Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem

1.9K 170 40
                                    

https://www.wattpad.com/1013548378?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=%2BSwzoldpHIsFz6f9CzoxUoZyR1bP5QymltbYeweCJaVs7z5akK5RVV2Cr1gqyAUT2bWZrW9C85rSEa3d%2Fqau96alqTfkicdyKiEm1wiN0OU0O3MKyiMSk%2FcrABJvdK3B
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 4️⃣1️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

Tunda Faruq ya bar algers,Mahir ya sake mik'e kafa suka ci-gaba gurgure juna, hankalin su kwance ga Dadah da ta tsaya mishi, wato mugu irin Mahir babu na biyun shi, a siyasance ya haɗa hada Dadah da kayan kawa na rayuwa, kuma idan zai zauna sau dari da ita sai ya nuna mata ai tafi Noorh kyau da kuruciyar.

Haka yayi matukar tasiri a ranta, dan haka cikin ruwan sanyi yayi ta lallabata har tasaka lokacin komawa Noorh dakin mijinta.

Sai dai yan uwan Babanta sun kuma niman Alfarmar ta haihu sai ta koma d'akinta, haka Ummi ta sanya shi dole ya bar ƙasar domin tasan matukar yana kasar ba zai tab'a barin yarinyar ta samu kulawar da ake bukata ba, domin Aunty Mariya sun tattauna da Ummi akan lafiyar ƙwaƙwalwar ta, kuma itama tayi na'am da abinda tace.
"Insha Allah zai barta ta samu sauki ba zai zauna a kasar ba ma balle ya kawo muku matsala."

Gaskiya Ummi Uwa ce, domin tsayawa tayi ka'in da na'in, ta tabbatar da Mahir ya bar kasar, sannan ta kwantar da hankalin domin ciwon Noorh din ana son mata jinyar shi na gaske yadda zai taimaka lafiyarta ta dawo, dan haka suka yi nazarin abinda ya dace da lafiyarta aka fara saka lokacin da za a cire Babyn cikinta,

.... Bayan watanni uku da kwanaki, aka mata aiki inda suka ciro yara uku kyakyawa masu kama da Baban su, musamman matan biyu namiji ɗaya, shine ya dauko Noorh, hoton su Ummi ta tura Mishi, kamar zai yi hauka daya gansu.

Haka kuma ta hana shi zuwa, zama yayi a gaban abokan shi yayi ta zabga murmushin jin dadi, yana gaya musu matar shi ta haihu yara uku.

----
After few days.

Aka fara daura Noorh akan magani, dama sabida drugs ne yasa suka mata aiki aka cire babyns ɗinta, a hankali lafiyar ya fara shigarta, har ta fara fahimtar ta haihu, amma nutsuwar da take samu ya hanata magana, sai da tayi sati Uku sannan aka kawo mata yaranta, idan kaganta sai ka zubda kwalla sani anyi mata aski an kwashe gashin kanta tass, sai yar robon bututun hancin.

Lokacin da Dadah ta ganta tayi kuka ta tausaya mata, balle Kuma Nanah cewa take.
"Mariyah Maisarah Don Allah kar na rasa A'isha kamar yadda na rasa Salha."

Matukar kana da imani inda ka ga yadda suke kuka sai ka zubda kwalla, haka tayi ta murmushi tana kallon su, musamman yaranta.

A cikin kwanakin ne Allah ya tunkud'o Mahir, lokacin da ya ganta kuka yake, tare da rungume ta. Juyawa yayi ya kalli Dr Naaz.
"Meke damun Noorh!"
"Ba wani abu bane ciwon dake brain ɗinta ne, yake son shiga matakin Cancer, shine aka mata aiki aka cire Yaran kagan su ko suna ba asamu su ba."

Rungume shi tayi tare da kifa kanta a kirjin.
"Mahir"
"Shiii!"
Shafa kwal-kwal din kanta yayi, hawaye na sauka a idanun shi.
"Baby I love you!"
Kuka ne ya kwace mata,
"Honey me too!"
"Iyayen su da suke kallon su ta window glass sai da suka zubda kwalla."
Haka yana ji yana gani aka fitar da ita zuwa dakin da za ayi mata aikin ƙarshe.

Ko kallon yaran ya kasa, zaman dirshan yayi a bakin kofar aikin, yana kuka da duk zuciyar shi.

Lokacin da Faruq yaga yadda Mahir ya koma,.sai da yayi kuka domin bai tab'a tsammanin.son da sukewa juna ya kai haka ba.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now