Hopefully

1.8K 191 47
                                    

https://my.w.tt/SwMczZ4vXcb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣6️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Yadda take fadar zata baka dariya da mamaki, amma iya gaskiyar kenan. Dan haka suka kyale ta, tayi ta masifar ta dan sun san halin ta, da iya faɗa.

         .... Washi gari da ta isa asibitin.
"Wayyo Allah na, ku kyale min Babyna, karku ta mun babyna."
Tana shiga, ta ajiye kayan hannunta ta nufi dakin da aka kwantar da Noorh take ihun babynta, tana shiga ta same ta can kuryan gado, ga jinin da yake bin kafaffunta. A hankali ta taka har bayan Noorh din.
"Zo zan baki babynki." Da sauri ta juya tana kallon Dr Naaz.

       Mika mata hannu tayi, tare da takowa a hankali, sabida ciwon da marar ta yaƙe, ta nuna mata gadon, ta kwanta. Allura tayi mata, sannan ta saka nurse suka kawo gadon marasa lafiya, aka tura ta a kai, wani daki aka shiga da ita, nan Dr Naaz. Ta nutsu a binciken lafiyar cikin, abin tausayi cikin yana nan bugun zuciyar shi yana nan normal.

            Shafa kan Noorh tayi cike da soyayyar ta, cikin nutsuwa ta shiga ƙoƙarin daure bakin mahaifar, dakyar ta samu ta daure cikin, sannan ta gyara mata kwanciya aka kuma fito da ita. Har yamma bata farka ba, sai tsakiyar dare, sannan ta bude idanunta. A hankali taso tashi taji an daureta, komawa yayi ta kwanta tare da jin nauyin cikin ta. Kallon Dr Naaz tayi tana zaune ta daura daya akan daya, dauke kai tayi tare da jin kwalla yana cika mata idanu.
"Ga abinci nan, nasan lafiyarki ta samu ba kamar da ba, sannan yana da kyau ki nemi yan uwanki su tsaya miki domin jibi za a fara shari'ar ki, kuma hukuncin kisa ce ga duk wanda ya shigo da miyagun kwayoyi."

     Kura mata idanu tayi, sannan ta fashe da kuka. Tare da dauke kanta, tana tab'a cikin Jikinta.
"Wallahi ban san kome ba!"
"Na sani mana,. amma ai su ba zasu fahimci haka ba, ina yan uwanki?"
"Ban san inda zan same su ba!" Ta faɗa cikin kuka,
"Toh me ya kawo ki kasar nan?"
"Nazo niman sune?"
Kura mata ido tayi iyaka kokarinta bata hango cutar haukar ba, dan haka ta mike tare da cewa.
"Daga wata ƙasa?"
"Nigeria!" Da sauri Dr Naaz ta kalle ta, cike da mamaki. Dawowa tayi ta zauna tana kallonta.
"Ya sunan ki?"
"A'isha Omar!"
Kura mata ido tayi zuciyarta yana girgiza, kafin ta mike bata ce mata kome ba, tunda ta fita Noorh ta shiga ƙoƙarin kunce daurin da aka mata, tana kuncewa. Ta sauko a gadon tare da kallon window, a hankali ta bude ta zura kafarta ta sauka cikin rashin sanin ta taka wani karfe sai da ya huda mata tafin kafarta, burin ta tabar asibitin kawai.

       Kamar wanda ake ingiza ta haka ta bar asibitin, ta bazama gari, tunda ta bar asibitin ba a lura da haka ba, sai washi gari da Dr Naaz suka zo da iyayenta, anan suka samu bata nan, ga lokacin da take kunce kanta,da yadda ta dira ta window. Da sauri aka duba bayan, ga yadda jini ya b'ata ko ina.

     Abin tambaya taya haka ya faru? A lokacin hukumar yan sanda suka zo,nan suka bazama nimanta a gari.

     •••
Lagos.
Yau kwana biyar, ana shirya babban bikin baikon Mahir da Tasleem. Sai gyarata Mommy take sosai gudun kar yazo musu da abin damuwa.

     Mahir da Ummi, kuwa daukewa Yaranta wuta tayi inda ta kore Samiha da Hidaya,.tare da cewa karta kuma ganin su Adeemah kuwa, sosai Ummi ta hanata sukuni, tare da saka mata ido. Gefe daya suna rusa Nazzir da Mahaifin shi, duk wani abun da yake da saka hannu akai sai da Mahir ya mishi cunen yan sanda. Sannan yasa aka kama mishi Nazzir, ya duba zanen Dragonfly dake bayan shi, kafin ya kyale su.

        Duk da wannan faffutikar, zuciyar shi yana ga matar shi, wanda yake yawan mafarkinta cikin kuka da damuwa, ya matsu ya gama dasu Nazzir, ya baza niman matar shi. Kamar yadda yake ji a jikin shi tana cikin damuwa.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now