My wife...

1.8K 166 28
                                    

https://my.w.tt/S20XewskWcb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣5️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

      Zuɓewa yayi a kasa, ranshi na kara dugunzuma, wayar cajin laptop din shi ya ja da ƙarfi.

Ya nufi gidan Ummi cikin tafasasshen zuciya, yana shiga cikin gidan, sun zauna suna mai da yadda suka kori Noorh, ya shiga dukar su kamar hauka, ya gigice. Ya fita hankalin shi dukar su yake Hajiya da take d'akinta sai da ta fito, bai kulata ba.

Yana cikin wannan lamari, Allah ya kawo Ummi, rike Hannun shi tayi.
"Me yasa ba zaka nutsu ba!"
Bakin shi cike da iska, ya rasa yadda zai yi yace.
"Sun koreta? Ummi wallahi idan ban gan mata ta ba, Ummi tab'a kirjina, zuciyata kamar zata buga. Ji yadda yake bugawa.

      Ummi daga ranar da ta fara min rashin kunya naji Allah ya kawo min matar da nake so ne! Ummi Duk cikin matan da nake gani kowacce shakkar gaya min magana take, Ummi Har yau Noorh bata bude bakinta tace ina sonka ba Mahir. Ummi yaushe zan sami mace irinta? Macen da ta kalli idanunka ta gaya maka abinda yayi mata.

    .wasu suna son mace me kunya hakuri kawaici, Ni mace me zafi nake bukata, macen da zafin kanmu zai zama daya. Macen da babu wanda ya isa takata. Ummi yau sun koran mun mata na da cikin jikin ta, Ina laifin su bari ta haihu, amma basu yi wannan tunanin ba! Suka shirya min karya tare da kore min matar da nake so. Ummi bayn yarinyar da muka gamu a jirgin kasa, Ummi har yau ban kuma ganin me kama da ita ba, sai Noorh.

           Ummi dubu sau dubu, na kome da na mallaka, idan za a ce na zab'a dashi da Noorh zan zabi Noorh na bar kome, Ummi ba zan iya rabuwa da Noorh ba dan su, Amma Ummi idan kika ce na rabu da ita, zan iya hakuri da ita."
  Bata ce mishi kome ba, ta amshi bulalan ta wullar sannan ta wuce kitchen ta debi ruwa ta mika mishi ya sha, wani irin ajiyar zuciya yake saukewa a kai akai.

Da gudu ya nufi dakin Noorh na gidan, bai sami kome ba. Sai awarwaron Zinarin Ummi, jikin shi a sanyayye ya sauko,  kallon hannun shi Ummi tayi.
"Baba na,.a ina kasami wannan awarwaron?"
"Na mahaifiyar Noorh ce?"
Amsa tayi tare da juyawa zuwa sama, kallon inda take ajiye nata tayi, ta ciro su.. guda biyu,

A hankali abinda ya faru, shekaru goma sha biyu suka shiga dawo mata, da lokacin da ta cire a hannunta, ta mikawa Mahaifiyar Aisha. Wani irin sanyin tausayin yaran guda biyu ne ya dira a zuciyarta, yau itace ta rike! Toh ya batun wancan Aishan? Lokaci guda lissafin ya dagule mata.

      A hankali ta fito, tana kallon shi.
"A ina kasami Noorh har ta baka wannan awarwaron?"
A hankali gaya mata, kome jikin yan uwan shi mata, ya mutu.

Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, kukan da yake tarewa ne, ya fashe da shi, cikin muryan kuka ya d'ago kai yana bata labarin matsalar Noorh,
"Zata tafi kasar da bata san kowa ba, idan yawan jama'a ya cika mata idanu, ciwonta niman tashi yake, har kuna da bakin zaginta Mahaukaciya?

         Kunsan wacece Noorh? Toh ita din Jinin abdullah keluarga ce, itama jinin mu daya, mu jinin  Boualem ne ita kuma abdullah keluarga."
Yadda yake fadar asalin Noorh, sannan yace musu.
"Yayan Mahaifiyar ta, shine Shugaban sojojin ƙasar Algeria.  Noorh kaddarar muce ya kawo iyayenta. Amma Noorh mata ta ce! Jikar Sheikh Bin Abu Turab, ce fa"
    Yadda yake bayanin alaƙar su da nasabarsu da Noorh abin tausayi ne, tashi yayi cikin tashin hankali.
Ummi! Yau zan raba dukiyar mu kowa ya dauki nashi, amma bazan iya cigaba da kallon wadannan mutanen a matsayin yan uwana ba, sabida su na rasa mata na da cikin jikinta."
.daga haka ya saka kai zai fita.
"Kul! Naji ko na gani ka tab'a wani abu na amanar da Allah ya baka, babu yadda ka iya dasu. Amma idan ka barni da su Zan hukunta su dai dai da laifin su.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now