MR Arrogant

1.9K 183 28
                                    

https://t.me/joinchat/IQpnHR2pz0-DVPLh9lzhWQ

Shafin Telegram dina zaku iya samun shi Daga farko...
MAH~NOOR
My First Wife♡
        Chapter 1️⃣2️⃣
     MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM
Ga
#Mr Arrogant

Wani irin kunya ce ya kama ta,ta kalle ni kamar zata yi kuka, tace min.
"Noorh! Kinji abinda yake gaya min"
Kallon shi nayi tare da cewa.
"Gaskiya wannan abin bai dace ba, kuma kar a kuma."

"Hmm!" Ya ce mana, tare da juya keya,
     Nan muka shiga hidmar gaban mu.
     ••
"Lion Man! Dama akan gurbattacen lemon nan ne, ko zaka saka hannu." 
Hannun shi rike da wata mug, ya juya musu baya, daya hannun shi kuma a cikin aljuhun wandon shi, yana kurb'an coffee a hankali kamar baya son sha.

          Ajiyewa yayi a kan wani table,inda Coffee machine yake.
"Ba zan saka ba!"
"Amma kuma Lion!"
"Bana Crossing limit! Kuma kasan waye ni? Kuma kasan abinda nake yi da wanda bana yi, ba zan saka muku hannu ba, sai naji me zaku yi da gurbattacen lemon."
        Cikin inda-inda Nazzir yace..
"Babu kome fa, domin zubda shi ake."
"Better! Kasan ina da Opinions akan abinda yaƙe gabana."

        Shiru yayi tare da ɗaukar mug din shi ya cigaba da kurb'an coffee din shi, yana kallon yadda suka b'ata fuska.
"Tiger! Ya naga ranka ya b'aci? Ko akwai abinda na rushe muku ne?"

"A'a wallahi! Kawai dai gani nayi kamar aka samu saka hannunka akan kome, za a samu cikakkiyar nasarar da ake bukata." Ya faɗa a sanyayye.
" Toh kasa hannun mana, ai kane wakilin Kamfanin, ni ban zo zama bane har yanzun."

    Ya fadi haka yana murmushi, tare da kallon su.
"Lion!"
"It's about business matter! Babu abinda ya dame ni nazo holiday ne kuma kuna fara damuna zan gudu inda na fito. Dan haka ni ba, kuyi duk abinda yayi muku."

   Ya fadi haka, tare da nufar Hanyar waje, yana rike da mug. Ya nufi cikin kamfanin, tafiya yake tare da nazarin abinda Nazzir yazo mishi da shi.
      Kan shi a kan cup din da yake hannun shi, bai san lokacin da ya sake hanyar shi ba. Sai dai da ya hango wata mace tana daukar abu, tare da leke. Da sauri ya isa gurin.

A tunaninta Nazzir ne, dan haka cikin wani irin sauri tazo zata bangaje shi ya fisgota, ji yayi kamar an jona mishi lantarki, da sauri ya saketa, tare da  kallon fuskarta wanda yaƙe cikin niffab, sake ta yayi tare da kai hannum shi zai cire abin fiskarta, zuciyarshi tana wani irin bugawa.
     
     Exactly itama abinda take ji kenan, kurawa juna ido suka yi lallai ala dole suke san tuna lokacin da ya shude. Hannun shi ya kai a karo na biyu, ta buge hannun shi tare da saka hannun ta dukkan biyu ta ture shi. Yana tsaye akan kafar shi, sai mug din hannun shi da ya zube a Whiter hijab din ta, cikin takaici ta kalle.
      Dariya ta bashi yayi wani karamin murmushi sannan ya kuma takowa gaban ta, zai cire nikaff. Da bangaje shi sai da ya jingina da bango, da zura da gudu, ya kai hannun shi ya riko wuyar hannun, warwaron azurfa ta wanda na mahaifiyarta ne haka ya zare a hannunta.  Ya fadi durkusawa tayi zata dauka ya taka hannunta tare da dauke kan shi.

     "Kai wani irin mugu ne? Zaka kashe ni ne?" Ta faɗa muryan ta na rawa, san ko a jikin kamar ma irin bada shi take ba, sake take hannun yayi tare durkusawa gabanta, yana kallon yadda Eyelashe ɗinta suka jike alamar zata sake kuka. Murmushin mugunta yayi sannan ya d'aga kafar shi akan hannunta da suka yi jajjur. Ya mike abin shi.
   Ya bar gurinta, juyawa yayi cikin jin haushi tace mishi.
"Mugun banza kawai! Kuma sai na saka Nazzir ya kore ka. Dube shi me kama da yara ƙanana."
. Cak ya tsaya tare da juyawa yana kallonta, kawai yayi tafiyar shi amma dole yaci kaniyar wannan me dodon fuskar nan.

MAH~NOOR🌹On viuen les histories. Descobreix ara