The Name

1.9K 216 30
                                    

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣6️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
#the name
Kar da wayarta yayi ne ya dakatar da ita d'aga nikkab din, ta dauka.
"Assalamu alaikum!"
"Kizo manager na son ganinki!"
"Ok!"
Ajiyar zuciya tayi sannan ta juya zuwa cikin Station din, tana shiga ta tsaya.
"Sir gani!"
Kallo daya yayi mata sannan ya had'iye yawu.
"Wato zunzurutun kokarin da kika yi ta kuma sawa za a d'aga darajar gidan tv nan, amma ga wani bincike da na samu, akan mutanen da Mr Mahir Yasaka aka kashe su! Sannan sun sha bada hujjar cewa ba kisan kai bane kashe kai ne! Har zuwa mutuwar Badar, am sorry!"

Ya faɗa sakamakon ganin yadda fuskarta ya kuma cikin jimami, tura mata yayi, sannan ya kuma kawo wani list yace.
"Wannan kuma mutane ne, da idan wani abu ya faru dasu ake koran su, babu kyakyawan sallama."
Wannan kuma mutanen da yake tozartawa ne, ba tare da sanin su ba, zai kore su babu sallama.
Noorh nasan zaki iya, amma maganar gaskiya, sai kin cire wannan nikkab ɗin da yake fuskar ki, da haka zaki iya ladabtar da Mr Mahir, a bisa tozarta ki da yayi."

Cikin farin ciki, ta zauna tare da cewa.
"Nagode yallabai, sannan kuma zanyi aikin da zai d'aga darajar Station dinka, sannan batun nikkab Insha Allah gobe zan fara zuwa babu shi."

"Yawwa akwai taron manema labarai da za ayi a kamfanin Hamoud Boualem, CEO zai gabatar da abinda ya kashe Badar, kuma ina ga wannan sune Hujjojin da zaki rike, Noorh sakamakon abinda kika yi, ta janyo miki nasara, sannan ki bani Acct Number ki, domin Mr Aysar Haladu yana bukatar ki fara mishi tallar kayan ruwan shi."
Dake bahaushe yace duk wanda ya rigaka kwana toh fa shi asubanci zai yi, sam Noorh bata san dalilin da Badar yace karta kuskura tayi magana ba! Saboda, sai da ya gama bincike ya fahimci akwai manyan mutane da suke buƙatar durkusar da Mahir da kamfanonin shi na kasar.

Abubuwa da ya bankado ya tura mata ta email din ta, dan ya yarda da ita sosai, sama da yadda ya yarda da kowa, shi yasa ya zaɓi ya bata aikin, sakamakon yadda take bata da hayaniya, kuma bata da rawan kai irin na Tasleem.

Murmushi Manager yayi sannan ya ce mata.
"Insha Allah zuwa yamma zaki fara ganin kuɗin aikinki." Godiya tayi sannan ta fita, fitowa wani matashi wanda ba zai wuce sa'ar Mahir ba ya fito yana murmushi.

"Yarinyar tayi aikin da ake bukata, kuma kamar yadda akan gaya min, akwai wasu abubuwan da ake bukata ne ta fito dashi, domin kafin mutuwar shi yayi waya da ita. Kuma itace tasan halin Mahir ita kadai zata iya tunzura shi ya aikata abinda nake buƙata, sauran kuma zamu ji dashi. Idan nace zan saka a mishi wani abu, Ni zan fadi domin ana tab'a shi hukumar tsaro zasu yi magana, amma idan na barshi aka sami fitinannen da ya shiga gaban shiga cikin al'amarin shi zai zama na duniya ta zuba mishi ido. Abu na farko da ta faɗa wallahi nasan ba haka bane! Mahir ba mazinaci bane domin na zauna dashi a Militry College 2003, sannan mun kuma haduwa a team na a Kashmir 2007. Kuma dukkan mu course yake hadamu.

Kawai nasarar shi nake son ta zama namu ni da Abokina, sauran da suke ƙoƙarin ganin bayan shi, sai su kara himma, Ni dai kamfanin shi nake son ya rufe."
Murmushi Manager yayi sannan yace masa.
"Ba kai kadai kake son ganin shi ya fadi ba, amma ka sani duk abinda zaku yi, ku tabbatar kun gama shi cikin kwanakin nan. Idan ya wuce haka wani abu ya biyo baya toh wallahi zaku iya fadawa matsala."

Sun jima suna tattaunawa, sannan suka yi sallama.
---
Duba takardun tayi lokacin da take cikin napep, kamar daga sama taji an daki napep din su, haka tayi ta tangal tangal, kafin Allah ya taimaka suka tsaya, Motar Mahir ta gani amma bashi bane.
Fitowa tayi tare da kallon mutanen da suka tsaya suka jajjanta musu.
"Wannan al'amarin ba su kyauta ba, Allah ya tsare ku."
"Wato dan yaga bai samu damar min kome ba, shine ya turo a kashe ni?"
"Kin san shi ne?"
"Mahir Hamoud Boualem CEO!"

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now