Sisterhood

1.6K 210 18
                                    

https://my.w.tt/i6E1Vi9ETbb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣8️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

   _Allah ya baki lafiya ubangiji ya da zakkar jiki ne Aisha Bagudu! Allah ya baki lafiya_

My Honey Fans ina alfahari da ku, musamman comments dinku.😍😘 Da masu daukar dumin mr kyam-kyam😜

~Sisterhood~
.......
"Noorh! Amma dole zaki sake jiki da Mr Nazzir, ba dan kome ba dan kawai ya samu ya shigar sake cikin mutanen da yake da kusanci da su, haka zai taimaka wajen shiga gurin ba tare da wani ya fahimta ba.
      Sannan wancan yar uwar naki, kiyi kokarin dakatar da ita domin tana gab da rasa darajar ta, idan haka ta faru. Ba lallai bane kome yazo da sauki amma idan kika shige jikin Nazzir ita zata kuɓuta domin Nazzir manemin mata ne na bugawa a jarida kafin ya ci nasara akanta kinyi nisa da ita, kema nasan zaki kub'uta, sabida Mr Mahir ba zai iya bari wani abu ya same ki ba."
    "Toh idan wani abu ya fito daga baya fa? Kai da kanka ka gaya min Mr Mahir bai da kirki idan wani abu ya hada mu da, ya kore ni."
"Ba zai tab'a faruwa ba, na gama shirya mana kome Insha Allah koda zan yi Survive na, am sure dat zaki kai labari, nasan zaki tsira Insha Allah." Kallon shi nayi sannan na lashe bakina, dai dai an buga kofar Shigowa.
   Mikewa nayi na isa bakin kofar, shi kuma ya mai da kome, sannan na bude kofar, wani irin kallo take bina dashi, tare da jan tsaki me ƙarfi. Bata hanya nayi. Sannan ta bangaje ni ta wuce,
Dariya nayi mata, me cike da tausayin ta, sannan na koma na hada takardun na saka a jakata, daurewa take kawai amma dan abu kadan kuka zai sakata.
              A hankali muka tashi tare da nufar gida, Ni Badar ne ya mai dani tare da bani wasu kayan aikin. Muna isowa Mr Nazzir yana isowa da Tasleem. Kanta na rawa, ta fito murmushi nayi ta sake min, sannan na nufi cikin gidan.
"A'isha Omar Jimeta!"
A hankali na juya ina kallon shi, cak ta tsaya itama, na isa har gurin shi. Murmushi muka sakewa juna, tare da cewa.
"Sir!"
"Noorh! Ina son magana dake, idan da hali."
"Gaskiya na dawo gida kenan, kuma ba zan iya dogon magana ba, kuma bani da lokacin da zan yi magana da kai."
   Murmushi yayi sannan yace.
"Toh ba damuwa, ranki shi dad'e. Idan da hali a bani lokacin da zan zo mu gana."
"Amma kamar akwai wani abu a tsakanin ku da Baby Queen?"
Na tambaye shi, murmushi yayi min sannan yace min.
"Am deeply sorry, babu soyayya."
"Aikuwa babu abinda zai hada ni da kai, kawai ka rabu da ni, karka ja min magana, don Allah ka rabu dani, idan kace abota zan yi da kai but babu batun soyayya, sai dai abota na yarda da haka. Shima sai na duba yanayin mu'amala da kai. Da kuma Baby Queen."
Daga haka na barshi tsaye, fuskar shi zaka kalla ka fahimci yaji yana cike da mamaki, sabida tunda yake babu macen da tab'ata nuna bata yin shi, asalima bai tab'a jin akwai ranar da mace zata ce bata yin soyayyar shi.
   Dan ya fahimci shi yakewa mata alfarma basu ke mishi ba, sai gashi once, A'isha Omar ta mishi kwarjini.
             Murmusawa yayi yana bin bayanta da Mayun idanun shi nan, ji yaƙe kamar ya dauke ta ya boye ta a gidan shi. Yarinyar ta yi mishi bazata, ta cika mishi ido.
     Kamata yayi ace ta kware akan harkan rayuwa, amma wani sirrin da yake hangowa cikin idanun ta, ya sanya shi jin shakkar ambaton soyayya a tsakanin su. Ina ba zai iya zama da ita ba, a matsayin abota ba, abinda zuciyar shi ke son dai itace tazo a matsayin matar auren shi haka zai bashi damar tafiya da ita yadda ya dace.
           Dakyar yaja kafar shi ya shiga motar shi, yana sake kallon yadda tasleem take tsaye, tare da kallon shi, bai damu da ita ba.
        Bayan fitar shi ta shiga cikin gidan, a haukace tana shiga ta hango Noorh tana haurawa step. Kafin ta iso step din ta zame, sakamakon zubewar ruwa, lokacin da me aikin su ta dauko daga sama dauke da kayan wankin da Mommy ta jika, aikuwa sai da ta bugu. Wani irin kuka tasaka, me mugun karfi ta kuma tashi da sauri ta haura sama.
... Tana shiga ta samu Noorh tana banɗaki shiga tayi tare da, niman rufeta da duka. Allah ya taimaka Bata cire kayanta ba, aikuwa suka kacame da dambe, Tasleem ta fadi ita kuma ta haura cikinta tayi ta dukarta, ihunta ya janyon hankalin Mommy.
               Tana zuwa ta sami Noorh bisa Tasleem, aikuwa ta rufe Noorh da duka, ita kuma ta Cigaba da dukar Tasleem sosai take dukarta, ganin zata kashe mata Ƴa kawai ta tureta da karfin tsiya, sai da ta fadi cikin zafin nama ta mike tana zubda yawun bakinta, sabida bakinta ya fashe.
    "Wayyo Allah na, Mommy ta kwace min shi, Mommy zata kashe ni, sai na kashe ki wallahi wayyo Allah na, na shiga uku na lalace."  Inji Tasleem,
Murmusa musu Noorh tayi sannan tace.
"Wallahi matukar baki daina haukar tab'a ni ba, toh ba zan daina dukarki ba."
"Yar iska, yar cin arziki ita da gidan Ubanta ki saka hannu ki daketa"
Kallon Mommy tayi sannan tace.
"Gidan ubana ne nima,.babu wanda ya isa ya kore ni."
"Ni zaki yiwa rashin kunya?" Cikin taurin kai tace.
"Koyarwarki ce ni, tunda na taso kika koya min kuma na haddace."
    Sake baki tayi, tana kallon Noorh.
"Idanunki sun bude ko? Kin saba da maza?"
"Bani ya dace ki gayawa haka ba,sai wacce take damuwa akan wanda bai san tana yi ba. Ni da ayi namiji kar  ayi shi, itace mayyar maza, wacce zuciyarta ta rayu saboda maza."
Daga haka na fito, daga bayin na zauna ina huci, tare da jiran me zata ce. Haka suka fita can sai ga Daddy, ya shigo da masifa, kallon shi nayi cikin kuka nace mishi.
"Tunda Na rasa kowa, kuka mai dani bare, baku da wani abu sai Yarki baku san kome ba sai Yarku a duniya babu abinda kuke boye akanta.
  .kunsan yadda nake ji? Kun rabani da  dangin Mahaifiyata, kun rike min dukiyata, ku bani hakkina da iyayena suka bar min, sai na fita a rayuwar Yarku."..
Daga haka ta shiga hada kayanta tana kuka, tare da cewa zata bar gidan ma ta huta,
   Shiru yayi sannan, ya fita ya rasa abinda zai ce, tabbas dole ya hakura da abinda yake shirin faruwa, domin tunda ta fara fad'ar haka, wata rana zata iya yunkurin sai ta karbi kayan ta. Shi kam ya gama barnata da kome.
           **
Ranar kwana akayi a gidan, babu wanda ya iya, cin abinci sabida wutar da Noorh ta kunna musu, washi gari, ko karyawa bata yi ba tabar musu abincin su.
Kafin Tasleem ta isa gurin aiki, sai da suka mata fada, tare da cewa karta kuskura tayi wani shirme da Noorh zata daketa, ko tayi wani abu da zai sanya tayi magana. Don Allah tayi shiru ta zuba mata ido. Zasu san abinda zasu yi da Noorh.

