sannan tace mata.
"Toh baki nuna mana fuskarki ba, hanya ba zamu yi na gida dake ba, Hidaya, Raziya. Umar.  Alhaji Ina Maher yaƙe? Kuzo nan."
Lokaci guda suka haɗu, tare da cewa.
"Ummin Maher lafiya?"
Dafa shi tayi sannan ta nunawa Mutumin Aisha da take zaune, tana kallon su. Sannan ta kalli Iyayen Aisha, tace musu.
"Yar su na gani ina so! Tunda zasu sauka a Gombe ne mu kuma A Yola, shine nace ko zamu hada iri da ita shi Sunan shi Muh'd ita Aisha kuma kunga hadin zai yi ai?"
   Dariya suka yi sannan suka ce.
"Toh wallahi sai kin buɗe mana fuskarki mun gani,"
Cike da mamaki ta d'aga mayafin kyakyawan fuskar ta ya bayyana,
Masha Allah. Gaskiya tayi mana.
Sai Lokacin Mahaifiyar Aisha tayi magana tare da cewa.
"Toh indai haka ne toh ba sai ayi magana ba,"cikin Dariya ta kai karshen Maganar ta.
Shima baban Aisha din yace.
"Kun shirya kenan? Toh ni zan amshi auren kenan."
Jin haka yasa Yar yarinyar ta mike da gudu tabar gurin su.
"'laaa! Kunga ta gudu."

     Garin gudu ta bangaji wani mutum, tsayawa tayi tare da kallon shi badan kome ba, sai yadda ya rike mata arms ɗinta, kallon shi tayi cikin idanu ta buge hannun shi, tare da fallasa zata gudu ya dawo da ita, gaban shi, ya kai hannu zai d'aga mayafinta, yana kallon cikin idanun ta, sai ji suka yi kamar jirgin zai sauka kan digar shi kuma ya cigaba da tafiyar... Ya kuma dage sai ya d'aga mayafinta. Tana buge hannun shi. Ya kuma fusata zai bude mayafinta abokan shi suna musu dariya, ta kuma buge hannun shi, cikin dan banzan tsiwa tace mishi.
"Dalla kyale ni, an ce maka kowa irinka me mara kirki, ka nace sai kaga face dina, who are you?"
Yadda tayi maganar cikin rashin kunya da Rashin mutunci ya sake fusata shi.
"Waye Babanki?"
Cikin ɓacin rai ta d'ago kanta idanun ta na cikowa da kwalla tace.
"Babanka ne!" Ta bashi amsa kai tsaye.
      "Laaa! Man kai ne ta gayawa magana yarinyar da bata fi sa'ar Sister ka ba, lallai ka ci ubanta!"

       Bude eyes din shi yayi akanta, ya kai hannun shi ya dafe inda take, sannan ya sunkuyar da kanshi, dai dai fuskarta kamar zai sumbaci ta, ta saka hannunta da karfi ta ture shi tare da barin wajen da gudu, tsaki yayi yana faɗin.
"Fawwas kai banza ne, sai ta rena ni"
     "Idan ka buɗe fuskarka ba, ko ka manta akwai hirami a fuskarka."

     Dariya suka saka, ya koma mazaunin shi yana wasa da wata yar takarda shedar shiga jirgin, wanda aka rubuta Yola.
......
"Toh Sadakin wannan zinariyar dai ya fi karfin kudi sai dai mu biya da zinari irinta."
    Dan haka gashi wannan zai dauki kudi masu yawa, na bada sadakin." Amsa Maman Aisha tayi tare da kallon ana dariya aka cika sharudan auren babu b'ata lokaci aka daura auren, a gurin a ranar goma ga watan Maris, ala dubu biyu da tara. A cikin jirgin kasa da zai kai mutane zuwa Yola da abuja.
          Bayan sun gama, kenan Maman Aisha ta mikawa Mahaifyar Mahir, kayanta suka ci-gaba da hira, jin wasu alamomin da jirgin yake zai sauka akan hanyar shi ya mugun daga musu hankalin.
Take masu yara suka fara niman Yaran su, Aisha iyayen ta suka mike niman ta, kafin su isa inda take jirgin tayi wani irin kara tare da fadawa hanyar da ba nata ba, kafin kace me sun hadu da wani jirgin da ya dibo kaya zuwa Lagos, dake jirgin dasu A'ishah suke ciki.akwai mai  taragon farko, suna haduwa da juna suka wani bada sauti dammmm. Kafin kace me. Jirgin ya kama da wuta, sosai a take, yayita bin jikin jirgin gashi babu halin tsira, domin kana fita ma faduwa zakayi a wani abu dan wasu sun gwada haka, amma babu ci, domin suna fita jirgin mutum yana faduwa zaka ga bai shura ba, gashi a hatsarin ya faru ne a garin Barikin Ladi, na garin jos. Sabida jirgin zai bi ta garin bununu na bauchi state, sannan zai sauke fasinjar Gombe, har dasu Aisha a cikin masu sauka gombe...

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now