You are my Destiny

1.9K 171 19
                                    

https://my.w.tt/WNKRxS2oKcb

MAH~NOOR✧✧
   My First Wife♡
        Chapter 2️⃣6️⃣
     MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

  Riko hannun ta yayi tare da rungumo ta, jikin shi yana jan kumatunta, tare da cewa.
"Ke ƙaddara ta ce! Kece zanen ƙaddara ta ce, kece abinda na jima ina nima, Noorh don Allah karki juya min baya, karki guje ni.
      Na shirya miki rayuwa domin ki dani, Noorh ina son na baki mamaki a rayuwarki."

  Kura mishi ido tayi, tare da kallon yadda bakin shi yake moi- moi.
Jan kumatunta yayi, itama taja nashi. Wannan abun ya bata dariya ganin yadda take goga Hancin shi akan goshinta, tana dariya a nan suka lalace ya biye mata suka yi ta shirme.

       .... A cikin watanin da suka yi ba karamin wahala ya sha da Noorh ba, domin tsakaninta da Allah take wajiga shi, gashi matukar ta gama period ɗinta, toh wallahi sai ya bata maganin barci, domin wata irin fitinanniya take zama, har sai da ya kai ta taga likita, anan yake gaya mishi sabida bata da hankali ne, bai zama dole ta sarrafa kanta ba, sai yadda zuciyarta tai da ita, sosai yake tausaya mata, a hankali yake aikin shi tare da taimakawar Usman Kamfut, yana bashi taimako sosai, domin yana kan aiki akan Manager da Aysar Haladu.

    .... Bayan wata Shida, suka kuma tattarawa, suka koma, Canada inda aka fara aiki. A lokacin banda Shibha babu wanda Mahir ya gayawa, amma zuciyar shi bata fada kiran Allah ba, zunzurutun yana dame da aikin har Saudiyya ya kaita suka yi Umra, sanan suka wuce Canada. Yana masalaci aka fito da ita, baya nan. Sai bayan mintinan goma ya shigo asibitin sanye da ash jalabiya sai yar hular da ya saka, wato malam tab'a ni kasha hadisi, hannun shi rike da yar karamar calbi, yana tafe yana azkr. Har ya isa yana zuwa yaga babu alamar ana aikin.
Raba ido ya shiga yi, kafin yaga nurse din da suka shiga mata aiki, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya shiga cikin dakin ya samu an samata ruwa da alluran barci, zama yayi a dakin har dare,sunyi juyin duniyar nan ya koma masaukin shi yaki.

      Har asuba yana zaune sai dai hada kanshi da gadon da yayi, tare da bashi, sanyin asuba ya sashi mik'ewa ya nufi ban daki, yayi alola sannan ya tafi Matsala.

     Bayan awa biyu, ya wuce bata farka na wani biyun ya kuma wuccewa,tana barci sai da ta kwana biyu, kafin ta fara ganin abubuwa kamar mafarki, tun daga ranar da suka baro wata ƙasa da mahaifanta da kanenta, sai, tare da lokacin da wani mugun abu ya fara,  a hankali har rayuwar da suka yi da Mahir, kuka take tare da niman zata mike, kuka take tana cewa.
"Ammyn na, Abbina." Tuno abinda ya faru lokaci guda, ba karamin dad'i yake dashi ba, sai dai a duk lokacin da ta tuna Mahir fuskarta ne yake nuna alamar jin haushin. Sai da ta gama dawowa hankalinta, sannan ta farka da kuka. likitan da yayi aiki ne ya tsaya akanta,har ya tabbatar ta koma barci, shiru Mahir yayi yana matukar jin shakkar farkawar ta,.

      Domin yana jin. Sai da tayi awa biyar kafin ta farka. Cikin yatsin fuska, take kallon dakin a hankali, dafe goshina nayi tare da watsa idanuna a ko ina, ganin shi nayi ya kafe ni da idanun shi. Murguda mishi baki nayi tare da fauce hannun na da ya rike, ina me b'ata rai.
"Sannu masifatu!"
Wani banzan kallo na watsa mishi, tare da juyar da kaina. Zan miki.
"Ki tsaya a cire miki."
"Ka ga Malam karka dame ni, wai meye matsalarka da ni ne? Meye hadinka dani ne? Don Allah ka fita a rayuwata."

      A hankali kirjin shi yake bugawa, yana fadin shikenan. Ta manta abinda ya faru, Noorh ta dawo.
"Ke bana son hauka, dalla ki koma ki kwanta, ko na matse ki."
Ya mike da tare da nad'e hannun rigarshi.
"Ni bana son Iskanci, karka yarda ka saka kazamin hannunka a jikina."
.cike da Mamaki yake kallon ta, yadda tayi maganar hankalin ta kwance.
Janye rigarta yayi sama, ta kai mishi duka, a hannun shi bakinta  bai fasa faɗin.
"Allah ya isa min mugu dan is.."
Make mata bakin ta yayi, cikin jin haushi tace mishi.
"Allah ya isa Azzalumin."
Yaji haushin sosai, ya kuma buge  mata hannun ta da bakin ta. Idanunta sun yi jajjur, tana son yin kuka, amma tsabar taurin kai ya hanata tayi kuka sai zunzurutun rashin kunya.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now