        ---
A gurin aiki kuwa, tsoron Allah da tsoron Noorh ya hana Tasleem yin wani abun Arzikin, asalima tsoron kar Noorh ta fusata ya saka ta ki sake jikin ta.
   Koda aka tashi tare da Mr Nazzir suka  dawo, domin shi ya kawo  Noorh har gida.

    Ba sannu ba madalla ta ficce daga motar, ta barshi rike da kayan shirmen shi, da ya kawo mata, ta shiga gidan. Fitowa Tasleem tayi tare da harde hannu a kirjinta, tana kallon Nazzir.
Har inda yake ya isa, sannan ta zauna a cikin motar,
"Me kake nufi? Meye nayi maka da nayi deserve abinda kake min? Ka rasa wacce zaka yi mu'amala da ita sai Yar uwata.
    Don Allah ka rufa min asiri, zan baka duk abinda kake bukata don Allah kayi hakuri kaji kaina."
Ta faɗa cikin kuka, tare da hade hannun ta, gwanin tausayi. Kallon ta yayi sannan yace mata.
"Toh me zan miki? Na biki na biki, baki fahimci ma'anar soyayyar mu ba, Ni ina miki so tsakani da Allah, da kika ki sake jikinki dani shi yasa nayi tunanin na tuntubi A'isha Omar."

