Dreams

1.7K 175 16
                                    

https://my.w.tt/r1iGAQFv1bb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣0️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

    KU TAYA MU ADDU'A JIKAR KULU da A'ISHAH BAGUDU ba lafiya Ubangiji ya basu lafiya 🙏🏼 😢

#Dreams

Sosai yake kallonta, yana niman makusa a tare da ita, bai samu ba dan haka ya bar gidan yana biye dashi kamar bindin shi, bai ce mata kome ba, ya nufi Mansion din shi, tun ko ta kanta bai bi ba, bai kuma damu da ya mata magana ba, sai da suka isa ya kira Haroon ya gaya mishi ya sake Dolna.

       Aikuwa suna shiga ya sake gidan, karen ya tawo da mugun gudu, bai damu ba yace mishi.
"Kamo min kafarta."
.wato da karen nan ya saka ta a gaba, tana ihu tana kuka tare da Rokon shi.
"Ba zaki gane ba, sai ya yanke miki kafa."
"Don Allah kayi hakuri."
Abinda take fada kenan, tare da niman ya taimaka mata, Haroon ne ya bude mata kofar,
Da kuka ta isa gidan. Jikinta yana rawa, zama yayi. Dariya yake yana tuno abinda yayi sai ya tsane mace babu kamun kai, shi yasa wani wata zai gudu Yola ko zai huta da Jarabar matan zamani.

Da ta isa gidan Ummin da gudu ta isa jikin Mahaifiyar ta, tana kuka tare da labarta musu abinda ya faru, dariya Alishbah tayi sannan tace mata.
"Ai wallahi tunda kika ga haka, gwara ki rabu dashi. Har baki ji ba ki godewa Allah da Haroon yake gidan, da baya nan haka zai shige yayi kwanciyar shi, kawai ki rabu da shi."

   Ran Mahaifiyarta ya b'aci sosai, dan haka ta riko hannun ta suka bar gidan, bai shigo ba sai bayan la'asar, yana shigowa Ummi tace mishi.
"Allah ya shirya min kai. Ka hada ni da Kawata!" Ta faɗa a hankali.
Zama yayi yana kallon karatun da Dr Ibrahim Khalil yake  a sunnah tv, lumshe idanun shi yayi haka kawai yau yake jin bugun zuciyar shi tana fin na kullum.

     Kwanciya yayi tare da dafe goshinsa, yana sauke ajiyar zuciya. Har barci ya dauke ta.

      "Wayyo Ammih na!" Na fada da karfi bai ga fuskar ta ba, amma yana jin lokacin da matar tace mishi.
"Don Allah ka dauko min Yarinya ta, gata can Ai...."
Karar da jirgin yayi ya sanya wani abu ya buge mishi kanshi yayi da ya fad'i, kasa ita kuma matar karfe ya fasa mata kanta.

"Wayyo Allah na! Ammihhhhhhh"
A firgice ya farkaz tare da niman kwacewa zai fita da gudu,Ummi ta danne shi, tana tofa mishi Addu'a. Ita ta fara gajiya da wannan matsalar Mahir, dole zata mai dashi asibitin da ake kula da lafiyar ƙwaƙwalwar shi, dan ya kwana biyu bai je an duba shi ba, kuma da alamun mafarkin nan yana nan tare dashi ko kuma yawan takura mishi da maganar aure ne ya sanya yake yawan jin haka oho, tunda ta samu ya sauke ajiyar zuciya, tare da daura kan shi akan cinyarta, yana lumshe idanun shi, alamar ya samu nutsiwa kenan.
   ••
Iskanci Tasleem bai ajiyeta a guri daya ba, Ni basa gaba na. Kawai abin da na sani, shine Allah ya bani sa'a na samu wata hanyar da zai kai yi wancan part din ba kome bane, dai wani riga ne da ake sakawa, dan haka nayi amfani da rigar na samu shiga bangaren, cikin ikon Allah na samu damar leko abinda suke ta hanyar nadewa a wani ƙaramin Camera.
      Tunda na gama na fito, ban kuma komawa ba, na turawa Badar. Take shima ya tura ma'aikatar su.
    Washi gari mun zo aka taramu wai Mr Nazzir zai yi magana.
  Lokacin da ya fara jawabinsa. Ina sauraron shi, jin abinda ya faɗa muka kalli juna a razane.
"Da alamu akwai yan leken asiri, sun shigo cikin gidan nan.
      Toh ba wani abu bane da zaran kuma kama su, toh zamu mika su ga jami'an tsaron, dan haka kowa ya shiga hankalin shi, kuma ku nutsu kuyi abinda ya kawo ku, matukar muka kama wani toh bamu bazamu yi kuka da kan mu ba, amma shi yayi kuka da abinda zai faru.
Karku damu ba barazana bane, tunatar wa ne."

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now