Other side

1.8K 198 42
                                    

https://www.wattpad.com/1010638382?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=t2vwVWQ6R91YNEa2KNee5i420PyN1JrEhumbRRqCRdz5YTOoQL1ZJLcrISZd7lMQcvWlnV4CA9a9pOvRLjzx5TfDagW0gPV2qQkotFhqHb6BOKq1Bu9MEnMI16fJUADn

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣7️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

_Alhamdulillahi nagode sosai, daga duk inda kuke ina mikawa Fans din Mahnoor gaisuwa na Nagode da addu'o'in ku_

  *Ina mika sakon ta'aziya ga Aunty Mami wacce tayi rashin yar uwarta, tare da Maman Sultan wanda ta rasa mahaifinta, Allah ya jikan rai ya kuma gafarta musu, ya kyautatta namu bayan su*
"Ummi don Allah ki rufa min asiri, wallahi zuciyata zata buga, nayi iya hakurin da zanyin please i need my wife" banza tayi dashi, ta cigaba da aikin ta,kamar bata san da abinda yake rokonta ba.

    "Amma Maryam!"
"Hajiya don Allah karki saka baki akan wannan al'amarin, Ki kyale ni da MUH'D!" Ummi ta katse Hajiya,
Shiru tayi tana kallon yadda Mahir ya tara kasumba da uwar gemu.
"Kai dalla can, tashi kaje ka gyara kanka, ka wani zauna buzu buzu da kai sai kace me cutar hauka!"
Inji Hajiya, "Hajiya nifa ba zanje ko ina ba, kawai Ummi ta gaya min meye nufinta da aurena da Noor?"

Cak ta tsaya da aikin da take a kan laptop, ta juya tana kallon shi, bata ce mishi kome ba, ta juya tare da wurga mishi takardan.
"Ka aureta ba bisa son ranta ba, kayi ta amfani da ita ba bisa ka'ida ba."
"Yanzun Ummi Noorh dince ta gaya miki haka?"
Dakuwa tayi mishi, da hannu bibbiyu, tare da mishi alamar da yana kusa sai ta watsa mishi mari.
"Kaniyarka, da zaka zo kusadani sai na maka shegen duka, meye ba zata fada ba, kasan irin kukan da take yi idan ta tuna ta rasa duk wani abinda akewa yar gata sabida rashin hankalin da kayi mata?

           Kasan dalilin da yasa tayi ta maka borin bata son zaman nan, tunda taji labarin wacce aka yi aurenku tun farko, tuni kishin ka ya gama turmusheta, mara kirkin mutum kawai, yarinyar nan haka ka aureta ko dan irin abubuwan al'ada babu, ka gama rena mata hankali, da cewa mafarki take, toh Wallahi ta gaya min rabuwa zaka yi da ita na gaya maka."

       Mikewa yayi cikin jin haushi da b'acin rai ya ki kula takardan da zai saka hannu, ya saki Noorh.
"Wallahi indai ana daura igiyar aure sau dubu, toh na kuma damke auren Noorh akaina, naga wanda zai yi wannan aikin amma ba dai ni ba!"

Ya juya fuuuuu, kamar zai yi hauka sabida yana matukar son matar shi, kuma baya jin zai iya sake ta.

    Kallon ta Hajiya tayi, tare da cewa.
"Nasan yadda yarinyar ta koma gurin yan uwanmu, toh wallahi ina tausaya mishi, domin matukar ta isa hannun Hajiya Dadah toh wallahi ina tausaya MUH'D don kuwa."

    "Hajiya na fahimci haka shi yasa nake kokarin na koya mishi, yadda zai jure abinda zai biyo baya, domin bana manta lokacin da Ubaidullah yayi faɗa da Su'ada, yadda kowa ya juya mishi baya, gasu yanzun har da Yarinyar da ake shirin aurar da ita Dr Naaz, kuma ban san Baban Noorh ba sai shi kawai na sani da Abubakar da Dr Hisham Abdullahi keluarga."

    "Kin san Umar yaki zaman algeria ne, aiki da china da kuma turawa ya hana shi zama, rabon Noorh da yan uwanta ya dawo dashi daga china koda aka yi auren haka ya tafi ya barta, sai da yayi shekara biyu ya dawo ya tafi da ita,  ita tanka zo duba dangi, Kinga yaje algeria kenan yazo nigeria, dan shi Dr Abdullahi keluarga yaki ya bar yaran shi anan Nigeria, itama Dada da take yar Nigeria yaki barinta zuwa akai akai, kakan wancan Yarinyar masu shegen son abun duniya suka zauna anan din." Ta wani bi gefenta da harara, zaka zata Tasleem din tana gurin ne zunzurutun tsanar da tayiwa Tasleem din ne kawai.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now