Faruq

1.6K 177 42
                                    

https://www.wattpad.com/1012619907?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=%2F3Psbc8CzWLIt7nhOc%2Fefbq6TGO%2FoqXkdLl3tWqojpTg2slpkg41f2y3BNyNBTybBTJuuTrS0AdI0DareqPNPHmvNiA4X%2BuxvowSA2Z7n4iZx0w6%2BJj7HrArcFk40LE%2F

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣9️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

   Zama tayi a gaban Noorh cikin tsananin kaunar Jikarta, ji take kamar tana barin gurin zata samu mugun labarin an sace ta,shi yasa da Yaranta suka nemi ta koma gida wani irin kallo tayi musu cikin balokoko take kallon su, tab'e baki tayi sannan tace.
"Wato nayi saki reshe ku kama min ganye? Na tafi ku aiko min da cewa ƙaddara ce ta sani tafiya shine tafi ta baku sani ba, ko ba haka ba?"

   Duk suka yi shiru, kafin ta gyada kai sannan yace musu.
"Toh bani zuwa ko ina sai naga yanayin jikin nata, idan kuma a kanku nake zaku iya dauka ta cak ku kai ni gida."

     Shiru suka yi, tare da sunkuyar da kansu, dan sun san tunda Dadah tace babu inda zata ko zasu mutu su dawo ba zata je ko ina ba.

     .....
Allah ya azurtata da yara bakwai, maza hudu mata uku.
Dr Hisham, Dr Ubaidullahi, Dr Abubakar, sannan Baban Noorh, Asiyah, Mariya, sai Ma'idah tana aure a gidan su Maman Noorh, tana auren General Adam Yaqub Wazir,

      Wato asalin familyn baki daya auren zumunta ne, Dr Hisham.

Yana auren Babbar Yayar Maman Noorh, wato Maisarah mahaifiyar Faruq, sannan  Ubaidullahi yana auren Yar Kanwar Hajiya Kakar Mahir, Su'adat.

            Ita kuma Mariyah tana auren Kawun Mahir kanin Baban shi, da suke Uba daya, Asiyah tana auren, Controller custom, Mr Abdul Fatah. Cousins Brother Maman Noorh ne, Kanwar shi me suna Siyamah ita Abubakar yake aure, Salha Maman Noorh kuma baban Noorh aka hada su, ita yar Nana ce, domin da ita da Maman Faruq da Maman Naaz Su'adat, duk Nana ce ta haife su. Su hudu Allah ya bata yaran.

Dan haka suma kuma yaran su auren zumunta aka musu. A halin yanzun kuma wanda yake kawo musu matsala a cikin gidan Shine Faruq dan.tunda aka mishi baiko da Naaz yace baya sonta kuma da suna mutunci sosai.

Tunda batun aure ya shigo ne, duk suka tsani junan su, sannan itama Naaz akwai wanda take so, mahaifin shi yana daya daga cikin manyan yan kasuwan ƙasar.

           ----
A hankali take bude idanunta, tare da bin ko ina da kallo, wani dan banzan juyi da cikinta yayi yasata ware idanun ta, akan matar da take sallah.
"Masha Allah! Sannu yar nan? Yunwa kike ji ko?"
Tashi tayi daga abin sallah, sannan ta juya zuwa ban daki ta haɗa mata ruwan wanka, tazo ta cire mata karin ruwan (☹️🤔)

     Ta rike ta, ita Noorh ta mata kallon tausayi dan taga ta manyanta, ita kuma tana wa Noorh kallon tausayin ba zata iya kome ba. Dan haka suka shiga ban dakin da kanta, ta shiga taimakawa Noorh ta cire kayanta, tayi mata wanka sosai. Sannan ta fito da wata ƙatuwar towel ta kawo mata, da hijab kanta kuwa ta wanke shi kamar ba shine a curkude ba, sannan suka fito bayan ta duba kafarta, ta gyara mata zaman bandajin.

       Tunda suka fito, ta shimfid'a mata abin sallah, ta bata doguwar riga ta saka, sannan tace mata.
"Zaki yi sallar ko zaki fara cin abincin?"

Wani irin kuka ne yazo mata, ta zauna a bakin gadon.
"Duk abinda akace nayi zanyi."
Bata ruwan zafi tayi ta fara sha, tana idarwa ta koma ta dauko kwano a cikin ban daki ta bawa Noorh ruwa ta wanke bakinta, sannan ta umarce ta, da tayi sallah.
......
A hankali dakin ya fara cika, tana idar da Sallah ta juya tana kallon su, a hankali ta koma bayan Dadah ta kifa kanta, tana share kwalla.
"Beauty! Fito babu abinda zamu miki, ga Nanah ma tana shigowa."
Inji Faruq, tana kallon su baki daya kamar ta sansu amma ba zata ce ga inda ta tab'a ganin su ba,  shigowar kakanta da kuma Maman Naaz, tare da Maman Faruq, yasata kafe su da ido. A hankali ta mike tare da mika musu hannu, kafin su isa inda take ta nime zubewa a gurin. Da kiran.
"Ammyna!"

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now