   "Yanzun idan na baka kaina zaka soni?" Ta tambaye shi cikin kuka.
Wani irin murmushi yake me cike da nutsuwa, tabbas tarkon shi ya kama kurciya. Yarinyar da yake bukata, ta kawo kanta jan iska yayi tare da kai hannun shi wuyar shi.
"Ok! Ki gayawa Parent din ki, akwai gala a gurin aikin mu, kin shirya"

Cike da farin ciki ta bar gurin, ta iso cikin gidan. Tana kallon Noorh da take ta fama da aiki tare, cikin budar murya tace.
"Mommy daddy, kuzo kuji akwai event din da aka gayyace ni,Ni da Mr Nazzir Abu Aswad, yan bakin ciki Tabbas zaku mutu, Mommy an jima karfe takwas."

      Murmushi nayi tare da zuba musu. Idanu  domin na fahimci kwadayi ya dame su, ban tab'a jin tausayinta ba sai yanzun da na fahimci, sun gama lalata tarbiyyar yarinyar su. Ga baki daya sun zama sakarkaru.

        Haka ta shirya cikin wasu fitinanne gown, kan nan kuwa aka gyara shi, haka ta shigo da wani abu a cup tana sha, haka ta gama. Sannan ta dauki kayanta pursed din ta, bata kalle ni ba.

      Har zata fita nace mata.
"Tasleem! Karki yarda da Mr Nazzir, Samarin shaho ne. Karki yarda ya kai ki ya baro ki, Tasleem karki yarda kije inda Allah bai kai ki ba, Tasleem idan kika yi hakuri Allah zai baki abinda ya fi Nazzir.

    Don Allah don Allah karki yarda ki kai kanki daga hallaka."

"Ke wacece da zaki hanani, abinda nayi niyya ko Mommy da Daddy basu hanani ba, sai ke ke din banza ke din wofi.

   Mr Nazzir kuwa yanzun zamu fara soyayya dashi, banza mara zuciya. Idan ke yar halak ce karki kuma shiga harkata."

.daga haka ta fice abinta, tana fita na lallubi wata ta, na kira Badar ya turo min, Number Nazzir.

Ina sakawa, na kira shi..
"Kasan nace zamu yi abota da kai?
And karka yarda wani abu ya shiga tsakanin ku da Tasleem..idan kuwa ka bari har wani abu mara dadi ya shiga tsakanin ku, toh karka yi tsammanin zan tab'a kyale ka, ka bar min yar uwata."

   "Ok na barta, babu abinda zan mata," ya fadi haka cikin lalluma, lokacin tana gaban shi, kura mishi ido tayi cikin b'acin rai. Tace mishi.
"Me nene?"
"A'isha Omar wai kar na fita dake"
Rufe bakinta tayi sannan ta fashe da kuka, tana girgiza kai tare da juyawa zata fita ya fincikota ta zube a jikin shi ta sake wani irin kuka. Nan ya shiga rarrashin ta, tare da gaya mata magana masu laushi da dad'i.

     Yadda ita kanta bata san yaudarar ta yake ba, kafin wani lokaci har ya kashe mata jikinta, tana jan motar yayi ya nufi Hamoud Boualem Estate. Da ita.

   Gabaki daya hankalin Noorh ya tashi wani irin Fargaba tare da tashin hankali ya saka ta kasa magana, sai zirga-zirga take..kamar wacce tayi karya, zunzurutun tana gudun abinda zai faru da Tasleem, har kusan karfe goma, ta leko step taga babu kowa duk sun shige dakinsu. Wato basu damu da rayuwar yarinyar ba, takan su kawai suke "innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ya Allah protect Tasleem!"

Kiran wayar Mr nazzir tayi cikin tashin hankali tace.
"Please! Ka barta ta dawo gida, don Allah karka mata kome, bata san waye kai bane, don Allah."
Kashe wayar yayi tare da sake murmushin mugunta..
Yana cizon lips din shi yace.
"A'isha Omar, ke matar aurena ce. Ba zaki hanani abinda nayi niyya ba. Tasleem itace ta kawo kanta.....
Allah na dawo inji mai yawon duniya, ni kuma na kusan guduwa ba🤗 domin comments da vote yayi kasa...

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now