Interview

1.6K 226 27
                                    

https://my.w.tt/oCPVBn764bb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣1️⃣
MrsUsmaa400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM
#Interview
Idanun  shi lumshe yayi cikin nutsuwa, yana jin wani irin yanayi yana shigar shi, ba zai ce na Meye ba. Ganin bai da hujjar sawa kanshi damuwa yasa shi bude shanyayyun idanun shi masu kama da wanda ya kwankwadi kayan maye.

                A nutse ya dauki tap din shi ya shiga nazarin abinda zai kai shi Yola, tare da jin a ranshi koda ya isa yana bukatar yaji wani irin yanayi kamfanin su yake ciki. Kuma ya kome yake tafiya mishi.

      •••
"Wai Noor me ya sa kike haka ne? Don Allah ki tashi muje kinji. Yau baki daya baki da kuzari!"
   
       "Baby Queen! Jiki na ne babu dad'i, kawai kije ni ba zan sami zuwa ba kuma ki gayawa Badar."
  Kura mata ido tayi sannan itama ta koma bakin gadon ta zauna tare da cire yar karamar fashion hijab ɗinta, ta zauna tana kallon Noorh din.
"Ok nima na fasa zuwa."

"Don Allah tashi kin san yau mr Mahir zai zo kuma koda ban je ba, babu matsala. Ke kuma Mr Nazzir zai damu akanki."

    Cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Noorh, sannan tace mata.

     "Noorh! Kin hakura mr Nazzir din ne?" Ta tambaye ta cikin tsoro.
Tashi zaune Noorh tayi tana kallon ta, sannan tace mata.
"Yanzun banda b'atar basira dama me zanyi da shi? Ai sai ke. Ni bana son irin shi.
           Mijina Ready made ne, mijin da zan aura ya kere sa'a'o'in shi, first Class Handsome guy ne, irin me zafin nan, dai dai irina wanda bai damu da kyale kyale mutane ba."

   "Toh idan kin gan shi kece zaki fara Crushing din shi ko shi zai yi crush dinkin.?"

       Tashi zaune Noorh tayi tare da rungume kafaffuna, tana murmushi cikin wani irin ƙasaitacciyar murmushin da yaki barin fuskarta, lumshe idanun ta tayi tare da bude shi akan Tasleem. Sannan tace.
"Tasleem! A yayinda zamu hadu, zai zama na rana ce ta musamman. Ranar sai ya kasance mafi daraja a gare mu, domin zai zo mana a matsayin our first meeting, zai zama ranar da yafi Kowani rana Fantastic."
Ta faɗa cikin dariya.

       Jikin Tasleem ne yayi sanyi sannan tace mata.
"Ke baki da ra'ayin soyayyar shan minti ne, kafin aure."
Sauka tayi daga gadon, sannan tace mata.
"Ai idan Kinga namiji ya tab'a ni, toh ki yarda akan kaddarar ce ya gifta tsakanin mu, bayan haka bana fatan wani ya tab'a jikina. Ke bana fatan wani ya tab'a hijab dina.
      Ke nifa saurayi ganin asara nake nace mishi ina son shi, duk maneman da nake, bana cewa ina son su, haukar su suke kawai.

       Sabida banyi imani da soyayyar duniya a, dan haka manta kawai taso muje."

     Mikewa tayi cikin sauri, suka shirya. Koda suka iso falo babu kowa haka suka tab'a abinci sannan suka kuma fita daga gidan.

     A hankali Tasleem take jan motar. Har suka shiga kwantar da zata kai su kamfanin kawai, suka daki motar kamfanin,  cikin masifa Tasleem ta fito tana bawa driven motar hakuri, basu bude motar Ba, kuma bai sanya sun tafi ba. Abinda ya bani haushi, ina zuwa na make glass din motar, sauke glass din motar aka yi. Na zubawa driven motar  ido.
"Toh ishashe zaka bamu hanya mu shige ko dai na kara dukar motar ku, ka zauna da uban gashin baki kana hura hanci kai gaka nan ishashe.

     Tabbatacce. Toh bamu hanya ko kuma na fasa tayar motar. Wallahi ka godewa Allah ban iya mota ba, da ka shiga uku sai na budeka da kura. Dube shi kawai katon mutum da kai."

    Can bayan motar ta jiyo wani murya yana cewa.
"Wali ya katsaya?"
"Ok sir naji kace na tsaya ne."
Siririn tsaki ta ja, sannan ta bar gurin su,  ta nufi motar su tana cewa.
"Ke kiyi overtaking din yan banza, dan na lura akwai wani kazan gidan gona ne a cikin motar."

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now