Approched

2.1K 184 28
                                    

https://my.w.tt/CWCIoWRQBcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣2️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

    Tunda aka yi sallah dashi, ya nufi gidan Ummi. Ya zauna kallon hanyar Kitchen din yake, a hankali ya nufa, ba tare da ya san cewa zai iya haka ba, kawai ya shiga aikin hada girki, tare da nutsuwa yana yi idan baka nutsu ba, zai yi wuya ka fahimci girki yake domin kome da yake cikin nutsuwa da sanin ya kamata yaƙe.
      Yana kome bakin shi bai fasa ambaton Allah ba, har ya gama ya goge kitchen ɗin tare da wanke kome da ya b'ata, mutum ne me yalwan tsafta, ko me zai yi zaka samu a tsaftace yake, hatta girkin sai da ya saka afro, yana gamawa ya nufi inda Ummi take ajiye warmes ɗinta masu shegen kyau, ya dauke ya juye abincin a cikin su. Sannan ya jera a cikin wani basket. Ya dauko tare da gyara ko ina ya bar kitchen ɗin.
     Idan baka ji kamshin girki ba, ko wuka aka saka maka zaka rantse kace bai yi kome a kitchen ɗin ba, sannan ya nufi gidan shi. Tunda ya shiga ya samu haroon yana gyara gidan, a sanyayye ya nufi Master bedroom din shi. Yana shiga ya ajiye abincin akan wani table, sannan ya nufi kitchen dan yaji yana kaurin girki.
Wanka yayi sosai, sannan ya saka kai ya fito daga ban dakin babu abinda ya dame shi domin babu kome a jikin shi kamar doya haka ya fito.
          Tsayawa yayi gaban mirror ya goge jikin shi da karamin towel, sannan ya shafe jikin shi da mai me dadin kamshi tare da turare me sanyin dadi, ya wuce closet d'inshi ya dauko riga da wando masu kyau da laushi na wani material na kasar Senegal. Ya saka dinki yayi mugun amsar shi.
        Gyara gashin sa yayi sannan ya dauki jar dara, ya saka a kanshi, take hular ta tsaya akan shi, kamar yadda Nasiru Sarkin waka, yake saka hular shi akan sumar shi.
            Simple shoe ya zura a kafar shi, sannan ya dauki basket ya fita dashi, key din black phantom ya dauka, tare da fita a nutse yana kallon yadda gidan ya dauki kamshin turaren wuta.
           A hankali yana motar tare da barin gidan bayan an bude mishi get din gidan. Tare shi Nazzir yayi, tsaki yayi sannan ya tsaya tare da sauke glass din motar, kallon shi yayi tare da dauke kai.
"Lion! Jiya nazo baka nan kuma na kira wayarka, switchoff"
       Gyara zama yayi sannan yace mishi.
"Inda ka aike ni, Hamoud Boualem!"
Shiru yayi yana kallon Mahir, wato zunzurutun rashin mutunci ma da Abban shi ya haɗa shi.
"Toh kayi hakuri, zan raka ka!"
Wani irin kallon banza yayi mishi.
"Ko Ummi bata da ikon bina inda zani, balle kai karan kada miya, dilla bani hanya ko nabi kanka."
         "Wai Lion me kake takama dashi? Kana namiji ina namiji sai wani fisga kake min, uban me ka fini?"
       Jan motar shi yayi bai ma kuma tunanin ya bashi amsa ba, bude shi yayi da kura, sannan ya bar gidan baki daya. Cikin jin haushi ya shiga masifa, tare da rantsuwa sai ya cutar da Mahir sai ya lalata mishi kome.
         Kai tsaye Malam Mahir bai tsaya ko ina ba, sai Asibiti yana shiga ya tsayar da motar shi,  a hankali ya bude bayan motar ya dauko basket din abincin tare da wayar shi dake jikin chajin motar, sai key din motar ya saka a cikin aljuhun rigar shi, sannan ya shiga tafiya a hankali cikin nutsuwa. Zunzurutun yadda yake takun zaka dauka yanga ce ko kidifiri, a'a kawai tsabar miskilanci ne wanda a tafiyar ma sai anyi ta.
       Yadda yake shan kanshi zaka rantse Basarake ne, a'a Izzar kudi ne tare da jinin larabawa da yake gwaraye a cikin jikin shi, duk inda ya gifta nurse da drs mata bin shi suke da ido. Ba zaka tab'a cewa bai fahimci haka ba, sai dai yadda yake shan kamshi zai tabbatar maka da haka. Ganin haka ya kuma tsuke fuskar shi tam..har ya isa d'akin da take, wani karamin murmushi ya sauke tare da tura kofar da sallama, ana daru da ita tana musu larabci.
Tare da kai musu duka, kallon su yayi a hankali ya ajiye basket din. Ganin wani nurse namiji ya kai hannun shi kan k'ugun ta, cikin wani irin zafin nama,ya buge hannun!
         "Karka fara tab'a ta!" Ya daka mishi tsawa, tare da cewa su kyaleta, zai kira su idan ya gama bata abinci, suna fita yaga ta tsuguna a tsakiyar gadon, tana shashekar kuka. Abinci ya zuba mata, tare da saka cokali, ya taka a hankali har gabanta, kallon ta yayi tare da ajiye abincin ta kuma matsawa tare da dafe hannunta a saman gwiwarta.

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now