Exclusively

2K 168 24
                                    

https://my.w.tt/zaUNQPJWzcb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣1️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

    Alhamdulillahi Ubangiji nagode maka da Ni'imar da kai min ☺️
*
"Wato ciwon ne ya koma yadda bazamu iya shawo kanshi lokaci guda ba, sai munyi takatsantsan kafin mu tab'a kanta, domin zaman kwayoyin halittar jininta ya haifar da yiwuwar cutar Cancer a gurin" inji Dr,

     Dafe keyar  shi yayi tare da fidda manyan idanun shi waje.
A lokaci guda zuciyar shi ta shiga wani irin lugude! "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun" yana ji kamar zuciyar shi zata fado, kallon tausayi yayi mata zuciyar shi tayi rauni, kallon yadda ta koma lallai Allah abin tsoron ne duk.wanda bai ji tsoron Allah ba yayi asarar dimun da'iman.

    Cikin abinda bai fi kwana goma ba, ji yadda yarinyar ta koma. Fesar da iskar bakin shi yayi tare da kallon shi yace.
"Ya zamu yi?"
"Za iya fita da ita waje!"
"Toh kana ganin babu matsala?"
"Bana tunanin haka, amma Insha Allah akwai nasara!"

A hankali ya taka har inda suka fito da ita, sannan yana kallon su, suka fitar da ita zuwa dakin da aka kwantar da ita. Karo na farko da yaji a ranshi yana son bibiyar alamarinta, taya ta tsinci kanta cikin wannan yanayin, dan haka abinda ya fara, fita yayi bai tsaya ba, yayi amfani da abinda tambayar da yayi mata suna cikin dajin nan.
*Ina zan kai ki?*
*Gidan Marayu na Jos*

     Wani irin huceccen numfashi ya fesar, kafin ya saka kai ya fita daga Asibitin abu daya yake son sani. Me yasa Baban Tasleem yayi watsi da ita, dan haka ya tashi jirgi zuwa Jos ba tare da b'ata lokaci ba, ya kira wani abokin kasuwancin shi, maitamakin Governor Bitrus Yam ne, yana gaya mishi gashi nan zuwa, tuni aka baza jami'an tsaron sojoji da yan sanda.

      Tafiyar awa daya ta isar dashi garin jos, cikin farin ciki suka gaisa da juna, yace mishi.
"Da fatan zuwan ka zai zame mana Alkhairi."
"Insha Allah ba zai zama sharri ba, Mr Yam.

    Gaya mishi abinda ya kawo shi yayi, cikin azama ya kuwa dauke shi tare da jagorancin P.A d'inshi suka tafi har gidan Marayun.

             Tunda ya shiga gidan yake zubda kwalla, musamman yadda yaga yaran,  Mahir mutum ne mai raunin zuciya, da zaran yaga abu me tausayi sai ya zubda kwalla, kallon yaran yake cikin sanyin jiki, a hankali ya isa Office din shugaban gidan. Bayan sun gaisa sannan yace mishi.
"Suna na!"
"MAHIR Hamoud Boualem CEO na MHB Foods ko?"
Lashe bakin shi yayi tare da sake wata irin murmushi, kafin ya gyara zama, yana lashe bakin shi.
"Ranka ya dad'e! Muna baka hakuri da abinda A'isha Omar Jimeta tayi! Ba laifinta bane,  halin da ta shiga ne na rayuwa, amma kuma sai gashi an sami labarin mutuwarta."

Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude shi fess akan mutumin, yace.
"Babu kome na yafe mata, amma taya tazo gidan nan?"

        "Sir Mahir Hamoud Boualem, na yarda da kai shi yasa zan gaya maka abinda ya faru da A'isha, gashi kuma akwai wasu takardunta yana gurina.

2006

Bayan hatsarin da ya faru, daga hanyar jirgin kasa na jos zuwa garin Bununu na bauchi, mutane sun kone Wasu sun fada a ruwan bununu, dan haka lokacin da aka yi Report jirgin yayi hatsari garin cire mutanen muka sami wani mutum, wanda ya jikata.

     Mika min hannu yayi domin ina cikin yan agajin gaggawa na Red Cross. Mika min wata jaka yayi cikin wahalar azabar da yake ji.
"Nasan ko ya aka yi zata rayu, mune dai ba zamu rayu ba, ga hotonta nan, don Allah ka tayani mikata ga Hussain dina, don Allah karka sake ka bar mishi dukiyar dukka kai ma kayi kokarin daukar wani abu, don Allah rayuwarta nake son ta mike, burinta na zama likita ya tabbata, don Allah akwai wani diary,.akwai bayanin inda Dangin Uwarta suke tare da dangin mu.

MAH~NOOR🌹Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