She take my position

1.9K 177 33
                                    

https://my.w.tt/aRlDAIh8Dbb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣4️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu
I have many problems in my life...But my lips don't know that' they always smile..

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~#shetakemyposition~

      "Kun fahimce ni?" Ya tambaya cikin dakakkiyar murya.
"Yes sir"
Duk muka amsa, har zai wuce ya juyo tare da kallona, yace min.
"Are you ok?" Jinjina mishi kai nayi, ina kallon yadda Tasleem take harara na, ya sa kai zai fita. Yace.
"Tasleem Elhussain Jimeta, ina jiran ki" sai nan naga fuskarta a sake, tabi bayan shi, har office din shi, tunda ya bar gurin matan suka shiga kananun magana, ina jin su ban kula su ba. Hayaniya ce bana so a rayuwata. Shi yasa nayi banza dasu.  Zuwan Badar ya sani mik'ewa muka fito, zuwa inda zamu zauna. Kallona yayi sannan yayi magana kasa kasa.

"Noorh! Ki tsare kimarki, karki yarda da MD, ki kame kanki. Please karki zama balagazza shaddar kasuwa, ki zame macen da ke namiji zai bi ba kece zaki bishi ba don Allah, wallahi kallon kanwata nake miki."
Gyad'a mishi kai nayi tare da cewa. "Insha Allah zanyi yadda kace" yadda nayi maganar ne ya bashi dariya a dan tsorace.
"Karki damu, babu abinda zai faru" daga haka ya shiga min bayanin yadda kome yake tafiya a Office din shi yace min. "CEO baya nan, yana kasar Qatar, akan kasuwancin shi na man fetur, sannan wannan kamfanin about mutane dubu goma suke aiki a cikin shi, sannan akwai leburori masu kananun aiki. Mr Mahir bai da matslar kome, sai dai bai da dadin zama, har gwara MD akan shi. Sabida matukar yana nan toh wallahi kullum sai yayi kora.
              Yana karban gyara amma banda na mace, matukar zaki mishi gyara koran ki."
       "Ya Badr gyara koran su zai yi, domin babu abinda ya dame ni dashi" na fadi haka a sanyayye, kallona yayi sannan yace. "Toh naji koran su zai yi!"

Nan muka Cigaba da hidimar aikin.
         ★
   "Da nace karki kuma mata magana shine kika mata."  Ya cire rigar shi, tare da zama a kujera yana balle cire suit din jikin shi yayi, sannan ya shiga zare neck tie din shi, ya kalle ta tare da kiran ta da hannu. "Ki min tausa"
Wani irin girma kanta yayi tare da wani bada sauti na musamman, yau ita ce zata yiwa daya daga cikin young billionaire boys na naija. Jin wani irin karsashi ya shigeta, a hankali ta isa bayan shi, tare da fara mishi tausa, a sannu a hankali. Take mishi, yana aiki tare da lumshe idanun shi. Karar wayar shi tayi wacce take saman table din Office din, ya kai hannun shi ya d'auka.
         Lion Man! Ya gani, murmushi ya sake sannan ya kunna tare da sakawa a amsa kuwa.
"Barka dai Lion!"
"Tiger!" Ya kira sunan cikin wata irin kasalalliyar murya, juyawa yayi ya kalli Tasleem, da sauri ta tashi ta koma daya daga cikin kujerun cikin office din, ta zauna wasu gray colour, ta daura daya akan daya.
"Lion! Kana bukatar wani abu ne?"
         Shiru yayi, yaki bashi amsa. Sai da ya kuma maimaita abinda yace sau uku kafin yace mishi.
"Please ka daina min ihu,"

       "Ok what do u need? Ko kana bukatar zafaffan Yan mata zasu jiyar da kai dad'i." Wani irin iska yaja tare da yaji, sannan yace.
"No need, yan bautar ƙasan sun iso ko? And ka zab'a min daya a cikin su.  Wanda zai taimaka min da aiki Insha Allah ina hanya kowani lokaci."

       "Ok boss!"
Karamin tsaki yaja, jin ya kira shi da boss. Yana kashe wayar ya kalli Tasleem, yaga itace ta dace da Office din Mr Mahir, murmushi yayi sannan yace." Hey" da sauri ta mike tare da isa gurin shi, ta Cigaba da aikin, yana wani juyar da wuyar shi

         Zuwa gabanta yayi tare da zuba hannun shi duk biyu a aljuhun wandon shi.
"Zaki iya aiki da kuwa, akwai brother na, da zai dawo dan haka ki nutsu karki janyo ya kore ki "

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now